Editor

9513 Posts
Zaɓen gwamnoni: Kowa ya shiga tetayinsa, gargaɗin ‘yan sandan Kano ga masu shirin tada tarzoma

Zaɓen gwamnoni: Kowa ya shiga tetayinsa, gargaɗin ‘yan sandan Kano ga masu shirin tada tarzoma

Daga RABIU SANUSI a Kano Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta gargaɗi duk wasu dake da niyyar haifar tashin hankali a zaɓen gwamnoni da majalisar jihar da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Jami'in Hulɗa da Jama'a na rundunar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa ya fitar a ranar Lahadi. Jami'in ya ce dangane da bayanai da rundunar ke samu na ɗaura ɗamarar da wasu shugabanin siyasar suke yi na yunƙurin yin ta'ammali da 'yan dabar siyasa don tayar da tarzoma yayin zaɓe mai zuwa a jihar. Sanarwar ta ce, "kamar yadda…
Read More
Zaɓen Shugaban Ƙasa bai cimma muradin ‘yan Nijeriya ba – Amurka

Zaɓen Shugaban Ƙasa bai cimma muradin ‘yan Nijeriya ba – Amurka

Daga BASHIR ISAH Mako guda bayan gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisun tatayya a Nijeriya, ƙasar Amurka ta ce zaɓen bai cimma muradun 'yan ƙasar ba. Cikin sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, Jakadiyar Amurka a Nijeriya, Mary Beth Leonard, ta ce, da yawan 'yan Nijeriya ransu a ɓace yake game sa zaɓen yayin da wasu su ke cikin murnar lashe zaɓe. “A bayyane yake cewa baki ɗaya, zaɓen da ya gudana ran 25 ga Fabrairu bai cimma muradun 'yan Nijeriya ba. "'Yan Nijeriya sun nuna ƙwazo yayin zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu wajen tabbatar da…
Read More
Ɗan sanda ya kashe kansa bayan bindige matarsa

Ɗan sanda ya kashe kansa bayan bindige matarsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani ɗan sanda ya kashe kansa bayan da ya harbe uwar gidansa har lahira a garin Ilorin na Jihar Kwara. Mummunan lamarin ya faru ne a Chapel Redemption, UMCA, yankin Agba Dam na cikin garin Ilorin, a ranar Alhamis, 2 ga Maris, 2023. Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun sanar da cewa ɗan sandan ya aikata wannan aika-aika ne a kan batun wani yaro da ya taso a danginsu. Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa da dawowarta makarantar da yaronta, ɗan sandan ya kama matar da aka kashe, kuma…
Read More
’Yan sanda sun kama ɓarayi 50 a gobarar kasuwar Maiduguri 

’Yan sanda sun kama ɓarayi 50 a gobarar kasuwar Maiduguri 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ‘yan sandan Jihar Borno ta kama wasu mutane 50 da ake zargi da yin sace-sace a kasuwar Monday Market ta Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), Kamilu Shatambaya ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin a ranar Laraba a Maiduguri. Ya ce jami’an rundunar da aka tura domin kare rayuka da dukiyoyin da gobarar ta afku a kasuwar, sun kama waɗanda ake zargin ne a ranar 26 ga watan Fabrairu. Ya ce waɗanda ake zargin sun yi awon gaba da kadarorin waɗanda abin ya shafa…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun kashe mahaifin shugaban ƙaramar hukuma a Kano

Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun kashe mahaifin shugaban ƙaramar hukuma a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance su ba sun kashe Hakimin Maigari a Ƙaramar Hukumar Rimin Gado a Jihar Kano, Alhaji Ɗahiru Abba. Sabon babban sakataren shari’a na Jihar Kano, Alhaji Sanusi Abbas, wanda kuma ɗan gidan marigayin ne ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda majiyarmu ta Justice Watch ta ruwaito. A cewarsa, marigayin shi ne Hakimin ƙauyen Maigari, kuma uba ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Rimin Gado na yanzu, Barista Munir Dahiru Maigari. “Marigayi Maigari ya rasu ne bayan da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka…
Read More
Tinubu a matsayin shugaba da zai jagoranci Nijeriya

Tinubu a matsayin shugaba da zai jagoranci Nijeriya

An ayyana Bola Tinubu, mai shekara 70 a duniya a matsayin mutumin da ya lashe zaɓen shugaban ƙasan Nijeriya mafi ɗaukar hankali tun bayan mulkin sojoji a shekarar 1999. Tinubu, wanda ake kallo a matsayin jajirtaccen ɗan siyasa da ya kawo cigaba a jihar Legas, cibiyar kasuwancin ƙasar, ya yi nasara ne kan babbar jam'iyyar adawa mai fama da ɓaraka da kuma ɗan takara na uku da ke da magoya baya matasa. A ranar 29 ga watan Mayu, na wannan shekara ta 2023, zai maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari a kan mulki. Nijeriya, ƙasa mafi yawan al'umma a Afirka na…
Read More
Arsenal ta lallasa Everton karo na 100 a tarihi

Arsenal ta lallasa Everton karo na 100 a tarihi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Arsenal ta ci Everton 4-0 a kwatan wasan Firimiya da suka kara ranar Laraba a Emirates. Wasa ne da ya kamata su fafata tun ranar 11 ga watan Satumbar 2022. Arsenal ta ci qwallo ta hannun Bukayo Saka saura minti biyar su yi hutu, sannan Gabriel Martinelli ya ƙara na biyu daf da cikar minti na 45. Kyaftin ɗin Arsenal, Martin Odegaard shine ya ƙara na biyu, saura minti 19 a tashi daga karawar daga baya Martinelli ya aara na biyu na huɗu a wasan. Wannan shine karo na 100 da Arsenal ta ci Everton a…
Read More
Fitaccen tsohon ɗan wasa Fontaine ya rasu

Fitaccen tsohon ɗan wasa Fontaine ya rasu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Just Fontaine, wanda ya kafa tarihin zura mafi yawan ƙwallo a raga a gasar kofin duniya ɗaya, ya rasu yana da shekaru 89 a duniya. Fontaine ya ci wa Faransa ƙwallaye 13 a wasanni shida kacal a gasar kofin duniya da aka yi a Sweden a shekarar 1958 inda ta zo na uku. Yana matsayi na huɗu a jerin waɗanda suka fi zura ƙwallaye a gasar kofin duniya tare da Lionel Messi na Argentina. "Za a kewar tauraron ƙwallon Faransan, fitaccen ɗan wasan gaba, fitaccen ɗan wasan Reims," in ji tsohon kulob ɗin Stade de Reims.…
Read More
Gwamnan Badaru ya miƙa wa sabon Sarkin Dutse sandar mulki

Gwamnan Badaru ya miƙa wa sabon Sarkin Dutse sandar mulki

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Abubakar Badaru, ya miƙa sandar mulki ga sabon Sarkin Dutse, Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi. Bikin miƙa sandar ya gudana ne ranar Asabar a Dandalin Aminu Kano da ke Dutse, babban birnin jihar tare da samun ɗimbin mahalarta daga ciki da wajen jihar. Badaru ya ce sabon Sarkin ya gaji mahaifinsa ne nisa alherin da ya shuka sa'ilin da yake riƙe da masarautar a halin rayuwarsa. “Muna shawartar ka da ka yi koyi kyawawan ayyukan mahaifinka da kuma tabbatar da shugabanci nagari," in ji Gwamnan. Daga nan, Badaru ya yi addu'a wa…
Read More
Ba za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa ba – Ezeife

Ba za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa ba – Ezeife

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon gwamnan jihar Anambara, Chukwuemeka Ezeife, ya ce, ba za a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasar Nijeriya ba. Ezeife ya bayyana haka ne a yayin da ya ke zargin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC da yin maguɗin zaɓe a zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya inda jam’iyyarAPC da ɗan takararta Bola Ahmed Tinubu suka marawa baya. Tsohon shugaban na Anambra ya ce, a fili yake cewa Peter Obi na jam'iyyar LP ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a faɗin ƙasar. Shugaban Hukumar INEC, Mahmood Yakubu,…
Read More