Samuwar ’yan adam

Daga BASHIR MUDI YAKASAI

Samuwar ‘yan Adam da kuma tattaruwarsu guri guda su waye, su shiga al’amura, tun daga yawo domin neman kalaci, kamar sauran dabbobi da tsintsaye da ƙwari da dai sauran halittu na doran ƙasa da koguna da rafuka har ma da teku wacce ta mamaye duniya.

Masana kuma manazartar kimiyyar samuwar ‘yan Adam na wannan zamani namu sun bayyana cewa, ɗan Adam ya fara bayyana kusan shekaru sama da miliyan biyar da dubu ɗari huɗu (5,400,000), kafin wannan zamanin namu, kuma asalinsu ’yan Afirka ne.

Mutane irinmu, wato masu suffofi da ake gani a yanzu, sun fara, inji waɗannan manazarta, kusan shekaru dubu ɗari da sittin (160,000), sannu a hankali ya watsu a sauran sassa na duniya, musamman guraren da ɗan Adam kan rayu. Misali; a Afirka shi ne a gefen kogin Nilu. Wannan shi yake tabbatar da mutanan Masar na farko baƙaƙe ne.

Bayyanar baƙin mutum a doran ƙasa a yankin da ya raba duniya biyu, wato Ekwaita ya tasamma shekaru dubu talatin da uku (33,000), kuma farin mutum wajen shekaru dubu ashirin da biyu (22,000), ruwan ɗorawa ya bayyana ne a shekaru dubu goma sha biyar (15,000) da suka shuɗe.

Mun yi wannan shimfiɗa ne domin mu fahimci ina muka dosa. Shi mutum da muke gani ya fita daga ɗabi’a ta yawo kwararo-kwararo neman abinci har ta kai ya zauna guri guda a matsayin mashekari, har ta kai ya samar da ruga da ƙauye da karkara da gari da gunduma da birni da kuma daula.

Ya waye ya fito da sana’o’i, kamar farauta da noma da kiwo da neman ma’adanai da ƙira da sassaƙa da fawa da jima da dukanci da rini da gine-gine da kuma girke-girke, kai sana’a ta fi dubu.

Nan da nan dauloli suka bayyana a Afirka da nahiyar Asiya da Gabas ta Tsakiya da Indiya da nahiyar Turai.

Mu a nan Afirka ta Yamma muna da dauloli kamar na Songhai da Ghana da Mali da Borno da ƙasar Hausa da Oyo ga kuma daular Sokoto, jagorancin Mujaddadi Usman Ɗan Fodiyo.

Bayan noma da kiwo, babbar fasaha da kimiyya da ta ɗaukaka ɗan Adam ita ce gano ƙarafa, wato Azurfa da Tagulla da Tama da Kuza da Zinariya da Lu’u-Lu’u da Murjani da Tsakiya da dai sauransu. Wannan Fasaha da kuma kimiyyar sarrafa su ta haifar da wata fasahar ta nemo makamashin da zai narkar da su ta yadda za a sarrafa su zuwa buƙatun shi kansa ɗan Adam.

Daga farkon fari, ɗan Adam kamar yadda manazarta ke cewa, ya fara dogara ne daga wutar daji da ta faru daga tsawa, wato Aradu, saboda ruwan sama, inda sannu a hankali ya fahinci zai iya samar da wuta ta gurza duwatsu har ta kai amfani da ƙirare da karmami da bishiyu iri-iri har ta kai ga akwai lokacin da kimiyyar ɗanyen man fetur da gas ta kankama.

Wannan magana muna yin ta ne ta sama da shekaru dubu da suka shuɗe, domin kuwa fasahar haƙo man fetur da gas a gaɓar koguna a Kasar Sin, wato Chana, da Misira a yankin Gebel Zeit da Cuba da Baka a Kasar Azerbaijan ta yanzu da wasu yankuna na Indiya da Greece da Yankin Pasha da ta haɗa Iran da Iraq na yanzu.

Bayan makamashi da waɗannan ƙasashe suke yi da ɗanyen man fetur suna amfani da shi wajan gine-gine na fadojin sarakunansu da gina hanyoyi, domin ƙawata gari, domin a lokutan dawaki da shanu da kuma raƙuma su ne ababan sufuri suna amfani da ɗanyen man fetur a sinadarin noma, wato taki, wanda a yanzu ake kiran sa takin zamani da kuma wajen haɗa magunguna na gargajiya da kuma sihirice-sihirce na malaman duba.

Yayin da tafiya ta yi tafiya sai ɗanyen man fetur ya zama turare ɗan goma, kamar yadda ake yi wa saniya nagge Kirari da “daɗi goma”, domin kuwa babu abin yarwa a jikinta, ga nama domin buƙatar ɗan Adam kai tsaye, a matsayin abinci mai gina jiki, wato ‘Protein’; ga fata domin masu sana’ar dukanci, ga ƙashi domin masu masana’antu daban-daban har da masu magunguna, ga kuma bayan gida (kashi) saboda masu taki da za a zuba a gonaki.

Idan aka bi mu sannu a hankali za mu kawo muku siyasar haqo ɗanyen man fetur a duniya a nahiyar Afirka da wannan ƙasar tamu ta Najeriya da kuma maƙotanta da kuma yadda man fetur da gas suke taka rawa a harkokin rayuwa da tattalin arziki da zamantakewa.

Za mu kawo muku tarihin kafuwar ƙungiyoyi na ƙasashe masu arzikin man fetur da gas.

Bari mu kwana a nan, saboda ƙaranci lokaci. Sai mun sake saduwa. Na gode.

Bashir Mudi Yakasai, wanda ke zaune a Kano – Najeriya. Za a Iya tuntuvar sa ta: 09074988896 ko 08036827791. ko ta imail: [email protected]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *