Editor

9513 Posts
Tallafin N8000: Tinubu ya ba da umarnin sake fasalin rabo

Tallafin N8000: Tinubu ya ba da umarnin sake fasalin rabo

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gaggawa kan sake fasalin rabon tallafin N8000 da yake shirin raba wa 'yan ƙasa sakamakon cire tallafin mai. Wannan umarni na ƙunshe ne cikin sanarwar da Tinibun ya fitar ranar Talata daddare ta bakin mashawarcinsa Dele Alake. Alake ya ce Tinubu ya sake ba da umarnin a bayyana wa 'yan Nijeriya tanadin da gwamnati ta yi don rage wa 'yan ƙasa raɗaɗin cire tallafin mai. Sanarwar ta ce Tinubu ya ba da umarnin waiwayar tallafin ne saboda yadda 'yan Nijeriya suka bayyana ra'ayoyinsu kan batun. A ranar 13…
Read More
Akwai Matsala!

Akwai Matsala!

Lokacin Jonathan kowa ya san akwai tallafi a cikin aikin Hajji zuwa Gwamnatin Sama. Muhammadu Buhari na zuwa, kamar yadda ya cire tallafin man fetur a yanzu muke shan wannan uƙubar, cirewar ma ba ta fara aiki ba. Kawai ya cire tallafin Aikin Hajji. Hajjin da tsadar babbar kujera ba ya wuce Naira 900,000. Kuma za a ba ka Dala $3000 ko $2500. Ƙaramar Kujera Naira 600,000, za a ba ka tallafi na $1500. Lokacin in ka lissafa ko babbar kujera ka biya bai fi ta tasar maka a kan Naira 600,000 ba. Buhari ya cire tallafin Aikin Hajji. Ina…
Read More
Alhamdulillah, Abubuwa takwas a cikin shekaru takwas!

Alhamdulillah, Abubuwa takwas a cikin shekaru takwas!

Daga ZAINAB AHMAD BINT HIJAZI A cikin shekaru takwas aka rufe bodojin ƙasa da ya zama silar hauhawar farashin kayan masarufin da ya ba wa yunwa gindin zaman dirshan a ƙasa. Yau da yawa ba sa iya cin abinci sau uku a rana. A shekaru takwas rashin tsaro ya yi lalacewar da 'yan bindiga suka iya afkawa jirgin ƙasa, suka ci karensu ba babbaka. 'Yan IPOB suka yi ƙarfin da ba tare da shakkar komai ba suke saka dokar hana fita a wasu ranaku, tare da zubar da jinin mutane ba shakka bare tsoro. A shekaru takwas 'yan ƙungiyar Boko…
Read More
Auri-saki a ƙasar Hausa: Laifin wanene?

Auri-saki a ƙasar Hausa: Laifin wanene?

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a filinku na Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan makon za mu yi magana ne game da auri-saki a ƙasar Hausa. Ko ba a gaya maka ba mai karatu za ka yi wa kanka alƙalanci cewa ƙasar Hausa tana neman zama shalkwatar mace-macen aure a Nijeriya. Domin idan ka dubi sauran ƙabilu, ba su fiye samun wannan matsala ta saurin mutuwar aure da sakewa ba kamar yadda muke yi a nan yankin. A 'yan kwanakin nan ma da aka yi ta zance game da…
Read More
Jihohin Kano, Jigawa, Oyo da sauransu sun ba da hutun sabuwar shekarar Musulunci

Jihohin Kano, Jigawa, Oyo da sauransu sun ba da hutun sabuwar shekarar Musulunci

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatocin jihohin Kano da Oyo da Jigawa da sauransu, sun ayyana Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1445. Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwa mabambanta da jihohin suka fitar a ranar Talata. Gwamna Abba Kabira na Jihar Kano, ta fitar da tasa sanarwar ce ta nakin Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Baba Halilu Dantiye. Inda Gwamnan ya taya al’ummar musulmin duniya murnar shigowar sabuwar shekara ta Musulunci, ya kuma buƙaci ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar da su yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya…
Read More
Yau take sabuwar shekarar Musulunci, 1445

Yau take sabuwar shekarar Musulunci, 1445

Daga BASHIR ISAH A wannan Larabar aka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1445. A ranar Talata Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana Laraba, 19 ga Yulin 2023 a matsayin 1 ga watan Muharram na sabuwar shekarar ta 1445H. Kafin wannan lokaci, Basaraken ya buƙaci al’ummar Musulmi da su nemi jinjirin watan Muharram a ranar Litinin da ta gabata. Watan Muharram shi ne watan farko a kalandar Musulunci, kuma ɗaya daga cikin muhimman watannin da Musulunci yake bai wa fifiko. A wannan wata ne al’ummar Musulmin duniya kan yi azumin nafila a ranakun 9 da 10 ga…
Read More
Yanayin kasuwa ya haifar da ƙarin farashin fetur – Kyari

Yanayin kasuwa ya haifar da ƙarin farashin fetur – Kyari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kamfanin Fetur na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya ce yanayin kasuwa ne ya haifar da ƙarin farashin fetur da aka fuskanta a ranar Talata. Kyari ya bayyana haka ne yayin ganawarsu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ranar Talata a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Ya ce sakar wa ɓangaren mai mara da aka yi, hakan zai sa a riƙa fuskantar hawa da saukar farashin man lokaci-lokaci. Shugaban na NNPCL ya ce batun ƙarin farashin fetur daga N540 zuwa N617 da aka fuskanta ba wai don ƙarancin fetur ba ne, tare da tabbatar wa 'yan…
Read More
Sarkin Musulmi ya ayyana farkon shekarar Musulunci ta 1445

Sarkin Musulmi ya ayyana farkon shekarar Musulunci ta 1445

Daga BASHIR ISAH Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana Laraba, 19 ga Yulin 2023 a matsayin 1 ga watan Muharram na sabuwar shekarar 1445H. Kafin wannan lokaci, Basaraken ya buƙaci al'ummar Musulmi da su nemi jinjirin watan Muharram a ranar Litinin da ta gabata. Watan Muharram shi ne watan farko a kalandar Musulunci, kuma ɗaya daga cikin muhimman watannin da Musulunci yake bai wa fifiko. A wannan wata ne al'ummar Musulmin duniya kan yi azumin nafila a ranakun 9 da 10 ga watan, wato Tasu'a da Ashura don neman kusnci ga Allah Madaukakin Sarki.
Read More
An ƙara kuɗin fetur a Nijeriya

An ƙara kuɗin fetur a Nijeriya

A halin da ake ciki, 'yan kasuwa sun cilla farashin fetur daga N537 zuwa N617 kan lita guda a wasu gidajen mai mallakar Kamfanin Fetur na Ƙasa (NNPCL). An ga wani gidan mai mallakar NNPC s ranar Talata a Abuja yana sayar da fetur N617 kan kowace lita. Ya zuwa haɗa wannan labari babu wani bayani a hukumance daga ɓangaren NNPC ko makamancin haka dangane da ƙarin kuɗin man. Tun bayan da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin mai baki ɗaya a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki a watan Mayu, farashin man ya cilla sama…
Read More
Muna son matasa su karkato da tunaninsu ga sana’o’in gargajiya – Sarkin Askan Jos

Muna son matasa su karkato da tunaninsu ga sana’o’in gargajiya – Sarkin Askan Jos

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A yayin da sana'o'in gargajiya daban-daban ke samun koma baya, saboda sauye sauyen zamani da rashin samun tallafin hukumomi. An fara ganin farfaɗowar wasu tsofaffin sana'o'in Hausawa na iyaye da kakanni da ke ƙoƙarin jawo hankalin matasa ga raya al'adunsu na gado, don samun abin dogaro. Harkar wanzanci na daga cikin waɗannan sana'o'in da daruruwan matasa ke cin abinci a cikinta, sakamakon sabbin jinin shugabanni da aka samu da ke qoqarin inganta sana'ar da kuma ƙara kusantar da ƙungiyar raya harkar wanzanci ga gwamnati, don kawo wa sana'ar cigaba. Wakilin Blueprint Manhaja a Jos, ABBA ABUBAKAR…
Read More