Yanayin kasuwa ya haifar da ƙarin farashin fetur – Kyari

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Kamfanin Fetur na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya ce yanayin kasuwa ne ya haifar da ƙarin farashin fetur da aka fuskanta a ranar Talata.

Kyari ya bayyana haka ne yayin ganawarsu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ranar Talata a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Ya ce sakar wa ɓangaren mai mara da aka yi, hakan zai sa a riƙa fuskantar hawa da saukar farashin man lokaci-lokaci.

Shugaban na NNPCL ya ce batun ƙarin farashin fetur daga N540 zuwa N617 da aka fuskanta ba wai don ƙarancin fetur ba ne, tare da tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa “akwai mai a wadace.”

Kyari ya ce Nijeriya na da mai da zai wadaci ƙasa har tsawon kwanaki 32, don haka ya ce ba a fama da ƙarancin fetur.

A cewar Kyari, sashen kasuwanci na NNPCL ke da alhakin kula da farashin mai, kuma sukan daidaita farashin ne bisa la’akari da yanayin kasuwar man.