Tafiyar biri a yashi, akwai matsala!

Manhaja logo

Daga ABDULLAHI JIBRIL LARABI

Har yanzu muna cikin al’ummar da ke cike da gurgun tunani. Hakan shi ya sa zai yi wahala mu fita daga cikin matsalolin da suke tattare da mu.

Al’ummar da tun zamanin iyaye da Kakanni ake da matsaloli cinkus a gidajen aure har yanzu kuma an kasa shawo kan kaso mafi rinjaye na matsalar sai ma ƙara cigaba da kullum take yi.

A wannan yanayin da muka tsinci kanmu a ciki bai kamata mu mai da hankali ko da a Soshiyal midiya kan maganar yi wa miji wanki ba akwai matsalolin da suka sha gaban yin wanki mun kasa magance su.

Akwai matsalolin tattalin arziki wanda shi ya kamata mu mai da hankali a kai. Yaya za mu faɗaɗa ƙwaƙwalwarmu wajen samar wa kanmu sauƙin rayuwa da kuma samun abubuwan yi da za su inganta rayuwarmu da ta iyalinmu.

Yanzu maganar rage raɗaɗin talauci ya dace mu yi da kuma yadda za a inganta zaman auren ba sai an ɗora wa wani sashi hidimomi masu yawa ba.

Na yi mafi yawancin mutanen da suke magana a kan yi wa miji wanki matan da yawansu mazajensu ba sa aikin da ya haura N100,000 a wata. Wasu suna da yara kamar guda huɗu, wasu uku ko biyu.

To wannan N100,000 din misali in har a wannan zamanin ne da rabin buhun shinkafa ya tasamma Naira 20,000, katan ɗin taliya ya tasamma Naira 10,000, makaroni ya tasamma Naira 10,000. Man girki fari ya tasamma Naira 8000, lita 5 shi ne ƙaramin galan. Haka shi ma manja. Maggi tauraro Naira 700. Gishirin Mista Chef Naira 200 da ɗoriya.

Banda Omo da sabulun wanka. Banda kuɗin mota ko na mai da mijin zai zuba a mashin ɗinsa ya kai yara makaranta, ya wuce ofis ko kasuwa, ko wajen aikin hannu. Banda fa maganar biredi kullum za su iya Cinye na Naira 500 zuwa sama. Daman Yanzu doya da ƙwai ko dankali da ƙwai ya fara zama tarihi a gidaje da yawa. Banda Hidimar siyen magani ko wata lalurar.

To don wani ya taimaki wani da wanki har wata tsiya ce da za a zo Soshiyal midiya ana tattaunawa a kanta?. Idan Mijinki aiki yake ko kasuwar ma yake zuwa ko wata sana’ar hannu yake zai bar gida tun 8 ko don kai yara makaranta.

Wani zai ɗan dawo a gurguje ya karya ya shirya ya fita. Ba ki San Gwagwarmayar da yake a ofis ko wajen sana’arsa ba. Zai ci abinci na rana a wajen aikin duk fa cikin wannan albashin. Kuma ke ce wadda idan bai kawo wani abu daga cikin kayan da za a girka a ci ba za ki fara yi masa ƙorafi. To don kin rage masa kuɗin kashewa ta guskar wanke masa kayansa ai ba laifi ba ne.

Daman ba cewa aka yi dole ba. Wannan kyautatawa ne da rage raɗaɗi. Ke ma idan kina aiki ko wasu sana’o’in cikin gidan ba ma zai yiwu a yi maganar kiyi wa Miji aiki ba. Daman yin wankin in zai yiwu ana magana ne a kan matan da suke zaman gida ziryan. Shi ma kuma ba a ce dole ba. Kyautatawa ne kamar yadda yake kyautata miki shi ma mijin ta wasu fuskokin.

In kuka haze wancan lissafin na sama za ku ga a wata mai wancan iyalin ba lallai N100,000 a wannan tsadar rayuwar da Shugabannin Nijeriya suka ƙaƙaba mana za ta ishe shi rayuwa har ya yi walwalar za ta ajiye wani abu ko ya ɗauki kuɗi ya kai a yi masa wanki da guga.

Macen da take neman kuɗi ko aiki daman ba ta da lokacin yin wani wanki. Kuma su ne suke maganar ba wai da wadanda ba sa aiki ko sana’a suke ba. Don haka kar wasu matan da suke zaman gida ba aiki ba sana’a su ara su yafa.

Don Allah mu san Darajar Iyalanmu a wannan TAFIYAR BIRI A YASHIN DA AKE YI. Akwai mata dubunnai da aka mutu aka bar su da marayu wasu kuma aka sake su ba su da gata, ba su da yadda za su yi, WANKAU suka zava ya zama sana’ar da za su ci da kansu da yaransu. Kuma ba abinda ya same su.

Abdullahi Jibril Larabi (Uncle Larabi). Marubuci ne kuma manazarci. Ya rubuto ne daga jihar Kano.
Lambar waya: 08065418892

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *