Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Salam. Ina wuni Asas. Allah Ya taimake ki ga dukan lamuranki. Ki taimake ni, yadda Allah ya taimake ki. Mijina da muka yi aure da shi shekara takwas. Da aka kawo ni gidanshi, kullum sai ya ba ni magani zai kusance ni, bai taɓa fashi ba, sai da na yi shakara biyu da aure, har shan maganin ya ishe ni, amma ko na yi ƙorafi sai ya rarashe ni, idan na ƙiya sai ya qi kusanta ta ko da kuwa ya matsu da son yi.

To da iyaye suka fara zancen ba mu haihu ba, mu tafi asibiti, shi ne fa ya sanar da ni ba ya son haihuwa, kuma maganin da yake ba ni na kar na ɗauki ciki ne.

Da daɗin baki ya yaudare ni na biye ma shi har muka qara shekara biyu. Da hankali ya saukar min sosai na fara tunanin abinda zai faru gaba idan na ci gaba da rayuwa a haka. Ana nan sai likitan da muke zuwa ya bada shawarar na yi tsarin iyali da ake yi a asibiti, don maganin bai kamata na ci gaba da shan shi ba.

Ko na sa roba, ko a ɗaure bakin mahaifa da dai wasu da ya yi bayani. Shi ne fa da na dawo na shedama wata abokiyata, ta gaya min akwai yiwar na samu matsala idan na yi a gaba. Ba ma shi ya fi tada min da hankali ba kamar da ta ce akwai yiwar na samu kansa idan na yi, to kuma muna da kansa a gidanmu kinga Ina samun ta cikin sauƙi. To da na gaya mishi mu nemi wata mafita ba wannan ba, shi ne fa ya ce babu wata hanya idan ba wannan ba, kuma dole zan zaɓa, ko yin ko kuma a bakin aurena.

Kuma ya gaya min Allah zai fushi da ni idan har na yi sanadiyyar mutuwar aurena da kaina, kuma zai iya ma zama silar shiga ta wuta, don Annabi Muhammad sallallahu allaihi wa salam ya ce, macen da ta nemi saki daga mijinta ko ƙanshin aljanna ba za ta ji ba.

Wallahi ban san abin yi ba, shi ne na ce bari na neme ki, don na ga shawarar da ki ka ba wa wata a facebook sati uku da suka wuce. Allah Ya biya ki da aljanna.

AMSA:

Da wannan zan iya cewa, barazanar biyu ce gare ki, wanda na fahimci cewa ɗaya kawai ki ka sani zuwa yanzu, don haka bari mu fara da wadda ta fi damun ki, wato yadda tsarin iyali ke iya zama sanadin kamuwa da cutar daji, wato kansa.

Ɗaya daga cikin dalilan da ke sa ake wa mata kallon marasa hankali akwai ɗabi’a ta biye wa abinda muke so ya juya mu tamkar waina, koda kuwa muna da masaniyar inda ake juya mu na da hatsari a rayuwarmu.

Wani sa’in kuwa, ba ma ba wa ƙwaƙwalwarmu damar lalubo mana wata mafita a lokacin da muke tsoron hanyar da ababen da muke so ke ƙoƙarin tunkuɗa mu, duk a cikin irin wautarmu ta kada mu ɓata ran abinda muke so.

Zan buga misali ne da wannan matsala ta ki ‘yar’uwa. Shin kin san da cewa, akwai hanyoyi na ƙayyade iyali da aka tanada don maza? Waɗanda suka jima ana yi kuma ana samun biyan buƙata a yin su? Shin kin tava zama ki ka tambaye kanki ko akwai wata hanya da mijinki zai iya samun biyan buƙatarsa ba tare da ke aikata ba?

Idan kin yi wannan tunanin, ko kin tambaye kanki me ya sa bai kawo shi a cikin jerin damamakin da ku ke da su na cikar burinku ba. Me ya sa mata da yawa ba su san shirin ƙayyade iyali na ɓangaren maza ba, kuma ya aka yi su mazan suka yi gum da baki kansa duk da cewa da yawa sun san da zamansa.

Amsar waɗannan tambayoyin su ne, hangen nesa. Akwai hanyoyin da maza za su iya ƙayyade iyali, duk da cewa ba su kai yawan adadin na mata ba, sai dai a ɓangaren lafiya, sun fi garanti fiye da na mata, ma’ana na maza sun fi rashin barazana ga lafiya yayin da aka yi su.

Hangen nesa kamar yadda na faɗa ne ke hana su yi duk da sun san da zaman su.

Tunanin gaba ta yiwu su buƙaci haihuwa a gaba, kar abin ya kawo masu matsala da zata hana su samu, gwara su danganta abin ga mata don idan an samu matsala za su iya auran wasu su haifa masu, wanda idan sun yi wa kansu, idan an samu matsala dole za su haƙura don ba su da mafita.

Masana da dama sun tabbatar da lafiyar ƙayyade iyali na maza fiye da na mata akan kashi saba’in bisa ɗari, anan me zai sa maza su tilastawa mata yi bayan suke da buƙatar tsayar da haihuwa ba su ba.

Za mu kai ƙarshen wannan tambaya a sati mai zuwa.