Editor

9513 Posts
Gwamnatin Neja za ta rufe hanyar Minna-Bida ranar Talata

Gwamnatin Neja za ta rufe hanyar Minna-Bida ranar Talata

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Neja ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umaru Bago ta ba da sanarwar za ta rufe babbar hanyar Minna-Bida na sa'o'i shida domin bai wa ma'aikata damar gyara wani sashen hanyar da ya lalalace. Ta ce hakan zai faru ne daga ƙarfe 12 na rana zuwa 6 na yamma na ranar Talata, 18 ga Yuli, 2023. Gwamnatin ta ba da sanarwar ne ta bakin mai bai wa Gwamna shawara kan kafagen sadarwa na zamani, Abdullberqy U Ebbo. Sanar ta ce, "A sani, Gwamnatin Jihar Neja za ta rufe hanyar Minna-Bida ranar Talata, 18 ga Yuli, 2023 na sa'o'i…
Read More
Shin Buhari ya roƙi Tinubu ya dakatar da bincike?

Shin Buhari ya roƙi Tinubu ya dakatar da bincike?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A makon jiya mu ka samu labarin ganawar shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da tsohon shugaba Muhammadu Buhari a Landan. Tun bayan ganawar a ka samu raɗe-raɗin cewa tsohon shugaban ya buƙaci Tinubu ya ja birki ga binciken jami'an tsohuwar gwamnatin. Duk da ba faifan bidiyo ko na sauti da zai ƙarfafa wannan iƙirari; wasu sun yayata yiwuwar hakan bisa zaton ta kan yiwu labari mai kama da haka ya afku. Ficewar shugaba Bubari ƙetare bayan 'yan kwanaki a Daura ya nuna tsohon shugaban na neman wani waje da zai huta. Mai taimaka wa tsohon shugaban…
Read More
Tinubu ya bai wa Gbajabiamila, Akume sabbin muƙamai

Tinubu ya bai wa Gbajabiamila, Akume sabbin muƙamai

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa wani kwamiti na musamman wanda zai maye gurbin hukumomin gudanarwa da aka sauke a makon jiya a ɗaukacin ma'aikatun Gwamnatin Tarayya kafin a naɗa wasu sabbi. Majiyarmu ta rawaito cewa, Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, wato Hon. Femi Gbajabiamila, shi ne wanda Tinubu yaɗa shugabancin kwamitin. Ta ce aikin kwamitin shi ne zaɓowa da kuma tantance waɗanda za a naɗa hukumomin gudanarwa a ma'aikatun da lamarin ya shafa daidai da tsarin gwamnati. Haka nan, wata majiyar daga Fadar Shugaba Ƙasa ta bayyana cewa, Shugaba Tinubu ya ƙalubalanci kwamitin da ya…
Read More
Darussan da ya kamata Nijeriya ta koya daga ƙasashen Vietnam da Malaysia – Adesina

Darussan da ya kamata Nijeriya ta koya daga ƙasashen Vietnam da Malaysia – Adesina

Daga AMINA YUSUF ALI Wani rahoto ya bayyana cewa, Vietnam ta samu nasarar fitar da miliyoyin mutanen ƙasar daga cikin qangin talauci a shekaru 30 da suka wuce ta hanyar fitar da kayayyakinta zuwa ƙasashen waje, inji Akinwumi Adesina, shugaban Bankin Cigaban Afirka. Kasuwancin ƙasar Vietnam ya kama Dalar Amurka biliyan 380 a shekarar 2020. Don haka a cewar sa, ya kamata Nijeriya ta yi koyi da ƙasashen Asiya. Domin Najeriya jimillar kasuwancinta na ƙasar waje ya kama Dala biliyan 33.5 a shekarar 2020. Wato kaso 10 cikin ɗari na Vietnam. Sannan su kuma Najeriya kasuwancinta ya dogara kacokan da…
Read More
Gwamnan Kano ya bada tallafin karatu ga nakasassu zuwa ƙasashen ƙetare

Gwamnan Kano ya bada tallafin karatu ga nakasassu zuwa ƙasashen ƙetare

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da tallafin karatu a ƙasashen ƙetare ga nakasassu a jihar. Gwamnati ta ce nakasassu za su ci gajiyar shirin gwamnatin jihar na bayar da tallafin karatu a ƙasashen ƙetare muddin sun mallaki abubuwan da ake buƙata. Kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana hakan a ranar Alhamis. A cewar Kwamishinan, "Yana daga cikin manufofin gwamnati mai ci na tabbatar da adalci da samun daidaiton samun ilimi ga kowane ɗan jihar, daidai da yarjejeniyar ƙasa da ƙasa." "Tabbas za mu bada tallafin karatu ga waɗanda ke da…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta talauce lokacin da na karɓi mulki – Dauda

Gwamnatin Zamfara ta talauce lokacin da na karɓi mulki – Dauda

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya bayyana cewa, ya tarar da jihar cikin wani mawuyancin hali a lokacin da ya karvi mulki. Lawal, wanda ya bayyana hakan a yammacin Larabar da ta gabata a wani taron tattaunawa da ƙwararru a Jihar Zamfara a Abuja, ya ce, jihar na cikin wani hali kyau a lokacin da ya karvi mulki. “Na yi imani da tarihin jiharmu, wannan shi ne karo na farko da ƙwararru da al’ummar jihar Zamfara ke zuwa don yin cuɗanya da juna. "Na yi farin cikin jin wasu maganganun da aka yi. Lallai abin…
Read More
HortiNigeria ta gudanar da bita ga manoman Kano

HortiNigeria ta gudanar da bita ga manoman Kano

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja A ranar Talatar da ta gaba ta ne ƙungiyar HortiNigeria ta gabatar da taron bita na farko ga manoma a Jihar Kano. HortiNigeria, wata ƙungiya ce da take tallafa wa manoman lambu da dabarun yadda za su inganta nomansu. Ƙungiyar, wacce take samun tallafi daga Ƙasar Netherlands, ta qaddamar da aikin ne ta karkashin cibiyar samar da takin zamani ta kasa (IFDC) tare da wasu abokan hurdar su. A nasa Mohammed Salasi Idris daraktan shirye shirye na Horti Nigeria ya baiyanawa manema labarai cewa wannan shiri ne da gwamnatin netherland ta ɗauki nauyin na…
Read More
Na san talakawan Nijeriya na shan wahalar cire tallafin fetur – Tinubu

Na san talakawan Nijeriya na shan wahalar cire tallafin fetur – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA aAbuja Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya fahimci irin wahalhalun da ke tattare da cire tallafin man fetur, yana mai tabbatar da cewa matakin na da amfani ga ƙasar nan, musamman wajen tabbatar da ci gaba a nan gaba. Tinubu, wanda ya karɓi baƙuncin tsoffin gwamnoni 18 da su ka yi gwamna tare a 1999, a fadar shugaban ƙasa, ya roki 'yan Nijeriya da su ƙara haƙuri. Ya kuma tabbatar wa 'yan ƙasa cewa ana shirin aiwatar da tsarin da zai magance raɗaɗin cire tallafin man fetur. Tinubu ya ce gwamnati za ta ƙara…
Read More
Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin sabbin hafsoshin tsaro

Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin sabbin hafsoshin tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da naɗin shugabannin hukumomin tsaro, waɗanda sabon Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa. Majalisar Dattawa Nijeriya ta tabbatar da sunayen mutanen a ranar Alhamis, 13 ga Yuli, 2023, bayan tantance su a wani zaman sirri da aka kwashe sama da awa ɗaya ana yi. Shugaban Majalisar Dattijai Godswill Akpabio ya ce yayin zaman sirrin, shugabannin hafsoshin sun amsa tambayoyi kan batutuwan da suka shafi tsaro da kuma batutuwan da suka jivanci hakan. Shugaban ƙasar a cikin wata wasiƙa da aka karanta a ranar Litinin a zauren majalisar ya…
Read More
‘Yan ta’adda daga Nijar, Mali, Libya suna ƙaƙaba wa manoman Nijeriya haraji – Ɗan Majalisa

‘Yan ta’adda daga Nijar, Mali, Libya suna ƙaƙaba wa manoman Nijeriya haraji – Ɗan Majalisa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Tangaza/Gudu a Jihar Sakkwato, Sani Yakubu ya koka da cewa mayaqa masu iƙirarin jihadi daga Nijar, Mali da Libya da kuma ‘yan bindiga da ke kai hare-hare a Ƙaramar Hukumar Tangaza ta jihar sun sanya haraji kan manoma a yankin. Yakubu, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da ƙudiri a zauren majalisar a ran around Talata, ya ce mazavar Tangaza/Gudu ta yi wa dazuzzuka biyu ƙawanya; Dajin Tsauna wanda ya ratsa har zuwa Gwadabawa, Illela da Jamhuriyar Nijar da dajin Kuyan Bana wanda kuma ya…
Read More