18
Jul
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Masu Gidajen Burodi a Nijeriya ta ce za ta ƙara farashin burodi da kashi 15 cikin ɗari daga ranar 24 ga watan Juli. A cikin wata sanarwa da ta fitar, bayan kammala taron shugabanninta na ƙasa, ƙungiyar ta 'Association of Master Bakers and Caterers of Nigeria' ta ce ta ɗauki matakin ne bayan la'akari da nunnukawar farashin kayan aiki. Sanarwar wadda ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Mansur Umar ta ce tashin farashin ya biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tarayya ta yi. A ranar 29 ga watan Mayun 2023…
