Rusa badalar Kano da sake gina ta

Daga SAIFULLAHI YUSUF INDABAWA

 1. Shekara 39 aka yi ana gina Badalar Kano daga 1095 zuwa 1134 domin samar da tsaro daga mahara.
 2. Badalar tana da tsawon ƙafa hamsin (50), da faɗin ƙafa arba’in (40) da zagayen (nisa) ƙafa dubu arba’in da biyar da ɗari tara da talatin da biyu (45932). Idan ka lissafa tana Ariya Mai girman miliyan arba’in da biyu da dubu ɗari shida da ashirin da huɗu da ɗari takwas da tamanin da shida (42,624,896).
 3. Badalar tana da ƙofofi guda goma sha biyar (15) kamar Ƙofar Nassarawa, Sabuwar Ƙofa, Ƙofar Ɗan’agundi, Ƙofar Na’isa, Ƙofar Gadon Ƙaya, Ƙofar Famfo, Ƙofar Dukawuya, Qofar Kabuga, Ƙofar Kansakali, Ƙofar Waika, Ƙofar Ruwa, Ƙofar Dawanau, Ƙofar Wambai, Ƙofar Mazugal da Ƙofar Mata.
 4. Badalar tun bayan zuwan turawa da kafuwar Nijeriya ake gine-gine a kanta har zuwa wannan lokacin. Kamar misalin ginin Gidan Murtala dake Ƙofar Nassarawa da aka yi shi lokacin Gwamnan Kano Audu Bako a shekarar 1974.
 5. Kafin gabatar da sabbin gine-ginen da aka yi, Badalar ta zama wata matattarar matasa wajen gudanar da cinikayyar kayan maye, daba, ƙwacen waya, sa sauran abubuwa na hatsari ga rayuwa da cigaban al’umma.
 6. Mutane da dama sun rasa rayukansu a wannan guraren ta dalilai da dama da suka haɗar da zuwa wanka a cikin kududdufayen da ke wannan gurin, faɗan Daba, da sauran abubuwa makamantan haka.

Buƙatarmu:

 1. In dai za a rushe gine-ginen da a ka yi, a kan badala to a rushe su gabakiɗaya. Tun daga Ƙofar Nassarawa har zuwa abun da ya zaga ya dawo Ƙofar Wambai ya dawo kofar Nassarawa domin dawo da ganuwar asali saboda tarihin Kano kar ya vace. Wannan gine – ginan sun haɗa har da gidan Murtala, da Ado Bayero House wanda Yusuf Maitaima Sule University ke amfani da shi saboda muhimmancin da tarihi yake da shi na ƙoƙarin tsofaffin sarakunanmu da suka gina Badala lokacin mulkin Sarkin Kano Zamnagawa..
 2. Dawo da kududdufayen da suke bayan Badalan domin magance matsalar ambaliyar ruwa, gurvacewar muhalli da magudanen ruwa, tare da zagaye kududdufayen, da samar da cikakken tsaro a gurin kowanne kududdufi da za a sake haƙawa domin dawo da tarihi dan Asali.
 3. Samar da hanyoyin daqile taruwar matasan da kan samu matsala a irin waɗannan guraren tarihin, ta hanyar inganta yanayin kasuwanci da masana’antu, da sana’o’i, da ilimi domin inganta rayuwar matasan mu, su zamto a kan gaba wajen bunƙasawa da gina tattalin arzikin jihar cikin zaman lafiya da kyakkyawan yanayi.

Kafin nan, za mu yi farin ciki idan aka yi mana ƙarin bayani a kan:

 1. Me ya sa ba kowanne gini da aka yi shi akan Badalar aka yi wa rubutun a cire shi ko kuma a rushe idan masu shi ba su cire ba?
 2. Shin da gaske ne, duk wanda ba a saka masa alama ba yana da alaqa ne da gwamnati?
 3. Idan haka ne ya ya matsayin rantsuwar da shugaban gwamnati ya yi ranar da aka rantsar da shi cewar “…..Na yi alkawarin ba zan bi son zuciyata ba wajen gabatar da aiki na…..”, “….zan yi wa kowa adalci ba tare da fifiko ko ba, kamar yadda yake a doka…,” “…..ba zan bayyana dukkan wani sirri da ni kaɗai ya kamata na sani ba ga kowa, …zan sadaukar da kaina wajen hidimta wa al’umma domin tabbatar da walwalarsu?”
 4. Shin shi wannan rusau ɗin wacce walwalar ya bayar ga al’umma?
 5. Nawa ginin dawo da badalar zai ci?
 6. A ina za a samo kuɗin gina sabuwar badalar tare da haƙa kududdufaye a bayanta domin dawo da tarihin Kano?
 7. Misali idan za a gina duk faɗin ƙafa ɗaya a kan Naira dubu biyar da ɗari bakwai da sittin da ɗaya (5,761) ko ka ce a Dala bakwai kuɗin Amurka za a kashe Naira biliyan ɗari biyu da arba’in da biyar da miliyan ɗari biyar da sittin da biyu da dubu ashirin da aiyar da ɗari takwas da hamsin da shida (245,562,025,856.00) mai girman faɗin ƙafa miliyan arba’in da biyu da dubu ɗari shida da ashirin da huɗu da ɗari takwas da tamanin da shida (42,624,896 Square Feet).?
 8. Wannan kuɗin da shi ne mafi karanci da za a kashe wajen gina wannan badalar wanda da wahala ma a samu kamfanin da zai yi aikin a haka saboda tsabar sauqin kuɗin da kuma wahalar aikin ya yi kusan dai-dai da kasafin kuɗin gwamnatin Kano na shekarar 2023 da muke ciki a yanzu.
 9. Idan Abba zai gina wannan badalar, sai an tsayar da kowanne irin aiki a Kano da ake, na zahiri, da na gudanar da gwamnatin na shekara guda cir, da ya haɗar da manyan ayyukan gine-ginen hanyoyi, gidaje, ma’aikatu da kasuwanni da sauransu, da kuma gudanarwar gwamnati a dukkan ma’aikatun kano guda 23.
 10. Idan kuma a shekara huɗu za a gina badalar, Kasafin kuɗin Kano kaso 25 zuwa sama, za a dinga ware wa ginin badalar, wanda yana sama da kula da lafiya, da ilimi, da muhalli, da Shari’a da, kasuwanci, da noma, da tsare-tsare, da gudanarwa da dukkan ayyukan sauran ma’aikatu.
 11. Shin Badala ta fi waɗancan abubuwan ne?
 12. Ta yaya za a aiwatar da sauran alƙawarurrukan da aka yi wa al’umma na ilimi kyauta, tallafin karatun ƙasashen waje, samar da sabbin asibitoci da kasuwanni, inganta ayyukan noma, kula da haƙƙin ma’aikata da ‘yan fansho da sauran ayyukan gudanarwa na gwamnati?

A ƙarshe, a matsayina, na cikakken ɗan Kano, ina ba wa Gwamnatin Kano Shawari kamar haka:

 1. A tsaya a nutsu, a kalli tsarin da aka faɗa mana za a yi amfani da shi, tare da tsefe shi domin fitar da abun da zai yiwu wajen samar da cigaban Kano.
 2. Gwamnati ta sani, dukkan haƙƙin yan Kano ne a kanta, babu maganar a ware waɗansu, tunda Kano, tamu ce dukkan mu, idan ta ci gaba, mun cigaba, idan muka cigaba ta ci gaba. Gwamnati itace uwar kowa, kuma kowa nata ne, mu nata ne, ita tamu ce.
 3. A kalli maslahar al’umma a yi adalci a komai.
 4. Shugaban Gwamnati ya sani cewar shi al’umma suka zaɓe, kuma shi Allah zai tambaya a kan haƙƙoƙinsu, da aka ɗora masa na kulawa, lokacin da babu dukkan waɗan da suke saka shi, daga shi sai ayyukansa.
 5. Mu kuma ji tsoron Allah a kan komai.
  Saifullahi Yusuf Indabawa mai sharhi ne a kan lamurran siyasa. Ya rubuto daga jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *