Mun gurfanar da Emefiele a kotu – DSS

Daga NAISR S. GWANGWAZO a Abuja

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana cewa, ta gurfanar da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, a gaban kotu.

Hukumar ta bayyana hakan ne a yayin da ta ke mayar da martani kan hukuncin umarnin Babbar Kotun Abuja, wacce ta umarci hukumar da ta gurfanar da shi a gaban kotu cikin mako guda ko kuma ta sake shi nan take.

A yayin da Mai Shari’a Hamza Mu’azu ke yanke hukuncin kan haƙƙin bil’adama a ranar Alhamis, ya ce, cigaba da tsare mutum komai gajeren lokaci ya saɓa da haƙƙin ɗan adam.

“Idan al’ummar za su iya tunawa, a shekara ta 2022 Hukumar DSS ta nemi umarnin kotu kan tsare shi, domin gudanar da bincike kan wasu manyan laifuka.

“Kodayake ya samu umarnin wata kotun na dakatar da kama shi a Babbar Kotun Birnin Tarayya, Hukumar ta DSS ta kama shi a watan Yuni na 2023 bisa zargin aikata wasu manyan laifukan daban da syka shafi bayanai, waɗanda su ne suka kai ga gurfanar da shi.

“Hukumar tana mai tabbatar wa mutane cewa, za ta zama mai nuna ƙwarewa, adalci da daidaito wajen gudanar da lamarin da kuma sauke nauyin aikinta gwargwadon doka.”

Idan za a iya tunawa, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ne ya dakatar da Emefiele kuma ya bayar da umarnin bincikar bankin na CBN a ƙarƙashin jagorancinsa.

Daga nan ne rahotanni suka nuna cewa, Hukumar ta bi Emefiele har Legas ta cafke shi a lokacin da ake zargin ya na ƙoƙarin arcewa, inda ta izo ƙeyarsa zuwa Abuja.