Mu sake waiwayar illolin rabuwar aure

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Shekaru fiye da ashirin da suka gabata na taɓa yin wani nazari da ya ja hankalin masu karatu a jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, wanda daga baya aka sake buga shi a wasu jaridun Hausa. A lokacin na yi rubutu ne game da illolin rabuwar aure, wanda na duba ɓangarori daban-daban, kama daga rayuwar iyalin da aka rabu, musamman yaran da aka haifa tare da kuma al’umma baki ɗaya.

Abin da a qarshen nazari na nuna cewa, kuskuren da wasu ma’aurata ke yi shi ne suna duba matsalar kansu ce kawai ba sa tunani kan abin da zai iya biyo baya ba, a karan kansu ko kuma ga iyalin da za su bari cikin ƙunci.

Babu shakka, ba duk ma’auratan da ke rabuwa ne, suke yanke hukunci ido rufe ba, wasu kan ɗauki lokaci ana nazari da auna abubuwan da za a iya samun maslaha a kansu, har sai abin ya ƙure ne sannan ake haƙura a yanke shawarar rabuwa gaba ɗaya. Wasu ma da ke rayuwar birane ko ’yan boko, za ka ga har wajen qwararru ake zuwa, wato masana ilimin zamantakewa da sasanta tsakanin ma’aurata, don neman shawara da shiga tsakani, ana kashe maƙudan kuɗaɗe, don dai a kaucewa rabuwa da juna a ceto aurensu da ke gab da rushewa.

Don haka ba za mu zargi duk masu yanke shawarar rabuwa da juna a kan masu rashin hankali ko tunani ba. Za mu ba su uzuri kan cewa, mai yiwuwa abin da ya koro vera cikin wuta ne ya fi wutar zafi.

A makon da ya gabata na samu labarin rabuwar auren da ya girgiza ni matuƙa, har iyali biyu, waɗanda a baya nasan suna zaune lafiya da juna ko kuma dai ana zaune cikin kyautatawa da haƙuri da juna. Kusan dukkan su sun kasance cikin aure kimanin shekaru goma sha takwas ko kusa da haka, sun haifi yaran da suka girma suka fara mallakar hankalin kansu. Amma kwatsam, sai muka ji ai sun rabu da juna.

Ɗaya daga cikin su wanda babu laifi idan na ambaci sunan su a nan kasancewar labarin rabuwar ya yi yawo a jaridu da sauran kafafen sadarwa, shi ne rabuwar auren Malam Al-Ameen Ciroma, xan jarida kuma jarumin finafinan Hausa a Masana’antar Kannywood, da tsohuwar matarsa Wasila Isma’il, wacce ita ma tsohuwar jarumar finafinan Hausa ce. An ma bayyana cewa, aurensu shi ne mafi daɗewa a cikin auratayyar da aka yi tsakanin jaruman masana’antar.

Kodayake, kawo yanzu ba ni da masaniya kan dalilan da suka haifar da rabuwa a dukkan auren da nake magana a kai, amma har ga Allah na san su kansu da suka rabu suna cikin wani yanayi na alhini, da jujjuya abubuwan da suka faru a baya, ko suka janyo rabuwar aurensu, wanda za a iya cewa ya faru kamar a mafarki, kuma bisa ƙaddara. Ko kuma kamar yadda wasu ke cewa, yadda kowacce halitta ke da rai haka aure ma yana da nasa wa’adin, wanda idan ya zo ƙarshe babu makawa sai an rabu.

Za ta iya yiwuwa wani auren ya daxe da rabuwa a zukatan ma’auratan, domin wasu abubuwa na auratayya a tsakanin su tuni suka yanke, sai dai kawai ba a yanke hukunci da sanar da shaidu ba ne, sai da ƙarshen wa’adin ya zo. Wani auren kuma cike yake da zarge-zarge marasa daɗi, da aibata juna ko jifan juna da sunaye iri-iri na ɓatanci da muzantawa, alhalin a baya an nuna wa juna soyayya da kulawa. Wasu kuma dalilai ne na cin zarafi, zalunci, da tozartawa, inda za ka ji ana cewa ai da wannan zaman gara rabuwar saboda kada wani ya kashe wani, sakamakon azabtarwar da wani ke yi wa wani.

Ko dai a riƙa nuna shi mijin ne yake dukan matarsa, da wulaƙanta ta, ko tauye mata haƙƙoƙinta da ke jefa rayuwarta cikin mummunan hali. Ko kuma ita matar ce take wulaqanta mijin, aibata shi da cin zarafinsa, a wasu lokuta, walau da duka ko da harshenta. Tun mijin na ɓoyewa har dai ya iya fitar da abin da ake yi masa a ɓoye, jama’a su fahimci uƙubar da yake ciki, amma ya kasa bayyanawa saboda ana ganinsa namiji, kar a gane gazawarsa.

Matsaloli daban-daban ne ke haddasa rabuwar aure, kuma kowa da dalilinsa. Kamar yadda ake cewa, babu wani aure da ya yi kama da na wani to, haka ko a wajen rabuwa, za ka tarar kowa da nasa dalilin. Wani dalilin ma idan mutum ya ji sai ya yi dariya kafin ya fara tambayar garin yaya haka ta faru, domin dalili ne da za a iya sasantawa cikin ruwan sanyi a warware shi. Wani kuma abubuwa da dama ne aka riqa tara su har suka yi yawan da ba a iya warware su lokaci guda ba, sai dai a rabu idan ya so in suna da rabon sake komawa zaman aure a sake dawowa.

A wajen waɗanda suke da wayewar zamani su kan je har wajen alƙali a raba zaman na wani lokaci, ba da nufin saki ba, sai dai don a bai wa kowanne vangare damar zuwa ya yi nazari da tunani, kuma a bai wa zuciya da tunani zarafin da za ta huce a samu natsuwa, kafin a koma a sake fuskantar juna.

To, ko ma dai wanne dalili ne, ko wanne salo ne aka bi wajen rabuwar, za mu iya fahimtar cewa ba abu ne mai daɗi rabuwar aure ba. Saboda da zarar an yi aure an hayayyafa na tsawon wasu shekaru, ana ɗauka kan cewa an zama ɗaya, ko da an rabu ba rayuwa ba za ta sake armashi kamar a baya ba. Nauye nauyen kula da yara da damuwa a kan karatunsu ko tarbiyyarsu, nan ma wata jarrabawar ce.

Su kansu yaran da aka rabawa hankali, ko aka canza musu gida da makaranta, da abokan rayuwa suna shiga cikin damuwoyi iri-iri. Daga ciki akwai matsalar taɓarɓarewar tarbiyya, shaye-shaye, rashin ƙoƙari a makaranta da gudun shiga mutane. Wani lokaci har da yawan zafin rai da shiga rigima, ko cin zalin wasu yaran.

Abin takaici ne yadda wasu musamman mata ke bayyana cewa, su ne suka nemi a raba auren don sun gaji da ganin baqin ciki, sun gwammaci zaman zawarci da cigaba da ganin wulaƙancin da suke cewa suna gani a gidajen aurensu. Alhalin kuwa addinin Musulunci ya tsawatar sosai kan matan da suke neman mazajensu na aure su sake su. Wani lokaci kuma wasu ne a cikin mata ake samu da suke hurewa ‘yan uwansu mata, masu haƙurin zaman aure, kunne kan cewa su bar gidan, in ba so suke rayuwarsu ta lalace ba. Su riqa karanto musu wasu abubuwa na rashin tabbas da kwaɗaitar musu da rayuwar ’yanci da walwala a rayuwar zawarci. Sai bayan sun fito daga gidan miji su tarar da rayuwar ba a yadda suka zata ba.

Ƙalilan ne a matan da suke barin aurensu don ganin suna shan wahala, suke sake samun wata damar ta sake yin aure ko kuma kafa wani kasuwanci da zai riƙa kawo musu riba, suna kula da kansu, da ’ya’yansu. Wasu kuwa sai dai gyaran Allah, rayuwar ƙara lalacewa take yi, har ma su gwammaci gara da a ce su koma ɗakin aurensu da zaman da suke yi na rashin tabbas, da yaudarar manema da ke jefa su a rayuwar zinace-zinace da sayar da mutunci.

Ban sani ba ko saboda qaruwar talauci da ƙuncin rayuwa ne, ya sa darajar aure ke ƙara zubewa a idanun wasu matan da ke ganin babu abin da aure ke tsinanawa rayuwar su in ba takaici da wahala ba, don haka ma za ka yi ta ji a maganganunsu da rubuce-rubucensu a yanar gizo, suna nuna gazawar aure da lalacewar maza, ko muguntarsu a cewar wasu matan, wanda ke sa suna jin auren yana fita a ransu. Kuma hakan ba ya rasa nasaba da yadda wasu mazan suke yi wa auren riƙon sakainar kashi da sakewa mata da ’ya’ya wahalhalun aure da kula da kansu.

Nauyin da sharuɗɗan kula da haƙƙoƙin aure suka ɗora su kan maza. Amma yanzu a mafi yawan gidaje mata ne ake bari da ɗawainiya mazan sun juya musu baya, babu ko tallafawa. Sai ka ga mace bazar-bazar kamar za ta yi hauka, tana fafutukar yadda za ta nemawa iyali abin da za su ci ko kuɗin makaranta, saboda uban wanda ya kamata ya zama jagora a gidansa halin yau da mutuwar zuciya sun sa ya yi watsi da buƙatunsu.

Lallai wannan rubutu, yana so ya ƙara zaburar da iyaye, musamman ma’aurata da su dubi girman Allah, su tsaya su kula da gyaran gidajensu, a daina watsi da haƙƙoƙin da Allah ya ɗora mana.

A riƙa tausayawa juna ana kyautatawa, don a samu rabon duniya da lahira. Mata su daina sauraron waɗanda suka fitar da tsammani daga samun jin daɗin aure, hurewa wasu kunne don su ma su bi sahunsu suna gantali a titi, wanda babu inda zai kai su sai halaka.