Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A rana mai kamar ta yau (18 ga watan Yuni 1999) Allah Ya yi wa shahararren mawaqin Hausa Dr. Mamman Shata Katsina Rasuwa.
Bayani Kaɗan A Kan Shata:
An dai haifi Marigayi Alhaji Dr. Mamman shata a garin Musawa, A Shekarar 1923, kuma ya girma a katsina wato Jihar Katsinan Tarayyar Nijeriya. Ya yi ƙaura zuwa garin kano ya kuma rasu a ranar 18 Yunin Shekarar 1999 an binne shi a garin Daura kamar yadda yabar wasiya, To a lokacin da Marigayi Dr. Mamman Shata ya ke a raye akwai tambayoyi makamanta waxanda Malam Ɗan’zumi ya tambaya, waxanda shi da kansa Shatan ya amsa su a rayuwarsa. Saboda haka, mun yi ƙoƙarin tsinto irin waxannan hirarraki da aka yi da marigayin lokacin da ya ke raye a Duniya.
Ya na da waƙoƙi wanda har ya zuwa yanzu ba’asan adadinsu ba don shi kansa da aka tambaye shi cewa ya yi bai san adadin waƙoƙinsa ba, amma a shekarun baya an sami wata Baturiya da ta zo don tattara waƙoƙinsa inda ta fitar da ƙididdigar sun kai dubu huɗu. Kuma mawaƙi ne da yake da abin mamaki lwarai da gaske, yakan yi waqa duk lokacin da aka so hakan ba tare da inda-inda ba.
An tambayi Marigayi Dr. Mamman Shata cewar a ina ya soma waƙa sai ya kaɗa baki ya ce, “A nan Musawa inda aka haife ni a nan na soma waƙa kuma duk inda na je yawo to da waƙata suka ganni.”
Ko wane dalili ya sa Dr. Mamman Shata ya soma waƙa a rayuwarsa, ga dai amsar da ya bayar“ Dalili shi ne ƙiriniya ta yarinta kurum, bawai don gadon uwa ko uba ba, domin kuwa na daɗe ina yi bana karɓar ko anini, in ma an samu kuɗi sai dai makaɗa da maroka su ɗauka. Sai daga baya bayan na mai da waqa sana’a na fara amsar kuɗi.”
Shin waye sa wa Dr. Mamman Shata wannan suna nasa wato Shata?
“Wanda ya sa mini wannan suna Shata sunansa Magaji Salamu, shi ne ya sanya min suna Shata Mijin mai ɗaki, ita mai ɗakin kakata ce, ita ce ta haifi wanda ya haife ni„
Da aka tambayi Dr. cewar wace waqa ce ta fi suna kuma ya fi jin daɗinta ko kuma ta fi birge shi a duk ilahirin waƙoƙin da ya yi, sai ya ba da amsa kamar haka, “To, wannan wani abu ne mawuyaci a wurina kuma kowa ya ce zai iya ganewa ƙarya yake yi tunda shi Shatan bai gane ba.”
Bisa al’ada ga yanda mawaƙan Hausa suke yin waƙoƙinsu, akwai waƙa da suke yi wa kansu da kansu kirari a cikinta wadda aka fi sani da suna Bakandamiya. To, shi ma Marigayi Dr. Mamman Shata bai yi ƙasa a guiwa ba wajen yi wa kansa irin wannan waƙa.
Ɗaya daga cikin hikimomin da Allah ya baiwa Marigayin shi ne cewar ya na iya ƙirƙira waƙa a duk lokacin da ya ga dama ko kuma aka buƙaci da ya yi hakan. Misali waƙar da ya yi ta Dajin-runhu da kuma waqar da ya yi ta Kenndy Centre a lokacin da ya kai ziyara ƙasar Amurka.
Bisa al’adar Hausa, Mawaƙa sukan yi wa Mutane Waƙa, to amma a wani lokaci a kan yi wa waƙar mummunar fahimta, misali waƙar da ya yi ta kusoshin Birni Uwawu da kuma waƙar nan ta Na-malumfashi Habu Can-mama, wanda masu fashin baƙin waƙoƙi su ke ganin cewa, waɗannan waƙoƙi ya yi su ne domin ya nunawa Mutane cewar ’yan zamani sun rasa inda za su kama, su basu kama Duniya ba kuma basu kama Lahira ba. To da aka tambayi Dr. cewar shin ko wannan bayani na masu fashin baƙin waƙoƙi haka yake sai ya ce “To wannan zance ne irin nasu, shi wanda na yi wa ya san abin da na ce, kuma masu ji da basira sun san abin da na ce.”
Daga cikin dalilan da suka sa Marigayi Dr. Mamman Shata ya ke yi wa Mutane Waƙa, akwai ƙwarewa a kan sana’a misali, waƙar da ya yi ta Bawa Direba. An tambayi Marigayi Mamman Shata, shin waye Bawa direba ɗin nan, kuma mai ya sa ya yi masa waƙa, kuma da gaske ne dukkanin abubuwan da ya faɗa a cikin wannan waqa ta Bawa Direba, gaskiya ne haka abin yake, sai ya ce “Bawa jankin, shi kam Mutumin Katsina ne, amma a Musawa ya yi wayo, duk abin da na faɗi a waƙar Bawa haka yake ban ƙara masa ba, ban rage masa ba, kuma ko da ni ban faxi ba wani sai ya faɗi.”
Har ila yau Marigayi Dr. Mamman Shata yakan yi wa manyan shugabanni waƙa, musamman ma waɗanda suka tsayar da adalci, ’yanci, daidaito da kuma haɗin kan al’umma, Misali