Editor

9513 Posts
Majalisar Dokokin jihar Yobe ta zaɓi Hon. Mashio a matsayin Kakakinta

Majalisar Dokokin jihar Yobe ta zaɓi Hon. Mashio a matsayin Kakakinta

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu Hon. Chiroma Buba Mashio daga mazaɓar Jajere, ya zama sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe, zubi na 8. Hakan ya biyo bayan zaman da majalisar ta ƙaddamar a ranar Litinin a zauren majalisar dake Damaturu. Sa'ilin da aka fara gabatar da ƙudirin zaɓen sabon Kakakin Majalisar, wanda Hon. Adamu Dala Dogo mai wakiltar mazaɓar Karasuwa ya gabatar inda ya samu goyon bayan Hon. Bukar Mustapha na mazab'ɓar Geidam ta tsakiya tare da samun amincewar dukkanin 'yan majalisar dokokin su 24. An haifi Hon. Buba Mashio ne a ranar 25 ga Mayu, 1968 a garin Mashio…
Read More
A tuna da matasa a rabon muƙaman sabuwar gwamnati

A tuna da matasa a rabon muƙaman sabuwar gwamnati

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Matasa wani muhimmin jigo ne a harkokin siyasa, don suna taka muhimmiyar rawa wajen ƙara wa siyasa armashi. Su ne kan gaba a yaƙin neman zaɓe, da gudanar da ayyukan zaɓe da suka haɗa da aikin sa ido don wakiltar jam'iyyu, aikin tafiyar da zaɓe, har ma da shiga bangar siyasa. Kar ku manta hatta manna fostar ɗan takara matasa ne ke yi. A wasu wurare da dama, da zarar ɗan takara ya yi shirin bayyana aniyarsa ta neman wani muƙamin siyasa to, matasa na daga cikin rukunin farko da yake fara ganawa ko neman shawarar…
Read More
Kotu ta taka wa Abba Kabir birki kan rusau a Kano

Kotu ta taka wa Abba Kabir birki kan rusau a Kano

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotu mai zamanta a Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a S.A. Amobeda, ta dakatar da Gwamnan Jihar, Engr. Abba Kabir Yusuf, daga ci gaba da rushe gine-gine a jihar. Umarnin Kotun ya biyo bayan ƙarar da wani ɗan Kano mai suna Saminu Muhammad, ya shigar ta hannun lauyansa a gaban Kotun. Yayin zamanta a ranar Juma'a, Kotun ta bai wa Gwamnatin Jihar Kano umarnin dakatar da ci gaba da rusau a kan wasu gine-gine a yankin hanyar BUK. Alƙali Amobeda ya ce kada Gwamnatin jihar ta taɓa gine-gine masu lamba 41 da 43 da ke Salanta, a…
Read More
AEDC zai yi ƙarin kuɗin wutar lantarki a Yuli

AEDC zai yi ƙarin kuɗin wutar lantarki a Yuli

Daga BASHIR ISAH Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya ba da sanarwar zai ƙara kuɗin wuta ya zuwa 1 ga watan Yulin 2023. Cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi da daddare, AEDC ya ce buƙatar ƙarin wutar ta taso ne duba da yadda darajar Naira ke hawa da sauka a kasuwar canji. Sanarwar ta ce: “A sani, daga ranar 1 ga Yuli, 2023, za a yi ƙarin farashin wutar lantarki sakamakon hawa da saukar da farashi ke yi a kasuwar canji. “Farashin canji a ƙarƙashin ƙa'idojin MYTO na 2022 da ya kasance N441/$1 a da, yanzu yana…
Read More
Bill Gates ya buƙaci Nijeriya ta inganta hannun jarin cigaban al’umma

Bill Gates ya buƙaci Nijeriya ta inganta hannun jarin cigaban al’umma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hamshaƙin attajirin duniya kuma Shugaban Gidauniyar Bill da Melinda Gates, Bill Gates, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta inganta saka hannun jari wajen samar da mafita mai kyau ga mutane ƙasar. Ya bayyana hakan ne a yayin taron samar da ƙirƙire-ƙirƙire na matasa na Pan-African a ranar Laraba a Legas, a wani ɓangare na ziyarar da ya kai Nijeriya. Taron yana da taken: "Ci gaban Afirka: Sake Ƙarfafa Matasa a Kimiyyar Ƙirƙirar Ƙirƙirar." Gates ta ce, Nijeriya na cike da haziƙan mutane da dama, amma ya yi nuni da cewa zai yi wuya a iya cika…
Read More
CBN ya cire takunkumi a asusun banki na Dala, ya mayar da shi $10,000 kullum

CBN ya cire takunkumi a asusun banki na Dala, ya mayar da shi $10,000 kullum

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya cire takunkumin da ya sa a asusun bankin Dala. Inda ya lara kuɗin da za a iya zubawa zuwa Dalar Amurka $10,000 a kullum. Wannan bayani yana ƙunshe a wani jawabi da aka wallafa bayan ganawa da kwamiitin ma'aikatan banki a ranar Lahadin da ta gabata. 18 ga Yuni, 2023. An shirya taron ne saboda niyyar samar da sababbin dokoki da za a ƙaddamar a harkar bankin. Sabuwar dokar ta soke iyakar da aka sanya a kan hada-hadar asusun banki na Dala a shekarar 2021. Don yin biyayya ga wani umarni…
Read More
Za a fassara Huɗubar Arfar bana da harshen Hausa a Saudiyya

Za a fassara Huɗubar Arfar bana da harshen Hausa a Saudiyya

Daga BASHIR ISAH Hukumomin Saudiyya sun bayyanar da harsunan da za a fassara Huɗubar Arfa yayin aikin Hajjin 2023. Sanarwar hukumomin ta nuna manyan harsunan duniya guda 20 ne za a fassara huɗubar a cikinsu, ciki har da harshen Hausa. Shugaban kula da masallacin Ka'aba da na Annabi da ke Madina, Sheikh Dr. Abdulrahman Al-Sudais ne ya bayyana haka, yana mai cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin yaɗa huɗubar kai tsaye daga Masallacin Namirah. A cewarsa, harsunan da lamarin ya shafa sun haɗa da: Hausa, Faransanci, Ingilishi Persian, Urdu, Russian, Turkish, Punjabi, Sinan i, Malayo, Swahili, Spanish, Portuguese, Amharic, Jamussanci,…
Read More
Haraji: An ba wa Tinubu shawarar haɗe hukumomin NIMASA, FIRS da Kwastam a inuwa guda

Haraji: An ba wa Tinubu shawarar haɗe hukumomin NIMASA, FIRS da Kwastam a inuwa guda

Daga AMINA YUSUF ALI Kwamitin mashawartan gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu sun ba shi shawarar haɗe hukumomin NIMASA, hukumar haraji (FIRS), da kuma hukumar Kwastam, dukkansu su kasance a ƙarƙashin hukumar tattara haraji ta tarayya wato FIRS. Haɗewar a cewar kwamitin mashawartan za ta taimaka wajen amsar haraji na kai tsaye da ba na kai tsaye ba a madadin gwamnatin tarayya. Majalisar ta nemi a yi garambawul ga dokar tattalin arziki cikin gaggawa don ba wa shugaban ƙasa damar zartar da wannan hukunci. Wannan kwamitin mashawartan wacce Mista Tinubu ya haɗa don tallafawa wajen samar da tattalin arziki mai…
Read More
JAMB za ta fara barin ɗalibai shiga zauren jarrabawar UTME da wayoyinsu

JAMB za ta fara barin ɗalibai shiga zauren jarrabawar UTME da wayoyinsu

Daga BASHIR ISAH Hukumar Shirya Jarrabawar Neman Gurbin Karatu a Manyan Makarantu (JAMB), ta ce tana nazari kan wata sabuwar dokar da za ta bai wa masu rubuta Jarrabawar UTME damar yin amfani da wayar salula da makamancinta yayin rubuta jarrabawar. Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka a wurin taron da suka gudanar a ranar Asabar a Abuja. A cewar Shugaban, buƙatar samar da wannan sabuwar dokar ta taso ne duba da tsadar gudanar da jarrabawar UTME a faɗin ƙasa da hukumar kan fuskanta. Oloyede ya ƙara da cewa, hukumar JAMB ka kashe sama da Naira…
Read More
EFCC ’yar amshin Shata ce!

EFCC ’yar amshin Shata ce!

Hukumar Hana Cin Hanci da Karɓar Rashawa (EFCC), muna jin irin yadda ki ke ƙoƙari wajen gano masu wawure dukiyar ƙasa inda suke azurta kansu suna ƙoƙarin nakasa ƙasarmu. Duk da dai ji ne muke yi kin gano wane kowane ko suwane sun yi handama da baba-kere ko yin awon gaba da dukiyar ƙasa! Na sha ganin wasu maka-makan gidaje ko wasu gine-gine da hukamar EFCC ta kama inda har ta ke rubuta sunanta ajikin gidajen ko gine-ginen. Hakazalika, muna jin yadda hukumar ke cewa ta amso ko ta kwato maƙudan kuɗaɗen da wasu marasa kishin ƙasa suka handame. Sai…
Read More