Gwamnatin Neja za ta rufe hanyar Minna-Bida ranar Talata

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Neja ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umaru Bago ta ba da sanarwar za ta rufe babbar hanyar Minna-Bida na sa’o’i shida domin bai wa ma’aikata damar gyara wani sashen hanyar da ya lalalace.

Ta ce hakan zai faru ne daga ƙarfe 12 na rana zuwa 6 na yamma na ranar Talata, 18 ga Yuli, 2023.

Gwamnatin ta ba da sanarwar ne ta bakin mai bai wa Gwamna shawara kan kafagen sadarwa na zamani, Abdullberqy U Ebbo.

Sanar ta ce, “A sani, Gwamnatin Jihar Neja za ta rufe hanyar Minna-Bida ranar Talata, 18 ga Yuli, 2023 na sa’o’i shida (daga ƙarge 12pm zuwa 6pm) domin bai wa injiniyoyi damar aikin gayaran hanyar.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, akwai kwalbatoci da dama a hanyar da ke buƙatar gyara waɗanda kusan duk shekara sai sun lalace tare da haifar da ƙalubale ga ababen hawa masu amfani da hanyar.

Bisa wannan dalili ne gwamnatin jihar ta ga dacewar ɗaukar matakin gayar kwalbatocin a wannan damina domin samar da mafita na din-din-din, in ji sanarwar.

Gwamnatin ta ce tana bai wa jama’a haƙuri dangane da cikas da za su fuskanta yayin gyaran hanyar.