Alhamdulillah, Abubuwa takwas a cikin shekaru takwas!

Daga ZAINAB AHMAD BINT HIJAZI

  1. A cikin shekaru takwas aka rufe bodojin ƙasa da ya zama silar hauhawar farashin kayan masarufin da ya ba wa yunwa gindin zaman dirshan a ƙasa. Yau da yawa ba sa iya cin abinci sau uku a rana.
  2. A shekaru takwas rashin tsaro ya yi lalacewar da ‘yan bindiga suka iya afkawa jirgin ƙasa, suka ci karensu ba babbaka. ‘Yan IPOB suka yi ƙarfin da ba tare da shakkar komai ba suke saka dokar hana fita a wasu ranaku, tare da zubar da jinin mutane ba shakka bare tsoro.
  3. A shekaru takwas ‘yan ƙungiyar Boko Haram suka iya shigowa Birnin Tarayya, suka fasa gidan gyaran hali suka kwashe mutanensu ba tare da tangarɗa ba.
  4. A shekaru takwas Naira ta yi faduwar da ko a mafarki ‘yan ƙasa ba su tava tunani lalacewar za ta kai hakan ba.
  5. A shekaru takwas talaka ya shiga gigitar kasa sayan fetur da ya tashi daga Naira 76 zuwa 197 a wasu wuraren ma har sama da 300.
  6. A shekaru takwas aka wayi gari da ƙare-ƙaren kuɗin wutar lantarkin da ba a ma samu, aka kuma tabbatar baƙin man (diesel) din ma ya tashi daga 160 zuwa 800, wannan ya zama silar da ba talakan da zai iya saya sai shafaffu da mai.
  7. A shekaru takwas aka yi canjjn kuɗin da ya mai da mutane kamar mabarata da sai da ta kai ta kawo ko sadaka mutum ba ya iya yi.
  8. A shekaru takwas, ƙungiyar Malaman jami’a (ASUU) suka yi yajin aikin watannin da aka bar ɗiyan talakawa da shiga damuwar rashin sanin makomar Ilimin da suke nema.

Allah mun gode maka da ka kawo mu ƙarshen shekaru takwas. Allah Ka sa shekaru takwas su zame mana kaffara. Allah kar Ka maimata ma ‘yan ƙasar nan kwatankwacin wahalhalun shekaru takwas ɗin baya.

Allah kasa wannan da ya karɓi ragamarmu ya zama silar kawo canji mafi alkhairi ga mutanenmu, yankinmu da ƙasarmu gabaɗaya.

Allah kasa wannan sabon shugaba namu Bola Ahmad Tinubu ya zama dalilin da talaka zai samu ‘yanci a ƙasar nan.

Zainab Ahmad Bint hijazi marubuciya ce mai sharhi kan al’amurran yau da kullum. Ta rubuto ne daga Abuja.