(Ci gaba daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS
TAMBAYA:
Assalamu alaikum. ‘Yar’uwa barka da wannan lokaci. Ya iyali. Sannu da ƙoƙari. Don Allah shawara nake nema kan matsala ta. Wallahi na yi karatu har na kammala digiri na farko, na yi bautar ƙasa har yanzu na kai na samu aiki a ƙaramar hukuma, kusan shekara ɗaya da rabi kenan.
To shi ne na yi ɗan tanadi da ɗan abinda nake samu na albashi zuwa ‘yar buga-buga da nake yi na haɗa lefe, na tanadi kuɗi har dubu ɗari, sannan na je ga mahaifina kan sha’anin nema min aure. Anan fa ya ce bai san da zancen ba, wai ban isa aure ba tunda ban mallaki gida na kaina ba.
Wai shi ba zai je nema min aure ba don in zauna da matar a gidan haya. Kuma Allah Asas na isa aure, saboda shekaruna 32, kuma gidansu yarinyar da muke soyayya har sun fara gani na a matsayin mayaudari sun ce in fito ko ta zaɓi wani.
Kuma zancen da tsoho ke yi magana da tsakani da Allah ba lamari ne da zai yuwu a nan kusa ba zance na gaskiya ba, domin dubun ɗari da na haɗa da ƙyar ta samu, to bare a yi zancen na sai fili, kuma na gine shi. Ai ba kusa ba gaskiya, indai ba wata hanya ce ta samu ba. Kuma gaskiya Ina matse da son yin aure, kuma Ina da ɗan halin iya kula da matar da zan aura daidai na rufin asiri.
Ki taimaka min da shawarar yadda zan iya shawo kansa, don gaskiya na kusa kai wa maƙura. Na gode.
AMSA:
Da irin wannan ma kana samun matan da ke cire kunya su sanar da iyayensu su fa aure suke so, amma iyayen su qi sauraron su, duk don huɗubar mai farar fata. Kuma fa ba su so ‘ya’yan nasu su yi zina.
Ta yaya ka ke tunanin wanda ya sanar da kai yana jin shahararriyar yunwa, ya nemi ka bar shi ya je ya ci abinci, wanda yana da abin neman sa, ta ya ka ke tunanin zuciyarsa ba zata rinjaye shi ya nema bayan idonka ba.
Annabin rahma ya ce, “dukkanku makiyaya ne, kuma dukkanku abin tambaya ne akan abinda aka ba ku kiyo.”
Yana daga cikin haƙƙin iyaye ga ‘ya’yansu su yi masu biyayya, kuma yana daga cikin haqqin ‘ya’yan ga iyayen su yi masu adalci a ababen da su ne za su yarje masu yi, kamar misalin aure.
Ubangiji ya ce a yi aure don kame kai daga zina wadda Ya haramta. ‘Yarka ko ɗanka ya kai munzalin aure, kuma ya buƙaci yi, har ma yana da abin kula da matar idan ya aura, to kamata ya yi ka gaggauta aurar da su, musamman ma namiji da shi ke cewa yana so ba jira yake a neme shi ba.
Kawar da ido daga buƙatar zai iya zama fita ba wai gare ku kawai ba, har da ma waau iyayen, saboda idan ya biye wa shaiɗan ya fara neman mata a wajen aure, su yaran da zai lalata ɗiyan wasu ne.
Haka idan mace ce, rashin yi mata auren zai iya kai rayuwar wasu mazan da dama ga aikata zina, domin da babu matan da ke kula mazan banza, da su ma sun dawo ga lamarin aure, idan suna da ma sai su yi ƙari.
Rashin ba wa aure muhimmanci a lokacin da yara suka buƙace shi na ɗaya daga cikin gudunmawar ka ga yaɗuwar zina, saboda ba kowa ne aka ba wa ikon iya riqe kanshi ba, duba da cewa sha’awar ma hawa-hawa ce, akwai wanda ta yi masa yawan da ko mace ɗaya sai dai maneji, to irinsa idan ka hana shi auren bakiɗaya me ka ke tunanin zai faru.
Su kansu turawan da suka zame mana allon kwaikwayo, su fa ba su haramta zina ba, kuma ba su ce dole sai ‘ya’yan nasu sun kame kansu ba, don haka ba su da wata matsala da zinace-zinace matuƙar suna kare kai.
Shawara ta ga mutum biyu ce, na farko shine uba, ka sani babban kuskure ne shiga hurumin ubangiji, domin Shi Ya ce, ya hane mu da yin zina, kuma Ya halasta mana aure don kare kai, wannan ne ya sa akwai sauƙi sosai a cikinsa, kamar tadda manzon rahma ya ce, “mafi alkhairin aure shi ne, wanda aka sawwaƙa a cikinsa.”
Sauqin nan kuwa ana yin sa ne don ya ba wa kowa dama, mai kuɗi da talaka ya zamana yana iya yin sa ba tare da wahala ba.
Idan kuwa haka ne, kamata ya yi ka nema wa ɗanka mafita daidai da matsayin da ka ke da shi, wasu iyayen ma har gidan da suke ciki suke gutsura wa ‘ya’yansu idan ba su da halin gina masu wani don kawai su ba su damar kare kansu.
Idan har ba za ka iya taimakon ɗanka da muhallin zama ko na aro ne ba, to ka taima masa ko na hayar ne ya zauna, idan ba ka da hali, ka shige masa gaba, ta yadda ba zai ɗauki wanda ya fi ƙarfin sa ba a dawo ana ta wahala.
Ko ta wacce hanya bai kamata ka hana balagaggen ɗanka da ke da aikin yi aure ba, bayan kana da masaniyar zai iya kula da iyalinsa da xan abinda yake samu.
Idan har mai sana’ar dako ko makamantansu zai iya yin aure, ban ga abinda zai hana ma’aikacin qaramar hukuma da har ya haɗa da wata buga-buga yi ba.
Sai ta biyun gare ka mai tambaye ce, fushi ba naka ba ne, musamman kasancewar iyaye ne a lamarin, lalavawa ake yi don fatan gujewa fushin sa da zai iya kawo wa rayuwarka matsala a gaba.
Da farko idan mahaifinka mai sauraren ‘ya’yanshi ne, zai fi ka daure ka je masa da zancen karo na biyu, ka yi masana gamsasshen bayanin da zai iya fahimta har ya gano ka kai inda ya kamata ya bar ka ka yi aure don ya zama babin dole.
Idan kuwa savanin haka ne, ka nemi wanda ka san yana saurare, na daga iyaye, ‘yan’uwa ko abokai, ka yi masa bayani, shi kuwa ya je ya lallaɓar ma shi don a yi da izinin shi. Saboda duk da cewa, an ba ka wata ‘yar dama ta bijire wa zancen sa a wannan gaɓar, amma amincewarsa ce mafi alkhairi gare ka, don haka zan ƙara faɗa da babbar murya, ka bi shi a hankali da rarashi ya amince, sannan a yi auren.
Allah maɗaukakin sarki Ya ce, “ubangijinka ya shar’anta maka kada ka bautawa kowa sai Shi, su kuma iyaye ka yi masu biyayya.”