Editor

9513 Posts
Ƙidayar 2023: Hukumar NPC ta saki albashi da kuma alawus-alawus na ma’aikatantan wucin-gadi

Ƙidayar 2023: Hukumar NPC ta saki albashi da kuma alawus-alawus na ma’aikatantan wucin-gadi

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar Ƙidayar Al'ummar (NPC) ta fitar da tsarin albashi da alawus-alawus na ma'aikatanta na wucin-gadi waɗanda za su yi aikin qidayar al'umma da gidaje na shekarar bana ta 2023. Idan ba a manta ba a kwanan nan ne dai hukumar ta kammala aikinta na ɗaukar ma'aikatan wucin gadin da za su yi aikin ƙidayar, kuma sannan ta bayyana cewa, atisayen zai faru ne a tsakanin 29 ga Maris da kuma 2 ga watan Afirilu. A cewar hukumar NPC, kuɗin da za a biya ma'aikatan na wucin-gadi kala biyu ne - wato alawus da kuma albashi. A…
Read More
INEC ta tsayar da lokacin miƙa wa zaɓaɓɓun ‘yan majalisun tarayya shaidar lashe zaɓe

INEC ta tsayar da lokacin miƙa wa zaɓaɓɓun ‘yan majalisun tarayya shaidar lashe zaɓe

Daga BASHIR ISAH Ya zuwa ranakun Talata da Laraba masu zuwa ake sa ran Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga 'yan majalisun tarayya da suka kai bantensu a zaɓen da ya gudana. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka ranar Asabar da safe yayin taronsu da Kwamishinonin Zaɓe (REC) a Abuja. Yakubu ya ce 'yan majalisu 423 ne suka ci zaɓe, yayin da za a sake zaɓen 'yan majalisu a wasu mazaɓu 46. Ya ce, 'yan majalisun da suka ci zaɓen sun haɗa da sanatoci 98 cikin 109, da 'yan Majalisar Wakilai…
Read More
Gobara ta laƙume rumfunan kasuwa 80 a Kano

Gobara ta laƙume rumfunan kasuwa 80 a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta rawaito cewa, gobara ta lamushe aƙalla rumfuna 80 a kasuwar Kurmi da ke cikin ƙwaryar birnin Kano.  Wannna jawabi ya fito ne daga bakin kakakin hukumar kashe gobara a Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, a ƙarfe 5:23 ranar Larabar da ta gabata.  Abdullahi ya bayyana cewa, sun samu waya ta neman agaji daga wani wai shi  Aliyu Alkasim wanda ya gaya musu cewa gobara ta varke a kasuwar.  Ita dai kasuwar Kurmi kasuwa ce a Kano wacce ta shahara a sayar da kayan ƙamshi, turare, da fatun dabbobi.  Kakakin ya…
Read More
CNN ya ƙi ambatar Tinubu a matsayin zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa

CNN ya ƙi ambatar Tinubu a matsayin zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa

•Ya bayyana Obi a matsayin wanda ya kamata a ayyana Daga AISHA ASAS Tashar talabijin na CNN ya ƙi bayyana Bola Tinubu a tsayin wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, sai dai ya bayyana hasashen cewa, ɗan takara a Jam'iyyar LP,  Peter Obi, ne zai lashe zaɓen, abinda kawai ake jira shine, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta sanar cewa, shine zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya. Wannan ya biyo bayan sanarwar da hukumar zaɓe ta yi na tabbatar da ɗan takara a Jam'iyyar APC, Bola Ahmad  Tinubu a matsayin wanda…
Read More
Sulhu: Atiku ya fatattaki su Ganduje, ya ce da masu daraja zai zauna

Sulhu: Atiku ya fatattaki su Ganduje, ya ce da masu daraja zai zauna

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Wazirin Adamawa kuma ɗan takarar Jam’iyyar PDP a zaven 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya fatattaki tawagar neman sulhun da zaɓaɓɓen Shugaban Nijeriya mai jiran gado, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya aike masa, wacce ta ƙunshi Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan na Kebbi Atiku Bagudu, na Jihar Jigawa Badaru Abubakar da na Jihar Nasarawa Abdullahi Sule tare da tsohon Shugaban Hukumar EFCC Nuhu Ribadu. Majiya mai tushe daga jikin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ta shaida wa News Point Nigeria cewa, nan take Atikun ya ja kunnensu da kada ya sake ganin ƙeyarsu a…
Read More
Ɗan Sani Abacha, Abdullahi ya rasu a cikin barci

Ɗan Sani Abacha, Abdullahi ya rasu a cikin barci

Daga BASHIR ISAH Ɗan tsohon Shugaban Ƙasa, Marigayi Sani Abacha, Abdullahi Abacha, ya rasu yana da shekara 36. 'Yar uwar marigayin, Gumsu Sani Abacha, ita ce ta ba da sanarwar rasuwar ta shafinta na Tiwita a ranar Aasabar. Kazalika, majiya daga ahalin marigayin ta tabbatar da rasuwar Abdullahi, inda ta ce marigayin ya rasu ne a cikin barci a gidansu da ke Nelson Mandela Street, Abuja. “Lafiyarsa ƙalau a daren jiya, amma da safiyar nan sai gawarsa aka tarar," in ji majiyar. Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewar za a yi jana'izar marigayin da ƙarfe 4 na yammacin Asabar…
Read More
Canjin Kuɗi: Matakin taƙaita cire kuɗi ya saɓa wa doka – in ji Kotun Ƙoli

Canjin Kuɗi: Matakin taƙaita cire kuɗi ya saɓa wa doka – in ji Kotun Ƙoli

Daga BASHIR ISAH Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin cewar matakin taƙaita cire kuɗi da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ɗauka wanda hakan ya haifar da karancin kuɗi a ƙasa, hakan ya saɓa wa dokar 'yancin 'yan ƙasa. Kwamitin alƙalan ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a John Okoro, ne ya bayyan wannan hukuncin yayin zaman Kotun ranar Juma'a. “Irin wannan ƙayyadewar a kan 'yancin da mutum ke da shi na yin amfani da dukiyarsa yadda ya so saɓa wa doka ne, sai dai idan doka ce da kanta ta tanadi hakan," in ji ɗaya daga cikin alƙalan, Emmanuel Agim. Yayin zaman nata, Kotun…
Read More
Shugabannin duniya sun yi na’am da zaɓen Tinubu

Shugabannin duniya sun yi na’am da zaɓen Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sabon zaɓaɓɓen shugaban Tarayyar Nijeriya mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yana cigaba da samun tagomashi a duniya ta hanyar karɓar saƙon taya murna daga shugabannin ƙasashen duniya, inda kawo yanzu kusan dukkan manyan ƙasashen duniya masu faɗa-a-aji sun aiko masa da saƙonnin taya murna tare da ba shi tabbacin za su yi aiki tare da shi. Idan za a iya tunawa, a ranar Laraba, 1 ga Maris, 2023, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ta sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa…
Read More
2023: Yadda al’amuran zaɓe suka jawo tashin farashin man fetur zuwa Naira 300 kowacce lita

2023: Yadda al’amuran zaɓe suka jawo tashin farashin man fetur zuwa Naira 300 kowacce lita

AMINA YUSUF ALI Dillalan man fetur, a ranar Talatar da ta gabata sun bayyana cewa, tashoshin man fetur na Nijeriya da dama sun daina lodin man fetur a halin yanzu. Hakan ya faru ne sakamakon fargabar abinda ka- je-ya-zo a yayin tattara sakamakon babban zaɓe a faɗin ƙasar nan. Hakazalika, rahotannin sun bayyana cewa, hakan ya matuƙar jawo tsadar man fetur, inda ake sayar da man fetur a tsakanin Naira 194 zuwa 200 kowacce lita a gidajen man NNPC kaɗai, sai sauran gidajen man na 'yan kasuwa kuma ake sayar da su a kan Naira 250 zuwa 300 a kan…
Read More
Jihohi 7 sun janye ƙarar da suka shigar kan nasarar Tinubu

Jihohi 7 sun janye ƙarar da suka shigar kan nasarar Tinubu

Daga BASHIR ISAH Bakwai daga cikin jihohi takwas da suka shigar da ƙara Kotun Ƙoli suna ƙalubalantar nasarar sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, sun janye ƙarar tasu. Sun janye ƙarar ne a ranar Juma'a, tare da miƙa wa kotun sanarwar janye ci gaba da shari'ar. Jihohin da lamarin ya shafa, da suka haɗa da Adamawa, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Edo, Taraba da kuma Sakkwato sun cimma wannan matsaya ne ta tawagar lauyoyinsu ƙarƙashin jagorancin Chief Mike Ozekhome (SAN). “Kotu ta sani cewa masu ƙara sun yanke janye ƙarar da suka shigar kan wanda ke kare kansa," in ji sanarwar.…
Read More