Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta kama wasu mutane biyar da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a wana samame suka gudanar a jihar.
Wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar, Lawal Shiisu, ya fitar a ranar Laraba a Dutse, ya bayyana cewa an kama biyu daga cikin waɗanda ake zargi da laifin fashin wani direban babur.
Ya ce wanda abin ya ritsa da shi, Ashiru Musa, na ƙauyen Kyran, ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Fanisau.
Marigayin ya bayyana cewa ‘yan bindigar biyu ɗauke da makamai ne suka tare shi inda suka tafi da babur ɗinsa mai lamba AYE 918 UP Ogun.
Shiisu ya ce, ‘yan sintiri da ke aiki a yankin Fanisau sun yi ƙoƙarin bin sawun ‘yan fashi da makamin inda suka samu nasarar ƙwato babur ɗin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana sunayensu ‘yan Fashin da suka haɗa da Tijjani Haruna mai shekaru 19 da kuma Baballe Abdulrahman mai shekaru 25.
Kakakin ya ce jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga na ƙaramar hukumar Ringim sun kuma kama wasu mutum uku da ake zargi.
Waɗanda ake zargin su ne, Ahmadu Audu da Shuaibu Bayeri da kuma Samaila Musa, waɗanda suka fito daga ƙauyen Majiyar Kirdau a ƙaramar hukumar Ringim, an kama su ne bisa laifin haɗa baki, fashi da makami da kuma haddasa munanan raunuka.
Shiisu ya ce, waɗanda ake zargin sun amsa laifin sace babura da dama a ƙaramar hukumar Ringim da kewaye.
Ya ƙara da cewa, “Sun kuma ambaci wasu gungun ‘yan bindiga da kuma wanda suke taimaka musu a ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano.”
Shiisu ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike.