“Tun Ina ƙarama nake da burin neman na kaina”
DAGA MUKHTAR YAKUBU
A daidai lokacin da a ke ganin mata an bar su a baya wajen harkar kasuwanci da sana’o’i tare da kiraye kirayen da ƙungiyoyin kare muradun mata suke yi na mata su tashi su nemi na kan su, an samu wata jaruma a cikin mata wadda ta zama kallabi tsakanin rawuna.
Maryam Isah Abubakar Ceetar mace ce da take harkokin kasuwanci da sana’o’i na kanta wadda har ta kai a yanzu tana da kamfanin gine-gine da kuma qawata gidaje, baya ga harkokin kasuwanci da take yi.
Ganin yadda ta zamo ta daban a cikin mata ya sa jaridar Manhaja ta tattauna da ita domin jin yadda ta fara harkar kasuwanci da har ta kai ga kafa kamfanin ta na kanta, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.
MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatunmu.
MARYAM CEETAR: To Ni dai suna na Maryam Isah Abubakar wadda aka fi sani da Maryam Ceetar. Kuma haifaffiyar Kano ce a Unguwar Birget a nan na tashi na yi karatun firamare da sakandare kuma aka yi mini aure Ina da yara. Bayan wani lokaci da aurena ya mutu sai kuma na shiga harkar kasuwanci, har zuwa yanzu kuma a ta ɓangaren karatu na ci gaba a yanzu haka Ina F C E Kano.
To ko ya aka yi kika fara harkar kasuwanci tun da farko?
E ni daman tun da farko ina da burin neman na kaina tun ina ƙarama, don haka na tashi duk da ina zuwa makaranta, amma dai ina yin irin sana’o’i irin na yara na gida kuma har na girma da aka yi mini aure ma ina ‘yan sana’o’i, har kuma na fara sayar da atamfofi da shaddodi, kayan takalma da sauran kayayyaki na mata da na maza, wannan ya ba ni damar da na samar da kanti, kafin wannan a mota nake saka wa ina yawon talla kuma daga baya Allah Ya ɗaukaka abin na samar da kamfanin gine-gine da kuma ƙawata gidaje, mai suna Isnmom Nigeria Limited, wanda a yanzu shi aka fi sani na da shi a matsayin mai harkar kwangilar gine-gine da fenti.
Ita wannan harkar ta ki ta gine-gine a na ganin harka ce ta maza sai kuma kina mace kika samu kanki a ciki. Sha’awa ce ko dai abin da kika karanta kenan?
To shi dai kasuwanci ko sana’a a rayuwar nan duk wanda yake son ya samu rufin asiri to dole ne ya tashi ya nemi na kansa musamman ma dai mu mata idan mace ta haihu tana da ‘ya’ya ko ta na da aure tana tare da mijin ta , to sai ta tashi ta nemi na kanta domin ya zama an taru an rufa wa juna asiri kuma akwai ‘yan’uwa da wasu nauyin su zai iya zama a kanka da dai sauransu, don haka yanayin rayuwa a yanzu neman abin kai ga mace yana taimaka wa rayuwarta da ta ‘ya’ya domin haka ne zai sa mace ta tafiyar da rayuwarta cikin kwanciyar hankali.
Don haka ka ga ko harkar kasuwanci da nake yi na kayayyaki ina zuwa na sayo kaya a kasuwa, kuma ko abin da ya shafi fenti da gine-gine su ma harka ce ta na saya ba sai na fita waje ba duk abin da nake buƙata zan same shi daga waxanda suke shigo da shi daga waje. Kuma tun da a na samun kayan a nan to zai fi mini sauqi ma da fita wajen don na saya, don haka idan na tashi saye sai na je na sayi daidai wanda zan yi amfani da shi.
Duk da yake a ɓangaren abin da ya shafi fenti da ƙawata gidaje akwai wasu abubuwan da sai mun fita waje muke samun su, don haka idan ta kama na fita waje ɗin domin sayen kayan to na kan fita na je Indiya ko Chana.
Idan kika duba yanayin harkar kasuwancin na ki za a ga cewar abu ne da yake da wahala musamman a matsayin ki ta mace.
To gaskiya ni ina ganin babu wata wahala ga abin da mutum ya sa kansa, kuma yake da wata manufa da yake so ya cimma a rayuwarsa, don haka ba na jin wata wahala tun da ina da manufa. Don haka na san abin da na sa a gaba wannan ya sa ba zan ji wata wahala ba, kuma ko da wahala, ai babu abin da yake samuwa cikin sauƙi.
Yanzu idan mace ta na son ta zama babbar ‘yar kasuwa kamar Maryam Ceetar ya ya kamata ta fara?
E to shi kasuwanci dai ya na son haƙuri, duk lokacin da ka fara sai ka ga abin kamar ba zai yiwu ba, ko da kuɗi ka zuba sai ka kasa gane ma ina ribar ina uwar kuɗin. To dole sai an yi haƙuri kuma an tara hankali waje ɗaya a kan harkar neman da a ke yi a hankali sai kuma ka ga Allah ya kawo nasara mutum ya yi gaba, amma dai haquri ne dai matakin nasarar.
A matsayin ki ta mace mai gudanar da harkar kasuwanci da kuma kamfani, ko ya ki ke tsara rayuwarki wajen tafiyar da ayyukan ki?
To ka san duk wanda aka ce ya na da kamfani, ba shi kaɗai yake gudanar da komai ba, akwai ma’aikata a kowanne ɓangare da suke gudanar da aikin ko ina nan ko ba na nan kowanne an ba shi aikin sa a wajen da ya ƙware kuma yake tafiyar da shi yadda ya dace, don haka ne ma duk wata kwangila da aka ba ni sai ka ga an gama lafiya cikin nasara don haka ba a samun matsala da ni a wajen aiki. Don haka da kamfanin gine-gine da na fentin duk ina da qwararrun masu aiki ko ina nan ko ba na nan su na gudanar da aikin yadda ya kamata. Daman abu ne na tsari to mu kuma muna da tsarin tafiyar da aikin kamfaninmu.
Ita wannan harkar ta ki ta kwangila ta tsaya ne iya Kano ko har da sauran jihohi?
Ina, ai mu aikin mu bai tsaya iya Kano ba, duk da dai Kano gida ce a nan aka fi sanin mu, amma dai akwai gine-gine da kamfanin mu ya yi a Abuja, Kaduna, Jigawa, Katsina, Bauchi, Adamawa, Gombe da sauran jihohi, don haka babu inda ba ma zuwa don gudanar da aikin mu, kuma fenti na ko a ƙasar waje zan iya zuwa na yi saboda yadda muka ƙware a kan aikin, kuma a wajen Paint din kasa son muna da rajista da su saboda ingancin kayanmu
Wanne buri kike da shi a game da wannan harkar ta ki?
To burina dai shi ne ya zama duniya ta sanni a matsayin mai yin aiki mafi inganci, kuma ina da burin kamfanin ya ɗaukaka ya zama mutane masu yawan gaske sun samu aikin yi a cikin sa, kuma ina son na samar da wani vangare nan gaba na koyar da sana’o’i ga mata, don a matsayina na mace ina da burin na ga mata sun samu sana’o’i na dogaro da kansu musamman idan suna gidansu na zaman aure yadda za su samu kwanciyar hankali tsakanin su da maigida da kuma yaran da suka haifa.
Don ka ga a yanzu kamfanin da nake da shi ayyukan duk ya fi ƙarfi ga maza don haka nake son mata ma na samar musu na su vangaren da za su koyi sana’a da kasuwancin da za su dogara da kansu. Babbban burina dai a yanzu shi wannan da nake da shi a yanzu na samu ya tsaya da ƙafar sa
Ko menene saƙon ki na ƙarshe musamman ga mata?
To saƙo na dai shi ne mata su sani sana’a ta na da matuƙar muhimmanci a rayuwarsu ta zaman aure da kuma wadda ta samu kanta ba a zaman auren ba babu ma kamar in ta na da yara, kai ko ita kaɗai ce ya zama dole ta tashi ta nemi na kanta, don haka ina kira ga mata musamman mu na nan Arewa ko in ce Hausawa lokaci ya yi da za mu yi wa kanmu faɗa mu tashi mu nemi na kanmu, domin a yanzu akwai kasuwancin da mace ta na cikin gida ma za ta gudanar da shi ba tare da sai ta jira miji ya ɗauko ya ba ta ba. Kuma a ɓangaren kasuwanci ina son waɗanda mu ke harka irin ta gine-gine ya zama muna yin masu inganci, kuma mu cire son zuciya, ta yadda Allah zai saka albarka a cikin harkokin mu, ina fatan Allah ya yi mana jagorancin.
To madalla mun gode.
Ni ma na gode.