Jihohin Kano, Jigawa, Oyo da sauransu sun ba da hutun sabuwar shekarar Musulunci

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatocin jihohin Kano da Oyo da Jigawa da sauransu, sun ayyana Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1445.

Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwa mabambanta da jihohin suka fitar a ranar Talata.

Gwamna Abba Kabira na Jihar Kano, ta fitar da tasa sanarwar ce ta nakin Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Baba Halilu Dantiye.

Inda Gwamnan ya taya al’ummar musulmin duniya murnar shigowar sabuwar shekara ta Musulunci, ya kuma buƙaci ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar da su yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da bunƙasar tattalin arzikin jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Sannan ya yi kira ga al’umma da su riƙa gudanar da rayuwarsu bisa koyarwar addinin Musulunci tare da yin kyawawan ɗabi’u na kyautatawa da soyayya da kuma haƙuri da juna kamar yadda Annabi Muhammadu (S.A.W) ya karantar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *