Yau take sabuwar shekarar Musulunci, 1445

Daga BASHIR ISAH

A wannan Larabar aka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1445.

A ranar Talata Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana Laraba, 19 ga Yulin 2023 a matsayin 1 ga watan Muharram na sabuwar shekarar ta 1445H.

Kafin wannan lokaci, Basaraken ya buƙaci al’ummar Musulmi da su nemi jinjirin watan Muharram a ranar Litinin da ta gabata.

Watan Muharram shi ne watan farko a kalandar Musulunci, kuma ɗaya daga cikin muhimman watannin da Musulunci yake bai wa fifiko.

A wannan wata ne al’ummar Musulmin duniya kan yi azumin nafila a ranakun 9 da 10 ga watan, wato Tasu’a da Ashura don neman kusnci ga Allah Madaukakin Sarki.