Gwamnatin ramuwa?

Daga ALIYU ƊAHIRU ALIYU

Bakiɗayan mulkin Abdullahi Umar Ganduje daga 2019 zuwa 2023 na ramuwar gayya ya yi. Kuma shi a kan mutanen Kano ma bakiɗaya ya yi shi saboda ya san ba su zaɓe shi ba aka yi masa fashin zaɓe.

Don haka, duk wanda ya ce a tsaya a ba wa wanda ya ci zaɓe zaɓensa, sai da ya yi masa rashin mutunci. Da Sanusi Lamiɗo Sunusi da Mallam Abduljabbar duka abin da suka faɗa kenan amma Ganduje ya ɗaure ɗaya da sharri ya kuma yi wa ɗayan korar wulakanci ta yadda ‘yancinsa ma na yawo sai a kotu ya samo.

‘Yan Kwankwasiyya sau nawa suna kai ƙarar Daraktan DSS da suka ce abokin Ganduje ne yana sakawa a kamasu ko ba su da laifi? Da ka yi magana an kama ka a kai ka gaban wasu alƙalai biyu su ɗaure ka duk gaskiyarka. Wani alƙali ba irin ƙaurin sunan da bai yi ba.

Haka wani kwamishinan ‘Yansanda da aka kusa kawo shi Kano dab da zaɓe. A inda ma ba ka yi laifi ba sai a haɗa maka jama’a su yi maka sharri. Idan ku da yawa ne kuma, a haɗa ku da ‘yan daba. Duk fa waɗannan abubuwan ko shekara biyu ba a yi da yin su ba.

Saboda ‘yan Kano ba su zaɓi Ganduje a 2019 ba, ya je ya fito da ‘yan daba ya ba su muƙamai. Suka ci karensu babu babbaka a jihar nan. Kamfen ya zama bala’i saboda za su zo wucewa su yi wa mutane ƙwace.

Sace-sace ya yawaita saboda duk yadda ɗan daba ya kai, idan aka kai shi ga hukuma to yana da wani a gwamnati da zai tsaya masa ya fito. Daga ƙarshe har sai da ta kai ‘yan gari suna kwafo abin da a baya ake yi wa Lagos gori a kansa na “jungle justice” kuma Ganduje ya sauka sannan aka samu sauƙi.

Ganduje da muƙarrabansa suka lalata garin nan duk don ramuwa a kan talaka. Ba inda ba su yanka ba: hanyoyi, kasuwanni, makarantu, masallatai, badala da asibitoci. Lalacewar sai da ta kai har ofisoshin gwamnati suna siyarwa saboda kawai dagewa sai sun lalata Kano.

Suka bar makarantu suka lalace, asibitoci a lalace, hanyoyi a rakwakkwaɓe; hatta fitilun kan hanya duk wata sai sun fitar da kuɗinsu amma duk da haka ba sa kunnawa. Sai ƙarshen lalacewa shi ne shiga asibitocin da aka lalata ana sace injinansu da sunan gwanjo. Kai har litattafai a library sai da Ganduje ya siyar aka yi maganin sauro da su!

Saboda son ramuwar gayya ga mutanen da ba sa sonsa, Ganduje ya rufe makarantun da talakawa ke amfana sama da 50. Ya watsar da ɗaliban jihar Kano a ƙasar waje. Ya raba wa kansa da iyalinsa kadarorin gwamnati. Sannan ya dinga bin duk wanda ya ce masa ba haka ya dace ba yana daurewa.

‘Yan Adaidaita Sahu saboda kawai suna manna fastar Kwankwaso ya dinga azabtar da su da dokoki kala-kala har sai da ta kai ya haramta musu bin wasu tituna duk ba don rage cinkoso ba sai don kawai sun ce ba sa yinsa.

Duk wannan ba ka kira shi da ramuwa ba sai yanzu da ake ƙwato wa talakawa haƙƙoƙinsu shi ne za ka ce ramuwa? Kai ba ka da tunani ne? Ko jam’iyya da tumasanci sun rufe maka ido ba ka neman komai sai neman rashin nasarar masu son fitar da kai daga ƙunci?

Duk sharar nan da ta cika gari tana janyo cutuka da ambaliya amma a haka Ganduje ya siyar da motocin ɗiban sharar da ya zo ya tarar don ya azurta kansa. Ƙarshen lalacewa sai da ta kai an hasko shi a bidiyo yana karvar abin da kowa ya san rashawa ce. Duk kuma saboda ba ka san haƙƙinka ba kake cewa wai waɗannan mutanen za a ja wa layi a ƙyale su kawai! Ta ina?

Aliyu Ɗahiru Aliyu ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto daga Birnin Tarayyar Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *