Mu tausaya wa rayuwar zawarawa

Manhaja logo

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A ƙarshen makon da ya gabata ne aka gudanar da bukin Ranar Zawarawa ta Duniya, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta tsayar da ranar kowacce 23 ga watan Yuni don zama ranar da za a tattauna matsaloli da ƙalubalen da mata zawarawa, musamman waɗanda suka rasa mazajensu na aure a dalilin mutuwa ko yaƙe-yaƙe da sauran su, da nufin samar da hanyoyin taimaka musu ko tallafawa halin da suke ciki ta hanyar sana’o’i ko ayyukan yi.

Tun a shekarar 2010 ne aka ƙaddamar da wannan rana, wacce ƙasashen duniya da dama suke raya bukinta, ta hanyar shirya tarukan wayar da kai, raba kayan tallafi, bayar da jarin sana’o’i, da kuma jerin gwanon mata da ƙungiyoyi, don ƙalubalantar hukumomi da gwamnatoci da nufin samar da muhimman tsare tsare da dokoki na yadda za a inganta rayuwar gwagwaren mata, da ke rayuwa cikin ƙunci da tagayyara.

A Nijeriya ma an samu wasu jihohi da ƙungiyoyi da suka shirya taruka irin haka, inda aka rabawa mata zawarawa wasu kayan tallafi, da kuma gabatar da jawabai da nasihohi don ƙarfafa musu gwiwa.

Hajiya Altine Abdullahi Waziri, ita ce shugabar Ƙungiyar Muryar Mata Zawarawa da Marayu ta Nijeriya, wacce ta yi fice wajen gwagwarmaya kan ceto rayuwar aure, da neman samar da ingantaccen tsarin da zai inganta rayuwar zawarawa, kyautata zamantakewar auratayya, da rage yawaitar zawarawa a Jihar Kano da ma Nijeriya baki ɗaya.

A zantawar da na yi da ita albarkacin bikin wannan rana ta tunatar da ni jerin gwanon mata zawarawa a Birnin Kano a shekarar 2008 wanda ya ɗauki hankalin duniya, kuma ya haifar da sanya wannan rana ta Zawarawa da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi.

Ta koka matuƙa da riqon sakainar kashin da ake yi wa aure a tsakanin al’ummar Hausawa Musulmi ’yan Arewa ta yadda kan ƙaramin abin da bai kai ya kawo ba sai a saki mace. Wata da qananan yara ko da juna biyu, wata ma auren ko shekara ba a yi ba, an sake ta ta zama bazawara, babu wani kyakkyawan tsarin yadda za ta cigaba da rayuwarta ko kulawar abinci da sutura.

Wata ma babu wurin zama mai kyau, ko da kuwa a gaban iyayenta ne, sai hantara da kyara. A cewarta irin waɗannan dalilan ne yake sa wasu zawarawan shiga rayuwar da ba ta kamata ba, don su samu sanyi a ransu.

A hasashen da ta yi, Hajiya Altine da aka fi sani da shugabar zawarawa ta ce, a duk aure goma da aka ɗaura a Jihar Kano, ana samun mata fiye da ashirin da aurensu ke mutuwa, wanda a dalilin haka lissafin adadin zawarawan da ake da su ke qaruwa a kowacce rana.

Wannan ƙiyasi na Hajiya Altine bai tsaya a Jihar Kano kaɗai ba, kusan akasari jihohin Arewa ana samun irin wannan matsala ta yawan mace-macen aure.

Fatan ta shi ne gwamnati ta rungumi wannan matsala ta kafa hukuma ta musamman da za ta samar da dokoki da za su samar da tsaro, mutunci, da kare haƙƙoƙin aure da ma’aurata, ta hanyar samar da ƙwararru kan halayyar zamantakewa, ilimin shari’a, da kare haƙƙoƙin ɗan Adam, waɗanda za su jagoranci wannan hukuma, yadda za a mayar da al’amarin aure da saki a ƙarƙashinta.

A wani rubutu da ta yi a shafinta na Facebook, fitacciyar marubuciyar nan mai sharhi kan al’amuran da suka shafi zaman auratayya, Zuwaira Dauda Kolo, wacce ake yi wa laƙabi da Likitar Ma’aurata, ta bayyana cewa, zawarci wata riga ce da sai wadda guguwar ƙaddarar ta yayumo ta yafawa ta sigogi da dama.

Babu wata macen da za ta so lulluɓa rigar zawarci don son ranta, sai don karatun abin da littafin ƙaddararta ya shata mata. Wata na yafa rigar zawarci ne sanadiyyar mutuwar miji, wanda ƙarar kwana ke mata ƙarfa-ƙarfan yafawa, ba don ta gaji da zama da mijin ba, sai don ƙaddarar ƙarar kwana. Wata tana yafa rigar zawarci ne daga lokacin da kwanan aurenta ya ƙare, ko ta so ko bata so ba. Ko da kuwa ta tara ’ya’ya sun kai nawa ne haka za ta tsallakesu ta haure. Wasu zawaran na tsallake zunɗe da ƙananan maganganun mutane, wasu kuwa basa haurewa.

Allah Ya sani babu wadda za ta so zama haka, ko kuma a ce ta shafe shekaru ba ta yi aure ba bayan saukar ƙaddarar zawarci, sai dai yanayi da halin rayuwar abokan zaman kan saka fargaba da tunanin ina za a faɗa, kar a je ba a dace ba, musamman waɗanda suka yafa rigar zawarci ta silar rashin dacen abokan zama.

Likitar Ma’auratan ta bai wa matan da ƙaddarar zawarci ta same su shawarar su kame kansu, kuma su tausayawa kansu da zuri’arsu su miƙa wa Allah lamarinsu, su kuma koma gefe su jira sakamakon da zai zo musu daga Ubangiji.

Abin takaici ne ƙwarai yaddaake samun wasu zawarawa da ke shiga harkar karuwanci da shaye-shaye, ko fasiƙanci irin na maɗigo, don saboda rashin aure. A dalilin haka ya sa wasu kan yi wa duk wata bazawara kallon marar kamun kai ko fasiƙa, don haka su ma suna iya zuwa neman ta don su kwashi garavasa. Subhanallah!

Gaskiya ne Bahaushe da ya ce, idan ɓera da sata daddawa ma da wari. Akasarin matan da suke samun kansu a wannan rayuwa, suna shiganta ne a dalilin wasu gurɓatattun mazan da ke hure musu kunne kan za su aure su, amma a maimakon haka sai su hure musu kunne su yi ta lalata da su, daga bisani kuma su rabu da su babu aure babu mutunci. A haka ne ma har wasu za su cigaba da bin maza, saboda sabo da kuma neman abin da za su ci, ko su rufawa kansu asiri.

Sannan wasu mazan da ke sakin mata da yara ba tare da kulawa ko sauke nauyin kula da haƙƙoƙin yaran da aka bar ta da su ba, lallai suna aikata babban zalunci, domin wata a dalilin haka ta ke faɗawa mummunar rayuwa, don ta ciyar da yaran da aka bar mata.

Wasu yaran a dalilin haka suke tashi babu tarbiyya, su zama damuwa a cikin al’umma, saboda ba su tashi sun ga iyayensu a tare ba, kuma ba su samu soyayya da kulawar uba ko iyaye ba.

Haƙiƙa addinin Musulunci ya tanadi ƙa’idoji da sharuɗɗan yin aure da saki da kula da yara, kuma an buqaci kyautatawa mace da abin da za ta riƙe kanta kafin ta samu wani mijin. Amma Musulmai ƙalilan ne suke bin wannan tsarin na addini, don haka ake samun yawaitar zawarawa cikin mawuyacin hali da ƙuncin rayuwa.

Lallai na goyi bayan kiran da shugabar zawarawa Hajiya Altine Abdullahi take yi na buƙatar mahukunta su samar da hukuma ta musamman ba a Jihar Kano kaɗai ba, a dukkan faɗin qasar nan, wacce za ta riƙa kula da al’amarin auratayya da zamantakewar iyali, ƙarƙashin koyarwa ta addini da al’adun al’ummar yanki ko jiha, da kuma uwa uba, dokokin kare haƙƙoƙin ɗan Adam da kundin tsarin mulkin ƙasa.

Abin murna ne da alfahari jin cewa sabon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin dawo da tsohon tsarin nan na auren zawarawa, domin rage yawan zawarawan da ake da su, da kuma tallafawa waɗanda suke buƙatar yin auren babu halin yi.

Har wa yau kuma, ina kira ga masu hannu da shuni su riƙa kai ɗauki wajen tausayawa rayuwar waɗannan mata da iyalansu, ta hanyar ɗaukar nauyin karatun wasu da suke da burin cigaba da karatunsu, ko na ’ya’yansu, ko kuma samar musu da ayyukan dogaro da kansu, kamar sana’o’i ko wasu ayyuka na ƙwadago da za su riƙe kansu, kuma ya ɗauke hankalin su daga duk wata rayuwa marar kyau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *