Talaka bawan Allah

Manhaja logo

Tabbas a halin da ake ciki talakawa na cikin hali na gaba kura baya siyaki.

Na ce talaka bawan Allah ba ina nufin ware ma su mulki da ma su wadata a cikin bayin Allah ba. Dukkanin mu bayinSa ne kuma wadata da talauci duka jarrabawa ce.

Amma dai a wannan zamani amfi ganin damuwa ga ɓangaren talakawa a yanayi da mu ke ciki domin idan mutum bai da wadata hatta a gidansu zai zamo saniyar ware.

Kai a matsayin mutum magidanci muddin bai da wadata ta a zo a gani hatta iyalai sai kaɗan ke zamowa ma su sauraren mai gidan. Allah kai ma mu mafita daga halin kunci da damuwa zuwa samun mafita da aminci.

Talauci na sanya da dama zubar da mutumcin su domin a lamuran mu tausayi da sanin ya kamata ya yi wuya. Kyauta ta zamo ta bani in ba ka.

Yau da dama ba mu tausaya ma junan mu kowa ya zamo tamkar ramin kura idan ya samu wadata sai ya zamo butulu tamkar za ta dauwama.

Mu kuma talakawa da dama an jarrabe mu da hassada wacce ita ma matsala ce a rayuwa.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa. 07066434519.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *