15
Jul
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Everton na son ɗan wasan Faransa Moussa Dembele, mai shekara 27, da kuma mai bugawa Leicester, Jamie Vardy, mai shekara 36. Newcastle na ci gaba da tattaunawa da Leicester kan ɗan wasanta na gefe Harvey Barnes, mai shekara 25, kan fan miliyan £30. Ɗan wasan tsakiya a Nice da Wales Aaron Ramsey, mai shekara 32, ya samu tayi mai gwavi daga Saudiyya. Mai buga tsakiya a Tottenham da Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 27, ya kasance matashin da Atletico Madrid ta jima tana zawarci. Chelsea a shirye take ta sayar da Trevoh Chalobah, mai shekara 24,…
