Shugabancin APC: Kyari ya maye gurbin Adamu

Daga BASHIR ISAH

Mataimakin Shuagaban Jam’iyyar APC na ƙasa da daga shiyyar Arewa, Abubakar Kyari, ya maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa biyo bayan murabus da Adamu ɗin ya yi.

Wannan sauyin da jam’iyyar ta APC ta samu ya yi daidai da tanadin kundin dokokin jam’iyyar, wanda ya nuna cewa idan shugaban jam’iyyar na ƙasa ya yi murabus mataimakinsa ya maye gurbinsa a matsayin riƙon ƙwarya.

An ga Kyari ya jagoranci mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar wajen yin taro a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja cikin tsattsauran tsaro a ranar Litinin.

Waɗanda aka gani sun shiga wajen taron tare da Kyari sun haɗa da: Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Ƙa (Kudu), Emma Enukwu; Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa (Arewa maso Yamma), Salihu Lukman; Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa (Arewa maso Gabas), Salihu Mustapha.

Sai kuma Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa (Arewa ta Tsakiya), Muazu Bawa; Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa (Kudu maso Yamma), Issacs Kekemeke; Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa (Kudu maso Gabas), Ejoroma Arodiogu da kuma Mataimakin Sakataren Jam’iyya na Ƙasa, Barr. Festus Fuanter.

A ranar Lahadi Abdullahi Adamu ya miƙa wa Fadar Shugaban Ƙasa wasiƙar ajiye muƙaminsa a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa yayin da ya rage ‘yan sa’o’i kafin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da zai gudana Talata da Laraba.

Majiyarmu ta ce, Adamu ya sauka daga kujerarsa ne bayan da ya samu labarin cewa wasu na kewaye da Shugaban Ƙasa sun shirya tozarta shi a wajen taron da za a gudanar, don haka ya ɗauki matakin sauka daga kujerar shugabancin jam’iyyar don kare kansa daga tozarcinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *