04
Mar
Daga JAMIL GULMA a Kebbi A cikin shirye-shiryenta na tinkarar zaɓen gwamnoni mai zuwa, Jam'iyyar APC mai mulki a Kebbi ta rushe kwamitocin rumfunan zaɓe a jihar. Alhaji Isah Aslafi jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar ya bayyana wa jaridar Blueprint Manhaja da cewa wannan ya biyo bayan ganin abinda ya faru ne a zaɓen da ya gabata na Shugaban Ƙasa da 'yan majalisun tarayya wanda 'mun lura da yadda zaɓen ya bar mu da mamaki, saboda muna ganin muna da nasara amma sai akasin haka ta faru." Ya ƙara da cewa duk da yake dai sun yaba da ƙoƙarin…
