Tsofaffi na buƙatar tallafin gaggawa a Nijeriya – NSCC

Shugabar Ƙungiyar Kula da Tsofoffi ta Ƙasa (NSCC), Dokta Emem Omokaro, ta buƙaci masu ruwa da tsaki da su ƙarfafa hanyoyin da tsare-tsare don tabbatar da adalci ga tsofaffi ƙasar nan.

Omokaro, ta yi wannan kiran a ranar Larabar da ta gabata a Abuja, yayin wani taron masu ruwa da tsaki, ya yi kira da a haɗa kai don tabbatar da adalci ga tsofaffi.

Taron masu ruwa da tsaki da aka yi wa laƙabi da ‘Elder Justice’, cibiyar ce ta shirya tare da haɗin gwiwar hukumar kare haƙƙoƙin Dan Adam ta ƙasa da kuma Majalisar bada agaji ta Shari’a.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, an shirya taron ne a matsayin wani ɓangare na gudanar da bikin ranar wayar da kan dattijai ta duniya

Ranar ta na goyan bayan Shirin Majalisar Ɗinkin Duniya wanda ya yarda da muhimmancin cin zarafin dattijai a matsayin batun lafiyar jama’a ce da kuma tauye haƙƙin ɗan adam, kuma ana ƙoƙarin wayar da kan mutane da ƙungiyoyi da al’ummomi game da cin zarafi, sakaci da cin gajiyar dattawa.

A cewarta, “Martanin mu a nan shi ne ta yaya za mu tabbatar da adalci ga tsofaffi, kuma babban jawabi na zai kasance a kan haɗin gwiwa a kan shari’ar dattijai, da kuma inganta tsarin da ke ba da damar yin adalci ga tsofaffi ta hanyar aiki tare.

A nasa jawabin, Sakataren zartarwa, na hukumar kare haƙƙin ɗan adam (NHRC), Mista Tony Ojukwu, wanda Misis Fidelia Oroh ta wakilta, ya bayyana buƙatar haɗin gwiwa don daƙile cin zarafin tsofaffi a Nijeriya.