Ya zame min wajibi na yi shiga ta mutunci don ‘yan baya su koya – Hajara Ɗanyaro

Ni ce mace ta farko da ta riƙe muƙamin shugabar matan Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa”

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya

Ɗaya daga cikin mata da suka kafa tarihi a Jihar Nasarawa, jajirtacciyar mace da ta tabbatar wa duniya mata ma za su iya a ɓangaren siyasa, Hajiya Hajara Ɗanyaro Ibrahim ta samu damar amsar gayyatar da jaridar Manhaja ta yi mata, don tattaunawa da ita a wannan shafi na Mata A Yau.

Mace ce mai kamar maza, da ta iya shanye ƙalubalen da ke tattare da kutsawa cikin maza don neman abinda suke riƙe da shi, don haka rayuwarta za ta iya zama abin koyi ga mata da ke da sha’awar samun makoma irin tata, wato shiga harkar siyasa tare da zama wata tsiya a cikinta.

Honorabule Hajara Ɗanyaro Ibrahim ita ce mace ɗaya tilo da aka zava a kujerar majalisar dokokin Jihar Nasarawa don waƙiltar mazabar Nasarawa ta Tsakiya. Cikakkiyar ‘yar siyasa ce wacce kafin wannan zaɓen ta a matsayin ‘yar majalisar dokokin ta Jihar Nasarawa ta riƙe muƙamai da dama.

Wakilin mu a Jihar ta Nasarawa, John D. Wada, ya samu damar tattuana da ita. Hajiyar ta bayyana muhimman batutuwa da suka haɗa da rayuwarta zuwa gwagwarmayar siyasa da kuma irin nasarorin da ta samu. Baya ga haka, ta bayyana muhimmancin shiga ta al’ada ga macen Arewa da kuma shawarwari da ta bayar domin ‘yan’uwanta mata. Ga dai yadda hirar yakasance:

MANHAJA: Mu fara da jin tarihin rayuwarki a taƙaice.

HAJIYA HAJARA: Sunana Hajiya Hajara Ɗanyaro Ibrahim. An haife ni a garin Nasarawa Hedekwatar Ƙaramar Hukumar Nasarawa anan Jihar Nasarawa. Ina da aure da maigidana mai suna, Alhaji Abubakar Sadik Ubandoma. Muna da ‘ya’ya. Na yi karatun firamari ɗina a Ƙofar Kudu a nan Nasarawa. Daganan na yi sakandare ɗina a G.S.S. Nasarawa. Na cigaba a makarantan kimiya da ƙere-ƙere na tarayya shima anan Nasarawa inda na samu babban difoloma. Daganan na cigaba a babban jami’ar Jihar Nasarawa inda na samu digiri da kuma master digiri ɗina. Daganan na yi aikin banki na wasu lokuta anan Nasarawa inda na kai matsayin akanta.

Daganan sai na shiga harkar siyasa inda na tsaya takaran kansila a inuwar Jam’iyyar UNCP inda aka bani laƙabin ‘fatari mai ba wando kashi’. Ban samu nasara a zaben ba sakamakon maguɗi da akayi mani a lokacin. Daganan na samu muqamin shugabar matan jam’iyyar UNCP. Na kuma kasance mace ta farko da ta riƙe muƙamin shugabar matan jam’iyyar PDP a jihar nan, inda bayan na kammala wa’adina aka sake zaɓe ni a mukamin karo na biyu a shekarar 2000 kenan. Na kuma kasance mace ta farko da tsohon gwamnan jihar nan na farko a mulkin farar hula, sanata Abdullahi Adamu ya naɗa a matsayin Kwamishinan Hukumar Zaɓe ta jihar nan a lokacinsa.

Daganan na shugabanci cibiyar yaƙi da jahilci a jihar nan. Na kuma shugabanci wata ƙungiya mai zaman kanta da ake kira ‘project 50’ wanda ke tabbatar an samu gwamna da bai wuce shekaru 50 ba a jihar nan da qasa bakiɗaya. Da tsohon gwamnan jihar nan maigirma Umaru Tanko Almakura ya fito takara karo na fari a shekarar 2011 ne sai ya kuma naɗa ni a matsayin daraktan wayar da kawunan jama,a na kanfen ɗinsa.

Da ya sake samun nasara karo na biyu sai ya naɗa ni mai ba shi shawara ta musamman akan harkokin jam’iyyun siyasa a jihar nan wato daga shekarar 2012 zuwa 2013 kenan. Na kuma kasance Amiral hajj zuwa Ƙasar Saudiya har sau biyu a shekarar 2012 zuwa 2013. Na kuma riƙe muƙamin babbar mai bai wa gwamna Abdullahi Sule na jihar nan shawara ta musamman akan dukka harkoki da suka shafi nakasassun jihar nan bakiɗaya da kuma jinsi kafin yanzu da aka zaɓe ni mamba a majolisar dokokin Jihar Nasarawa, don wakiltal mazavar Nasarawa ta Tsakiya. Ka ji kaɗan daga cikin tarihin rayuwata.

Waɗannan nasarori da ki ka samu ya sa ni kaiwa ga tambayar ko kin samu wasu sarautu na gargajiya da ki ke riƙe da su?

Tabbas na samu sarautu na gargajiya da suka haɗa da, Garkuwar Matan Nasarawa da Tauraruwan Matan Loko da Jarumar Matan Jihar da Tafisu na Matan Jihar Nasarawa da sauransu.

Za mu so jin wasu lambobin yabo da ki ka samu.

Daga cikinsu akwai Jarumar Matan Afirka Masu Gina Ƙasa da Ambsadan Zaman Lafiya na Ƙungiyar Universal Peace Federation na shekarar 2008 da Mamar Afirka wanda ƙungiyar Election Communication Limited ke bayarwa ta bani kwanakin baya da sauransu.

Sanar da mu ƙasashen da ki ka samu damar ziyarta.

To ni dai kawo yanzu da yardar Allah na ziyarci ƙasashe da dama inda na tafi wasu ayyuka da suka haɗa da Dubai da Indiya da Germany da Saudiya, inda na kai ziyara a Makka da Madina da dai sauransu. Kuma har yanzu nakan tafi ƙasashen a duk lokaci da na samu hutu ko idan wani aiki ya kai ni.

Sanar da mu irin tufafin da ki ka fi sha’awar sawa.

To ni dai na fi sha’awar in ganni cikin tufafi irin namu na matan Arewa kamar dai yadda al’adunmu ta tanada. Ka san anan gida Arewa an fi so a ga mace ta fita cikin mutunci da al’ada ba fita irin ta matan zamani ba. Kuma kamar yadda ka sani ni cikakkiyar ‘yar sarauta ce. Saboda haka ya zame min wajibi in riƙa fita irin ta gargajiya da kuma mutunci don ‘yan’uwana mata da ke tasowa su yi koyi da haka. Saboda haka a taƙaice kamar yadda na bayyana na fi so in gan ni akoyaushe cikin tufafi irin namu na matan Arewa da kuma gargaji. Ka ji wannan kenan.

Za mu so jin irin nasarorin da ki ka cimma a rayuwarki kawo yanzu.

A gaskiya ba wai yabon kai ko wani abu makamancin sa ba a yau zan iya cewa da yardar Allah na samu nasarori da dama a rayuwata. Ka ga kamar yadda na bayyana maka taƙaitaccen tarihina za ka iya lura cewa duk da Ina mace na riƙe ko ince na shugabanci ƙungiyoyi daban-daban da dama ciki har da na siyasa da sauransu. Haka kuma na samu farin jini agun galibin shugabannin jihar nan musamman tsofaffin gwamnoni da suka shuɗe inda suka bani dama daban-daban na ba da tawa gudunmawa a matsayi daban-daban. Duk da Ina mace sun ga cancanta ta inda suka buqaci gudunmawa ta a ɓangaren shugabancin jihar nan.

Kuma kamar yadda ka sani na kawo cigaba da dama musamman a rayuwan ‘yan’uwana mata da nakasassu da sauran jama’a kawo yanzu ta hanyar ƙirƙiro tare da aiwatar da ingantattun shirye-shirye da ke kawo canje-canje masu ma’ana a rayuwansu a kulla-yaumin. Kuma Ina ci gaba da yin haka har yanzu ban fasa ba.

Saboda haka a taƙaice zance gaskiya na samu ɗinbin nasarori a rayuwata don ina ɗaya daga cikin fitattun matan jihar nan waɗanda suke taka rawar gani a yau. Kuma kamar yadda na bayyana maka ba yabon kai ne ko wani abu daban ba, kai kanka kasan abin da nake nufi.

Wacce shawara ki ke da ita ga mata ‘yan’uwannki?

Shawara ta garesu akoyaushe ita ce, su tashi su nemi ilimin addini dana zamani don su ne ginshiƙin zaman duniya. Idan ba su da halin yin haka, sai su rungumi sana’a. kada mace ta dogara ga mijinta kawai a wannan zamani don idan ta yi haka zata fuskanci wulankaci. Haka kuma dole ‘yan’uwana mata su tabbatar suna bai wa ‘ya’yansu kwakkyawar kulawa ta wajen samar musu da ilimi mai inganci don ya taimaka wa rayuwansu a gobe.

Da me ki ke fatan a dinga tunawa da ke?

A gaskiya ni kam zan so a tuna da ni a matsayin mace da ta yi dukka mai yiwa wajen tallafa wa mata musamman waɗanda suka rasa mazajensu da nakasassu da kuma marasa galihu a cikin al’umma. Don na lura da daɗewa cewa waɗannan mutane suna matuƙar buƙatar taimakon kowa cikin al’umma. Shi ya sa Ina so inyi amfani da wannan damar in yi kira na musamman ga masu hannu da shuni a ƙasar nan bakiɗaya da dukka gwamnatocin da ke ƙasar nan dukka mu haɗu mu haɗa kai wurin ganin mun tallafi rayuwar marasa gata.

Don AlIah a riqa taimaka wa marasa galihu cikin al’umma akoyaushe. Kada mu manta cewa lalura ce ta samesu ba yinsu ba ne. Kuma idan mun taimaka musu ba shakka za mu samu lada daga Ubangiji tun anan duniya da kuma gobe ƙiyama.

Mun gode.

Ni ma na gode sosai.