Editor

9513 Posts
Cibiyata ta inganta rayuwar jama’a za ta tallafa wa ‘yan Nijeriya – Oluremi Tinubu

Cibiyata ta inganta rayuwar jama’a za ta tallafa wa ‘yan Nijeriya – Oluremi Tinubu

Daga IRAHEEM HAMZA MUHAMMAD Cibiyar Inganta Rayuwar Jama'a, wacce a Turance ake kira da suna 'Renewed Hope Initiative' (RHI) ta ƙuduri aniyar rage ƙuncin rayuwa ga al'ummar Nijeriya. Ta faɗi haka ne bayan taron hukumar gudanarwa ta cibiyar da aka gudanar a ofishinta dake cikin Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock dake Abuja. Wannan sanarwa ta biyo bayan sanarwa da kakakinta Busola Kukoyi ta fitar. Uwargidan Shugaban Ƙasa Ahmed Bola Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu wacce ita ce Shugabar cibiyar don inganta rayuwar jama'a ta ce, an kammala tsari domin ƙaddamar da shirin a jihohi 36 da babban birnin Tarayya, Abuja.…
Read More
Editan Jaridar Blueprint ya zama Sakataren SWAN na ƙasa

Editan Jaridar Blueprint ya zama Sakataren SWAN na ƙasa

An rantsar da Eiditan Jaridar Blueprint na intanet, Amb. Ikenna Okonkwo, a matsayin Sakataren Ƙungiyar Marubuta Labaran Wasanni ta Nijeriya. Amb. Okonkwo ya gaji wannan matsayi ne a wajen Mr. Jude Opara bayan da ya tsaya takarar neman muƙamin ba tare da hamayya ba. Haka nan, Mr. Isaiah Benjamin na Jaridar Leadership shi ne wanda aka rantsar a matsayin shugaban ƙungiyar SWAN na ƙasa bayan babban taron da ƙungiyar ta gudanar a ranar Alhamis, 13 ga Yulin 2023.
Read More
Everton ta ɗauki Ashley Young

Everton ta ɗauki Ashley Young

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Everton ta ƙulla yarjejeniya da Ashley Young kan kwantiragin shekara ɗaya bayan ya bar Aston Villa a bazara. Ɗan wasan, mai shekaru 38, ya zama ɗan wasa na farko da Everton ta saya a ƙarƙashin kocinta Sean Dyche kuma har ya riga ya haɗe da sauran 'yan wasan ƙungiyar a sansanin da suke shirin tunkarar kakar wasa ta bana a ƙasar Switzerland. An fahimci cewa Young ya fara tattaunawa da Luton kuma waɗansu ƙungiyoyi a Saudiyya sun nuna sha'awarsu, amma daga baya ya yanke shawarar komawa Everton. Mai tsaron bayan ya lashe gasar Europa da League…
Read More
‘Yan sanda sun cafke wasu mutane biyar da ake zargin fashi da makami a Jihar Jigawa

‘Yan sanda sun cafke wasu mutane biyar da ake zargin fashi da makami a Jihar Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta kama wasu mutane biyar da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a wana samame suka gudanar a jihar. Wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar, Lawal Shiisu, ya fitar a ranar Laraba a Dutse, ya bayyana cewa an kama biyu daga cikin waɗanda ake zargi da laifin fashin wani direban babur. Ya ce wanda abin ya ritsa da shi, Ashiru Musa, na ƙauyen Kyran, ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Fanisau. Marigayin ya bayyana cewa ‘yan bindigar biyu ɗauke da makamai…
Read More
Majalisar Wakilai ta nemi a soke ƙarin kuɗin jami’a a Nijeriya

Majalisar Wakilai ta nemi a soke ƙarin kuɗin jami’a a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Wakilai ta umarci Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), ta dakatar da ƙarin kuɗin makarantar da jami’o’i suka yi nan take. Wakilin Mazaɓar Dala dake jihar Kano, Ali Sani Madakin Gini (NNPP) ne ya gabatar da wannan ƙudirin a zauren majalisar. Madakin Gini ya ce jami’o’in gwamnatin tarayya sun nunnuka kuɗin makaranta sakamakon hauhawar farashi da ƙarancin kuɗin tafiyarwa da suke samu daga gwamnati. Ya ce daga cikin jami’o’in da suka yi wannan ƙarin akwai Jami’ar Bayero dake Kano (BUK), Jami’ar Nijeriya dake Nsukka (UNN), Jami’ar Jos, da Jami’ar Noma ta Michael…
Read More
Tinubu ne zai bayyana sabuwar ranar da za a yi ƙidayar jama’a – NPC

Tinubu ne zai bayyana sabuwar ranar da za a yi ƙidayar jama’a – NPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) ta ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne da kansa zai bayyana sabbin ranakun da za a gudanar da ƙidayar jama’a da gidaje a Nijeriya. Shugaban hukumar, Nasir Isah Kwarra ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, bayan ya jagoranci tawagar hukumar domin yin bayanin inda suka kwana ga Shugaba Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja. Ya ce ya zuwa yanzu, hukumar ta miƙa rahotonta ga Shugaban, kuma shi take jira ya yi nazari a kai sannan ya yanke hukunci kan lokacin da za a gudanar da ita.…
Read More
Samuwar ’yan adam

Samuwar ’yan adam

Daga BASHIR MUDI YAKASAI Samuwar ‘yan Adam da kuma tattaruwarsu guri guda su waye, su shiga al’amura, tun daga yawo domin neman kalaci, kamar sauran dabbobi da tsintsaye da ƙwari da dai sauran halittu na doran ƙasa da koguna da rafuka har ma da teku wacce ta mamaye duniya. Masana kuma manazartar kimiyyar samuwar ‘yan Adam na wannan zamani namu sun bayyana cewa, ɗan Adam ya fara bayyana kusan shekaru sama da miliyan biyar da dubu ɗari huɗu (5,400,000), kafin wannan zamanin namu, kuma asalinsu ’yan Afirka ne. Mutane irinmu, wato masu suffofi da ake gani a yanzu, sun fara,…
Read More
Mun gurfanar da Emefiele a kotu – DSS

Mun gurfanar da Emefiele a kotu – DSS

Daga NAISR S. GWANGWAZO a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana cewa, ta gurfanar da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, a gaban kotu. Hukumar ta bayyana hakan ne a yayin da ta ke mayar da martani kan hukuncin umarnin Babbar Kotun Abuja, wacce ta umarci hukumar da ta gurfanar da shi a gaban kotu cikin mako guda ko kuma ta sake shi nan take. A yayin da Mai Shari’a Hamza Mu’azu ke yanke hukuncin kan haƙƙin bil’adama a ranar Alhamis, ya ce, cigaba da tsare mutum komai gajeren lokaci ya saɓa da haƙƙin…
Read More
Ya zame min wajibi na yi shiga ta mutunci don ‘yan baya su koya – Hajara Ɗanyaro

Ya zame min wajibi na yi shiga ta mutunci don ‘yan baya su koya – Hajara Ɗanyaro

"Ni ce mace ta farko da ta riƙe muƙamin shugabar matan Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa" Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Ɗaya daga cikin mata da suka kafa tarihi a Jihar Nasarawa, jajirtacciyar mace da ta tabbatar wa duniya mata ma za su iya a ɓangaren siyasa, Hajiya Hajara Ɗanyaro Ibrahim ta samu damar amsar gayyatar da jaridar Manhaja ta yi mata, don tattaunawa da ita a wannan shafi na Mata A Yau. Mace ce mai kamar maza, da ta iya shanye ƙalubalen da ke tattare da kutsawa cikin maza don neman abinda suke riƙe da shi, don haka…
Read More
Mu tausaya wa rayuwar zawarawa

Mu tausaya wa rayuwar zawarawa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A ƙarshen makon da ya gabata ne aka gudanar da bukin Ranar Zawarawa ta Duniya, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta tsayar da ranar kowacce 23 ga watan Yuni don zama ranar da za a tattauna matsaloli da ƙalubalen da mata zawarawa, musamman waɗanda suka rasa mazajensu na aure a dalilin mutuwa ko yaƙe-yaƙe da sauran su, da nufin samar da hanyoyin taimaka musu ko tallafawa halin da suke ciki ta hanyar sana'o'i ko ayyukan yi. Tun a shekarar 2010 ne aka ƙaddamar da wannan rana, wacce ƙasashen duniya da dama suke raya bukinta, ta hanyar shirya…
Read More