Shin Buhari ya roƙi Tinubu ya dakatar da bincike?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A makon jiya mu ka samu labarin ganawar shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da tsohon shugaba Muhammadu Buhari a Landan. Tun bayan ganawar a ka samu raɗe-raɗin cewa tsohon shugaban ya buƙaci Tinubu ya ja birki ga binciken jami’an tsohuwar gwamnatin.

Duk da ba faifan bidiyo ko na sauti da zai ƙarfafa wannan iƙirari; wasu sun yayata yiwuwar hakan bisa zaton ta kan yiwu labari mai kama da haka ya afku. Ficewar shugaba Bubari ƙetare bayan ‘yan kwanaki a Daura ya nuna tsohon shugaban na neman wani waje da zai huta.

Mai taimaka wa tsohon shugaban kan labaru, Garba Shehu, ya ce shugaban ya fice ƙetare don yadda mutane su ka yi ta tururuwa zuwa Daura don ganawa da tsohon shugaban.

Zuwan mutanen ya sa ba zai samu sararawa ba bayan mulki na tsawon shekaru 8 don haka ya tafi London. Ga wannan raɗe-raɗin ma har ila yau Garba Shehu ya fito ya yi watsi da hakan cewa ba gaskiya ba ne don a lokacin da ganawar ta gudana ba kowa sai mutanen biyu don haka kenan ba wata shaida kan Buhari ya yi wannan kira.

Koma me za a ce cafkewa ko riqe manyan jami’ai a tsohuwar gwamnatin Buhari da su ka haɗa da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Godwin Emefiele da shugaban hukumar yaƙi da cin hanci EFCC Abdulrasheed Bawa abun dubawa ne.

Haƙiƙa wadannan jami’an biyu sun yi tasiri a tsohuwar gwamnatin har ma wasu ke ganin ko za a sauke su daga mukaman su to ba zai kai ga riƙe su a hukumar bincike ta farin kaya DSS ba.

Shi kan sa tsohon shugaba Buhari a wani jawabi da ya yi tun ya na mulki ya ce duk wani ya neme shi ya ba da shaida a kotu to ya yi kuka da kan sa. Wannan na nuna kowa ya ɗebo da zafi bakin sa.

A hukumance ba a samu ƙarin bayani kan binciken da a ke yi wa jami’an biyu ba sai dai raɗe-raɗin da wasu ke yayatawa da ba abun ɗorarwa ba ne. Abun da ya fito fili shi ne mutanen biyu na nan a hannun DSS kuma duk wanda ya shiga komar DSS to zai sha bincike.

Ita dai hukumar wacce ke kula da bayanan sirri na cikin gida kan dau lokaci ta na binciken waɗanda a ke zargi da aikata laifuka kafin kai wa ga gaiyata ko cafkewa. Shugaban hukumar mai ci Yusuf Bichi na daga jami’an da shugaba Tinubu ya cigaba da aiki da su da hakan ke nuna gamsuwa da yanda su ke gudanar da ayyuka da su ka shafi lamuran tsaron cikin gida.

In ka ga a na binciken mai bincike to rana ta ɓaci kuma zai yi wuya a tuhumi wanda aikin sa bincike ne ba a sane shi da aiki da ƙarfin ofishin sa wajen aikata ba daidai ba.

Mawaƙi Ahmadu Doka na cewa a wata waƙa: “Duk abun da ke ba ka tsoro to wataran shi za ya ba ka tausai” wannan haka ya ke a kwana a tashi ta wuce wasa.

Kai in ma Allan ya yi wa mutum tsawon rai zai ga mutane masu ban tsoro sun zama abun tausayi a hannu tsufa ko rashin lafiya. Tsufa kan sa mai kuzari ya zama ba ya iya takawa da sawayen sa sai da taimakon sanda. Wani abu na ‘yan adam shi ne gwanin wani shi ne abokin adawar wani.

Ni a nan zan ce alqalancin jama’ar ƙasa shi ne mafi tasiri kan yadda shugabanni su ka gudanar da mulki. An yi sa’a irin mulkin dimokraɗiyya a Nijeriya na da wa’adi ga sashen zartarwa mafi tsawo shekaru 8. Tun ture burin tsohon shugaba Obasanji na mulki karo na uku ba a sake samun yanayin wannan yunƙurin ba.

Tsohon ministan jiragen sama Hadi Sirika ya ce za su yi kewar irin salon mulkin shugaba Buhari da ya damka amana ga waɗanda ya naɗa muƙamai da ba su damar amfani da basirar su wajen gudanar da aiki.

Sirika na magana ne kan yadda su ka gudanar da aiki a gwamnatin shugaba Buhari da ta kammala wa’adin mulkin ta a ƙarshen watan Mayu.

Hadi Sirika ya kara da cewa babbar nasara ce samun aiki da shugaba Buhari da mutane su ke yi wa kirari da “MAI GASKIYA” wanda ya ce hakan ya yi tasiri a gwamnatin da tamkar ya sa in shugaban ya naxa mutum muƙami ya na tsammanin zai zama mai gaskiya.

Tsohon ministan ya ce haƙiƙa shugaba Buhari ya ba su dama ba katsalandan wajen gudanar da ofisoshin su.

Da ya ke sharhi kan batun jirgin Nijeriya da kwamitin majalisar dokoki ya zarge shi da saba ƙa’ida ko ma zarmiya; Sirika ya ce shi dai ya yi iya ƙoƙarin sa kuma ba haka ya san majalisa ta ke yanke hukunci ba don shi ma tsohon ɗan majalisar ne. Sirika ya ce daga nan wajen binciken kwamitin kawai ya yanke matsaya cewa an yi ba daidai ba.

In za a tuna kwamitin majalisar dattawa na sha’anin sufurin jirgin sama ya ce sam Sirika bai ma gayyaci kwamitin ko sa hannun sa wajen ƙaddamar da jirgin Nijeriya inda a ka gano jirgin haya ne kawai a ka yi wa fenti don nunawa ‘yan qasa kuma kamfanin ma bai samu lasisin aiki ba tukun.

Sirika wanda na daga ’yan ƙalilan a ministocin gwamnatin Buhari da su ka yi magana kan ayyukan su zuwa yanzu ya ce ko ma gwamnatin Nijeriya ta tsame hannun ta daga kamfanin jirgin to ba zai hana shi aiki ba don ta na da jarin kashi 5% ne kacal don haka masu kashi 95% za su cigaba da aikin kafa kamfanin.

Duk ma wannan ya na zuwa ne lokacin da wasu masu sharhi ke buƙatar gwamnatin Tinubu ta nesanta kan ta daga sauraron masu kamun kafa daga jama’ar shugaba Buhari. Ma’ana kar gwamnatin Tinubu ta ɗauki jami’an Buhari ta sake ba su damar aiki a sabuwar gwamnati don son samu kamar yanda shugaba Buhari ya sauka da ma ficewa daga qasar, su ma muqarraban sa bayan mulkin shekaru 8 su koma gefe su zuba ido wasu sabbin fuskoki su zo don gwada kwarewar su.

In za a tuna muƙarraban Tinubu irin su Ibrahim Kabir Masari na nuna ba jan layi kan bincike da buga misali da kama dakataccen gwamnan babban banki Godwin Emefiele. Masari ya ce bai ga abun da mutan Buhari su ka manta a fadar Aso Rock da yanzu su ke son ɗaukowa ko ci gaba da gashi ba “ko daidai su ka yi ko akasin hakan to su bar fagen hakanan don wasu su zo su nuna bajintar su” Masari ya ce haƙiƙa tsoffin jami’an gwamnatin na tururuwa wajen shugaba Tinubu don neman ya ɗauke su aiki amma hakan abu ne mai kamar wuya don sabon zubi a ke son yi.

Abun jira shi ne ba da belin waɗanda a ka kama ko gurfanar da su gaban kotu.

Yanzu haka ana ta yayata cewa shugaba Tinubu na tattara sunayen waɗanda ya ke son ya naxa a majalisar sa ta zartarwa.

Aƙalla an ce akwai sunayen wasu daga gwamonin da su ka bar gado a bana da kuma wasu ’yan boko da ba a dama da su a gwamnatin Buhari ba. Tun da waɗannan ɓoyayyun bayanai ne ba za a tabbatar da kowaye zai tsallake siradin Tinubu na ƙarshe ba.

Majiya ta ce an tuntubi wasu da a ke son ba su wannan dama. In ma dai za a duba kwarewa to muƙarraban qut da qut na shugaba Tinubu na nuna za a sakawa ’yan siyasa da su ka marawa nasarar shugaba Tinubu baya.

A sharhi na adalci zai yi wuya waɗanda su ka yi ƙaurin suna a gwamnatin Buhari da jama’a ke ganin sun yi zarmiya su iya bayyana a ministocin Tinubu.

Kuma an fahimci shi ma Tinubun ya na da tasa jama’ar da ya kwan biyu ya na siyasa da su da zai so saka mu su. Ai tuni an shaida haka da naɗa Malam Nuhu Ribadu a matsayin mai ba da shawara kan harkokin tsaro.

Ribadu dai shi ya yi wa jam’iyyar Tinubu takarar shugaban ƙasa a 2011 yayin da shugaba Buhari ke narkakkiyar jam’iyyar CPC. In za a tuna Malam Ibrahim Shekarau ya yi wa ANPP takara a zaɓen da tsohon shugaba Jonathan ya lashe bayan nasara kan Atiku Abubakar a zaɓen fidda gwani a inuwar PDP.

Kammalawa;

Daga fara wannan mulki na farar hula ko dawowa dimokraɗiyya a 1999 bayan dogon mulkin soja an samu shugabanni 5 har kan mai ci a yanzu. Biyu daga cikin tsoffin shugabannin tsoffin sojoji ne da sun tava jagaorantar qasar a mulkin soja inda uku fararen hula ne.

Ku duba duk da biyun tsoffin sojoji ne amma tsarin jagorancin su daban. Shi kuma tsohon shugaba Umaru ’Yar’adua bai samu kammala wa’adi ba amma aƙalla an tuno ya yi yunƙurin hana fasa bututun mai ko kawo ƙarshen ta’annatin tsegarun Neja Delta, tsohon shugaba Jonathan ya so ceto tsarin karatun almajirai daga rashin kulawar gwamnati.

Me a ke sa rai daga Tinubu? Wani salon mulkin da ya bambanta da na sojoji biyu ko na ’yan uwan sa farar hula biyu?

Kowa ya yi da kyau zai ga da kyau, ko ba a nan duniya ba haka nan ma wanda ya yi akasin hakan.