Daga BASHIR ISAH
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bi sahun al’ummar musulmin duniya wajen gabatar da Sallar Idi ta Babbar Allah wadda aka yi a ranar Laraba, 10 ga watan Zul-Hijja wanda ya yi daidai da 28 ga watan Yunin 2023.
Tinubu ya yi Sallar Idinsa ne a filin Idi da ke Obalende a Dodan Barracks, Victoria Island, Legas.
Imam Suliman Abuo-Nolla shi ne wanda ya jagoranci gabatar da sallar mai raka’o’i biyu.
Ga ƙarin hotuna:



