Editor

9513 Posts
Asamoa Gyan ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa

Asamoa Gyan ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar Ghana, Asamoah Gyan ya sanar da yin murabus daga buga ƙwallon ƙafa. A wata sanarwa, Gyan ya ce lokaci ya yi da zai ajiye aikin taka leda a cikin mutunci. Ɗan wasan ya ci kwallaye 51 daga wasanni 109 daya buga wa ƙasarsa, lamarin da ya sa ya zama ɗan wasan Ghana a ya fi cin ƙwallaye a tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar. Ɗan wasan mai shekaru 37 ya fara sana’ar ƙwallon ƙafa ce a shekarar 2003 tare da ƙungiyar ƙwallon Liberty Professionals, inda daga bisani ya koma Turai, ya fara…
Read More
Okonjo-Iweala ta maida martani kan ce-ce-ku-cen da ake yi vame da cire Tinubu a hotonta

Okonjo-Iweala ta maida martani kan ce-ce-ku-cen da ake yi vame da cire Tinubu a hotonta

Daga BASHIR ISAH Shugabar Cibiyar Cinikayya ta Duniya, Ngozi Okonjo-Iweala, ta maida martani bayan da wasu ‘yan Nijeriya suka yi ca a kanta saboda cire Shugaba BoIa Tinubu da ta yi a wani hoton da suka ɗauka a wajen babban taron da ya gudana a Paris, babban birnin Faransa kwanan nan. A ranar Juma’a aka ga Okonjo-Iweala ta waIIafa hoton da suka ɗauka a wajen taro a shafinta na Tiwita inda a ciki aka gano ta yanke inda ya kamata a ga Shugaba Tinubu. Tinubu na daga cikin mahalarta taron wanda Shugaban Ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, ya shirya. Taron ya…
Read More
Ranar yaƙi da cutar Sikila a Nijeriya

Ranar yaƙi da cutar Sikila a Nijeriya

A Nijeriya, an ware ranar 19 ga watan Yunin kowace shekara domin tunawa da ranar cutar sikila ta duniya. Ana bikin ranar ne don wayar da kan jama'a na duniya kowace shekara da nufin havaka ilimin jama'a da fahimtar cutar sikila da ƙalubalen da marasa lafiyar da danginsu da masu kula da su ke fuskanta. Kafin mu san ya cutar ta ke, dole mu fara sanin yadda ake kamuwa da ita. Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum ya ji ciwo ko kuma ya yanke jikinsa yana ɗauke da abubuwa iri daban–daban, kamar su 'plasma', 'Red Blood Cells' (RBC),…
Read More
Babbar Sallah: Matawalle ya ba da gudummawar kuɗi da dabbobi na N200m

Babbar Sallah: Matawalle ya ba da gudummawar kuɗi da dabbobi na N200m

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Dr. Bello Mohammed Matawalle ya amince tare da fitar da Naira miliyan 200 na saye da raba shanu da raguna da kuma tsabar kuɗi ga al’umma daban-daban a jihar don gunar da bikin Babbar Sallah da ke tafe. Sakataren yaɗa labarai na Jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya miƙa wa Blueprint Manhaja ranar Asabar. Matawalle, wanda shi ne Jagoran jam’iyyar APC a jihar, ya umarci shugabannin jam’iyyar APC na jihar a ƙarƙashin shugabanta, Hon. Tukur Umar Danfulani, da ya jagoranci rabon kayan…
Read More
Batun maida Mohammed Dauda kan shugabancin hukumarmu ba gaskiya ba – NIA

Batun maida Mohammed Dauda kan shugabancin hukumarmu ba gaskiya ba – NIA

Daga BASHIR ISAH Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Ƙasa (NIA), ta ce, Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta maida Mohammed Dauda kan kujerar Darakta-Janar na hukumar ba kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka yaɗa. Cikin sanarwar da ya fitar a Abuja, Shugaban sashen shari'a na hukumar, Mr A. H. Wakili, ya ce ba gaskiya ba ne cewar an dawo da Mohammed Dauda kan muƙamin shugabancin hukumar. Sanarwar ta ce: “An ja hankalinmu kan wani rahoton da ba daidai ba wanda aka yaɗa a intanet dangane da maido da Ambasada Mohammed Dauda matsayin Darakta-Janar na Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Ƙasa…
Read More
An yaba da yadda Hon. Kana Ahmad ke canja fasalin hukumar samar da ruwa a Jihar Nasarawa

An yaba da yadda Hon. Kana Ahmad ke canja fasalin hukumar samar da ruwa a Jihar Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya An yaba wa sabbin dabaru da sabon Janar Manajan Hukumar Samar da Ruwa na Gwamnatin Jihar Nasarawa, Honorabul Kana Ahmad Mohammed ke cigaba da ƙirƙirowa a yanzu don canja fasalin hukumar a jihar. Injiniya Mohammed Addra wanda shine manajan daraktan babban cibiyar dake kula da harkokin ruwa a shiyar Arewa ta Tsakiya wato Lower Benue River Basin Authority (LBRBA) a turance ne ya bayyana haka a lokacin da janar manajan hukumar ta ruwa a jihar Nasarawa, Honorabul Kana Ahmad Mohammed ya jagoranci sauran shugabannin hukumar inda suka kai wa cibiyar ta LBRBA wata ziyarar…
Read More
Gwamna Raɗɗa zai sake fasalta Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji ta Jihar Katsina

Gwamna Raɗɗa zai sake fasalta Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji ta Jihar Katsina

Daga RABI'U SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya shirya sake fasalta Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji ta jihar domin bunqasa hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga ga jihar. Gwamnan ya sanar da hakan ne a lokacin wani taron gaggawa da ya kira hukumomin dake samar da kuɗaɗen shiga ga jihar a ranar Larabar nan 21 ga Yuni, 2023 da ya gudana a gidan gwamnatin jihar Katsina. Maigirma Gwamna Raɗɗa ya ce babban maƙasudin wannan taro shi ne don ƙara faɗakar da hukumomin dake samar da kuɗaɗen shiga da su kara matsa kaimi wajen gudanar da ayyukansu domin…
Read More
Sai na binciki Ganduje a kan bidiyon dala, in ji Muhuyi Magaji

Sai na binciki Ganduje a kan bidiyon dala, in ji Muhuyi Magaji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sabon Shugaban Hukumar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Barista Muhuyi Magajin Rimin-Gado, ya yi alƙawarin sake buɗe binciken da ake yi wa tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan faifan bidiyon da ya janyo cece-kuce. Jaridar Daily Nigerian ce a 2018 ta fitar da wasu faya-fayan bidiyo na Ganduje da ake zargin yana karɓar kuɗaɗe, Dalar Amurka daga hannun 'yan kwangila. Sai dai da yake magana a gidan talabijin na Trust TV, Rimin-Gado, wanda Ganduje ya tsige bayan wata hatsaniya, amma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da shi…
Read More
‘Yan sanda sun cafke wanda ya cinna wa yarinyar da ake zargi da maita wuta a Bauchi

‘Yan sanda sun cafke wanda ya cinna wa yarinyar da ake zargi da maita wuta a Bauchi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta cafke wani ɗan shekara 30 bisa zarginsa da ƙoƙarin kisan kai ta hanyar banka wa wata ƙaramar yarinya wuta. Ya zargi yarinyar da cewa ita mayya ce don haka ne ya cinna mata wuta bayan takun-sakar da ya shiga tsakaninsu. A sanarwar manema labarai da kakakin rundunar, Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, ya ce an kama mutumin ne bisa zargin yunqurin kisan kai da azabtar da ƙaramar yarinyar. Wanda ake zargin ya bayyana abin da ya faru a matsayin tsautsayin ya rutsa da ita, Hafsat Bala a ranar 18…
Read More
Abba Gida-Gida ya bayyana yadda matar Shugaban DSS ta yi barazanar hana shi zama Gwamna

Abba Gida-Gida ya bayyana yadda matar Shugaban DSS ta yi barazanar hana shi zama Gwamna

Daga RABI'U SANUSI a Kano Sabon Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tofa albarkacin bakinsa kan abin da ya faru tsakaninsa da uwargidan shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Magaji Bichi, jim kaɗan gabanin zaɓen 2023. Gwamna Yusuf ya ce matar Bichi ta yi barazanar hana shi zama gwamnan jihar Kano a zaɓen 2023. Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da yake tattaunawa da malaman Addinin Musulunci a gidan gwamnati da ke Kano, domin neman goyon bayan gwamnatinsa. Idan dai za a iya tunawa a wani lokaci gabanin zaɓen, an yi ta cece-kuce…
Read More