Akwai Matsala!

Lokacin Jonathan kowa ya san akwai tallafi a cikin aikin Hajji zuwa Gwamnatin Sama. Muhammadu Buhari na zuwa, kamar yadda ya cire tallafin man fetur a yanzu muke shan wannan uƙubar, cirewar ma ba ta fara aiki ba. Kawai ya cire tallafin Aikin Hajji.

Hajjin da tsadar babbar kujera ba ya wuce Naira 900,000. Kuma za a ba ka Dala $3000 ko $2500. Ƙaramar Kujera Naira 600,000, za a ba ka tallafi na $1500.

Lokacin in ka lissafa ko babbar kujera ka biya bai fi ta tasar maka a kan Naira 600,000 ba.

Buhari ya cire tallafin Aikin Hajji.

Ina cikin alhazan farko da na biya kuɗin Aikin Hajji Babu tallafi. Bayan a da na yi zaton idan Buhari ya hau Mulki zan samu sassauci da rangwame.

Ƙarshe dai, har yanzu da Buhari ya ga mulkinsa na kama-karya tsawon shekaru 8 Babu Wani mutum talaka ko wanda ya biya Aikin Hajji da ya mori wannan tallafin.

Idan akwai wanda ya mori wannan cire tallafin na aikin Hajji don Allah a yi min bayani cikin harshe mai taushi.

Cire tallafi ba laifi ba ne idan talaka zai mora. Amma Matsalar a Nijeriya ba a samun damar morar kuɗin tallafin.

Yanzu kamar tallafin nan fetur ɗin nan da za a ba wa ‘yan siyasa su ƙi yin aiki da shi su azurta kawunansu da Iyalansu. Sai dai mu ji ana cewa, sun saci kaza da kaza. Gara a ba wa su A.A Rano ɗin da su Aliko da sauransu. Aƙalla muna mora ta hanyar sauƙin man fetur ɗin. Kuma suna ɗaukar mutane aiki. Sannan suna taimakawa ta wasu vangarorin da yawa. Ko biya wa mutane kuɗin Hajji da Umrah da ciyarwa da sauransu.

Rayuwa ta ƙara tsada, ga talaka a Nijeriya sakamakon cire wannan tallafin. Abinda ka fi ƙarfi yanzu yana neman ya fi ƙarfinka. Motarka da kake cika Tanki a N10,000 kayi zirga-zirga yanzu sai ka saka N25,000 za ka cika ta. Kuma samun kuɗinka ba lallai in ya ƙaru ba. Allah ya azurta ƙasarmu Nijeriya da shugabanni nagari.

Abdullahi Jibril Dankantoma (Uncle Larabi/Alhaji Larabi,marubu cin ne kuma manazarci. Ya rubuto daga jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *