Editor

9513 Posts
Mawaƙi Ado Gwanja zai angonce yau Juma’a

Mawaƙi Ado Gwanja zai angonce yau Juma’a

Daga AISHA ASAS An kwana biyu ana raɗe-raɗen shahararren mawaƙin mata, Ado Gwanja, zai yi sabon aure bayan rabuwarsa da matarsa ta farko wadda suke da ‘ya ɗaya tilo da ita, sai dai babu wata hujja da ke nuna gaskiyar zancen, wanda hakan ke sa lokacin ya zo ya wuce ba tare da an ji labarin ɗaura auren ba. Sai dai a wannan karon labarin ya bambanta, domin ya samu isnadi mai ƙarfi da za a iya cewa ƙamshin gaskiyarsa ya rinjaye warin ƙaryarsa, domin labarin ya fito ne daga bakin yayan mawaƙin Alhaji Sa’idu Gwanjo, wanda ya sanar da…
Read More
Majalisa ta yi tir da yadda jami’an kwastam ke buɗe wa jama’a wuta ba bisa ƙa’ida ba a Katsina

Majalisa ta yi tir da yadda jami’an kwastam ke buɗe wa jama’a wuta ba bisa ƙa’ida ba a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Majalisar Dattawa ta Nijeria ta yi Allah-wadai game da buɗe wutar da wasu jami'an hukumar kwastam suka yi a kan mutanen da ba su ji ba, basu gani ba a Jihar Katsina. Majalisar ƙarƙashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio, ta kuma buƙaci hukumar da ta gudanar da bincike kan lamarin. Hakan na ƙunshe ne cikin wani ƙuduri da sanata mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, Sanata Abdul'Aziz Musa 'Yar'adua, ya gabatar a zauren majalisar inda ya buƙaci majalisar ta gaggauta gudanar da bincike bisa yadda jami'an hukumar a jihar Katsina ke amfani da makamai ba bisa ƙa'ida…
Read More
Gwamnan Kano ya yi sabbin naɗe-naɗe

Gwamnan Kano ya yi sabbin naɗe-naɗe

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi sabbin naɗe-naɗe na waɗanda za su jagoranci wasu hukumomin gwamnatin jihar. Waɗanda naɗin ya shafa sun haɗa da: Engr. Ado Ibrahim Umar, Manajin Darakta, Kano Hydo Electricity Development Company (KHEDCO) Alh. Auwalu Mukhtar Bichi, Manajkn Darakta, Kano State Investment and Properties Limited (KSIP). Dr. Farouq Kurawa, Manajin Darakta, Kano State Agricultural and Rural Development Authority (KNARDA) Dr. Tukur Dayyabu Minjibir, Manajin Darakta Kano Agricultural Supply Company (KASCO) Hon. Hussain Sarki Aliyu Madobi, Manajin Darakta, Sustainable Kano Project (SKP) Hon. Sadiq Kura Muhammad, Manajin Darakta, Zoological Garden Kano (ZGK) Engr.…
Read More
1445H: Buhari ya taya Musulmi murnar sabuwar shekara

1445H: Buhari ya taya Musulmi murnar sabuwar shekara

Daga BASHIR ISAH Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa saƙon taya murnar sabuwar shekarar Musulunci ta 1445H ga al'ummar Musulmin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya. Buhari ya miƙa saƙon ne ta hannun mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu. Ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga al'ummar Musulmin Nijeriya da na duniya da su yi koyi da karantarwar Annabi Muhammad (SAW) da sahabbansa. Tare da nusar da Musulmi cewa a sani kowane mahaluki mai ƙaura ne a wannan duniyar. Daga nan, Buhari ya yi kira ga 'yan Nijeriya da a dage da yi wa ƙasa addu'a…
Read More
Mun toshe duk wata kafa da kuɗaɗen gwamnati ke zurarewa – Raɗɗa

Mun toshe duk wata kafa da kuɗaɗen gwamnati ke zurarewa – Raɗɗa

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ce tun hawansa mulki gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin kawo tsarin toshe duk wasu kofofin da kuɗaɗen gwamnati ke sulalewa a jihar. Gwamnan ya sanar da hakan ne a wajen taron bitar da Gidauniyar Jihar Katsina ta shirya na shekarar 2023 da ya gudana a gidan gwamnatin jihar Katsina. Raɗɗa ya kuma ce gwamnatinsa ta kuma ɓullo da tsare-tsare masu inganci da za ta tunkari matsaloli da ƙalubalen da jihar ke fuskanta musamman a sha'anin tsaro, aikin gona, zaman kashe wando a tsakanin matasa da sauransu. Ya bayyana…
Read More
Gwamna Lawal ya taya Musulmin Zamfara shiga sabuwar shekarar 1445

Gwamna Lawal ya taya Musulmin Zamfara shiga sabuwar shekarar 1445

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya miƙa saƙon taya murna ga al'ummar Musulmin jihar dangane da shigowar sabuwar Musulunci ta 1445. Gwamnan ya yi wa Musulmin jihar, na ƙasa da ma duniya baki ɗaya fatan alheri da kuma murnar ganin sabuwar shekarar, tare da kira a gare su da su duƙufa da addu'ar samun zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa a jihar. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya sanya wa hannu. Ya ce, "Sabuwar shekarar ta Musulunci na nuni da hijirar da Annabi Muhammad (SAW) ya…
Read More
Gwamnan Zamfara ya yi wa Dahiru Mangal ta’aziyyar rasuwar matarsa a Katsina

Gwamnan Zamfara ya yi wa Dahiru Mangal ta’aziyyar rasuwar matarsa a Katsina

Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ziyarci Katsina don yin ta'aziyya ga Shugaban Kamfanin Jirgin Max, Alhaji Dahiru Barau Mangal bisa rasuwar matarsa. Shahararren ɗan kasuwar ya rasa matarsa Aisha ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata a babban birnin tarayya, Abuja. Gwamna Lawal a wata takardar manema labarai da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa wacce iyalanta za su yi kewar rashinta matuƙa. Haka nan ya yi addu'ar Allah Ya yi wa marigayiyar sakamako da masauki a Aljannah. "Mun zo ne domin yin jaje da ta'aziyya na…
Read More
Raɗɗa ya miƙa wa majalisa sunayen kwamishinoni don tantance su

Raɗɗa ya miƙa wa majalisa sunayen kwamishinoni don tantance su

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya miƙa wa Majalisar Dokokin jihar jerin sunayen mutane 20 domin tantance su a matsayin waɗanda za su shugabanci ma'aikatu daban-daban a jihar. Sunayen wanda mai taimaka wa gwamnan kan kafofin yaɗa labarai ya aike wa Majalisar a ranar Laraba sun haɗa da tsoffin kwamishinoni biyar na gwamnatin da ta gabata. A yayin zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin Kakakinta, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, an bayyana sunayen kwamishinoni 20 da kuma wasu shugabannin hukumomi biyu da suka haɗa da hukumar tattara kuɗin haraji ta jiha wadda aka bayar da…
Read More
Mu sake waiwayar illolin rabuwar aure

Mu sake waiwayar illolin rabuwar aure

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Shekaru fiye da ashirin da suka gabata na taɓa yin wani nazari da ya ja hankalin masu karatu a jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, wanda daga baya aka sake buga shi a wasu jaridun Hausa. A lokacin na yi rubutu ne game da illolin rabuwar aure, wanda na duba ɓangarori daban-daban, kama daga rayuwar iyalin da aka rabu, musamman yaran da aka haifa tare da kuma al'umma baki ɗaya. Abin da a qarshen nazari na nuna cewa, kuskuren da wasu ma'aurata ke yi shi ne suna duba matsalar kansu ce kawai ba sa tunani kan abin…
Read More
Tafiyar biri a yashi, akwai matsala!

Tafiyar biri a yashi, akwai matsala!

Daga ABDULLAHI JIBRIL LARABI Har yanzu muna cikin al'ummar da ke cike da gurgun tunani. Hakan shi ya sa zai yi wahala mu fita daga cikin matsalolin da suke tattare da mu. Al'ummar da tun zamanin iyaye da Kakanni ake da matsaloli cinkus a gidajen aure har yanzu kuma an kasa shawo kan kaso mafi rinjaye na matsalar sai ma ƙara cigaba da kullum take yi. A wannan yanayin da muka tsinci kanmu a ciki bai kamata mu mai da hankali ko da a Soshiyal midiya kan maganar yi wa miji wanki ba akwai matsalolin da suka sha gaban yin…
Read More