Adamu ya yi murabus daga shugabancin Jam’iyyar APC

Daga BASHIR ISAH

Sbugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya miƙa wasiƙar yin murabus daga kujerarsa ta shugabancin jam’iyyar kamar yadda Jaridar News Point Nigeria ta rawaito.

Majiyar News Point Nigeria ta bayya cewar, Sanata Adamu wanda ya zama shugaban APC a watan Maris, 2022, ya miƙa wasiƙar murabus daga muƙaminsa ga Fadar Shugaban Ƙasa gabanin dawowar Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga taron Ƙungiyar Ƙasashen Afirka (AU) da ya halarta a ƙasar Kenya.

Majiyar jaridar ta ce, Adamu ya aike da wasiƙar tasa ce ga Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, da misalin ƙarfe 4 na yammacin Lahadin da ta gabata.

“Ya yi murabus. An miƙa wasiƙar mai ɗauke da sa hannunsa ga fadar villa. Shugaba Tinubu ya yi wa wasiƙar. Amma da yake shugaban ba ya nan ya tafi Kenya don halartar taron AU, an miƙa wasiƙar ga shugaban ma’aikatan fadar shuagaban ƙasa,” in ji majiyar.

Kazalika, wata majiya ta kusa da Adamun ta tabbatar da hakan, inda ta ce, “Shugaban jam’iyyar na ƙasa ya yi murabus ne biyo bayan game kai da wasu na kewaye da Shugan Ƙasa suka yi don tozarta shi a wajen taron da jam’iyyar za ta yi gobe (Talata) da Laraba.”

Sai dai, majiyar ta ƙaryata rahoton cewa Tinubu ne ya buƙaci Adamu da ya yi murabus gabanin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar (NEC) da zai gudana Talata da Laraba.

Da farko jam’iyyar ta ayyana ranakun 10 da 11 ga Yulin da ake ciki a matsayin ranakun da za ta gudanar da taron NEC domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jam’iyyar ciki har da rikicin cikin gidan da Kwamitin Gudanarwa (NWC) ke fuskanta.

Amma daga bisani aka ɗage taron zuwa Talata, 18 da Laraba, 19 ga Yuli.

Wani jigo da aka kafa jam’iyyar da shi ya ce, Adamu ya yi murabus ne bayan da ya samu labarin cewar wasu mutum biyu na hannun daman Shugaban Ƙasa sun shirya yadda za a tozarta shi yayin taron.

“Ya yi murabus ne saboda sun fara tattara amincewar mambobi don tsige shi yayin taro mai zuwa. Ya yi murabus ne domin kare kansa daga tozarci “

Da aka nemi jin ta bakinsa, Adamu ya shaida wa News Point Nigeria ba zai ce komai a kan batun ba har sai Tinubu ya dawo daga taron AU da ya halarta.

“Ba zan yi magana kan batun ba saboda Shugaban Ƙasar ba ya nan,” in ji shi.

Idan dai za a iya tunawa, Sanata Adamu shi ne zaɓin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari don jagorancin jam’iyyar ta APC a wancan lokaci.

Haka nan, kafin zaɓen fidda gwanin takarar shugaban ƙasa na APC Adamu ya bayyanar da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar shugabancin ƙasa ba tare da hamayya ba.

Lamarin da ya tada ƙura a jam’iyyar inda gwamnonin APC daga Arewa suka haɗe kansu tare da nuna rashin yardarsu a kan hakan.

Wanda daga bisani gwamnonin suka ɗunguma zuwa Fadar Shugaban Ƙasa tare da neman a miƙa takarar kujerar shugabancin ƙasa ga shiyyar Kudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *