Editor

9513 Posts
Iyaye su ba wa ‘ya’yansu damar zaɓar abinda suke son zama a rayuwa – Hauwa Mustapha Babura

Iyaye su ba wa ‘ya’yansu damar zaɓar abinda suke son zama a rayuwa – Hauwa Mustapha Babura

"Shelanta sakamakon jarrabawa na ɗaya daga cikin abinda ke sa ƙiyayyar karatu ga yara" (Ci gaba daga satin da ya gabata) Daga ABUBAKAR M. TAHIR MANHAJA: A ɓangare ɗaya, al'ummar ƙasarmu Nijeriya suna da sha'awar kwaikwayo tare da ɗaukar al'adun turawa. Shin kina ganin idan hakan ya ƙara yawaita zai taimaka wurin rage matsalolin da ake fama da su a ƙasar nan? HAJIYA HAUWA: To a gaskiya wanna wani abu ne wanda yana buƙatar al'ummar ƙasarmu musamman matasa su rinqa kulawa sosai da tsarin da zasu koya a rayuwar turawa. Sau dayawa suna zavar ɗabi'un da ya yi masu daɗi…
Read More
Karamcin marubuta ya sa duniyar rubutu ta zama dangi gare ni – Aisha Sani Abdullahi

Karamcin marubuta ya sa duniyar rubutu ta zama dangi gare ni – Aisha Sani Abdullahi

"Marubuta su tabbatar hijabinsu ba kawai na zahiri ba ne har zuciyarsu su rufe" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ɗayyeesherthul-Humaerath, wani suna ne mai wuyar karantawa, amma kuma da shi aka fi sanin marubuciyar wacce matashiya ce daga Jos, da ta zama fitacciya a fagen rubuce rubucen adabi na yanar gizo. Asalin sunan ta Aisha Sani Abdullahi, ta yi rubuce rubuce da dama da suka shafi soyayya, zamantakewa, rayuwar zaman gidan miji da sauran su. Littattafanta Yel, Freeya, da suka zo da wani irin suna da salon da ba a saba da shi ba a tsakanin marubutan adabi sun ja hankali…
Read More
Zaɓen 2023: Za mu ƙalubalanci nasarar Tinubu a kotu – LP

Zaɓen 2023: Za mu ƙalubalanci nasarar Tinubu a kotu – LP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam'iyyar Labour Party (LP) mai adawa a zaɓen Shugaban Ƙasa na Nijeriya ta bayyana cewa za ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen da ya bayyana Bola Tinubu na Jam'iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya yi nasara. Yayin da yake jawabi a Abuja a ranar Laraba, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam'iyyar LP, Datti Baba Ahmed, ya jaddada cewa akwai kura-kurai a zaɓen. "Mun shiga zaɓen a matsayin LP kuma mun yi nasara da sunan LP," a cewarsa. "Kuma za mu ƙwaci haƙƙinmu da sunan LP". Tun a ranar Talata jam'iyyun adawa na PDP…
Read More
Sirrin nasarar marubutan Nijar a gasar Hikayata – Nana Aicha Hamissou

Sirrin nasarar marubutan Nijar a gasar Hikayata – Nana Aicha Hamissou

"Marubuci hantsi ne leƙa gidan kowa" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Akwai kyakyawar alaƙa da zumunci mai ƙarfi tsakanin marubutan Nijar da Nijeriya kamar yadda marubuciya Nana Aicha Hamissou Abdoulaye ta tabbatar a zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, inda ta bayyana sirrin nasarar da ake ganin marubutan Nijar na samu a shekarun baya bayan nan, musamman a gasar Hikayata ta BBC Hausa. A shekarar 2021 Nana Aicha ta zo mataki na biyu, yayin da a 2022 kuma Amira Souleymane ta samu nasara a mataki na farko. Abin arashin kuma shi ne dukkan su sun fito ne daga gari ɗaya wato Jihar…
Read More
Ku yi haƙuri game da wahalar da canjin kuɗi ya haifar, kiran Buhari ga ‘yan Nijeriya

Ku yi haƙuri game da wahalar da canjin kuɗi ya haifar, kiran Buhari ga ‘yan Nijeriya

Daga UMAR GARBA a Katsina Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ba wa al'ummar Jihar Katsina haƙuri dangane da mawuyacin halin da 'yan jihar da ma ƙasa baki ɗaya aka shiga sakamakon canjin kuɗi da Babban Bankin Ƙasa (CBN) ya yi. Buhari ya bayyana haka ne ran Laraba cikin wani jawabi da ya yi wa al'ummar jihar a gidansa da ke Daura. "Ina ƙara maku godiya da yarda da kuka yi da ni kuka zaɓe ni har sau biyu a matsayin shugaban ƙasa a jam'iyyar APC. "Ina baku haƙuri kan wahalar da aka sha ta canjin kuɗi an yi ne don…
Read More
Sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa da mataimakinsa sun ziyarci Buhari a Katsina

Sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa da mataimakinsa sun ziyarci Buhari a Katsina

Daga BASHIR ISAH Sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da mataimakinsa, Kashim Shettima, sun bi Shugaba Buhari da shaidar lashe zaɓen da INEC ta miƙa musu har Daura don tayaurna da kuma sanya musu albarka. Tinubu da Shettima sun wannan ziyarar ne bisa rakiyar Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Adamu. Sauran 'yan rakiyar sun haɗa da Gwamna Nasir El-Rufai (Kaduna), Atiku Bagudu (Kebbi), Dave Umahi (Ebonyi), Bello Matawalle (Zamfara), Abubakar Sani-Bello (Neja), Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Dapo Abiodun (Ogun), Badaru Abubakar (Jigawa) da kuma Simon Lalong (Filato). Sabon zaɓaɓɓen shugaban ya yi amfani da wannan dama wanen nuna…
Read More
Duk zaɓukan ’yan majalisar dokokin ƙasa na Sakkwato ba su kammalu ba – INEC

Duk zaɓukan ’yan majalisar dokokin ƙasa na Sakkwato ba su kammalu ba – INEC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa duk zaɓukan ’yan Majalisun Tarayya da aka gudanar a jihar Sakkwato ba su kammala ba. An samu labarin cewa akwai tashe-tashen hankula da kuma rashin kaɗa ƙuri'a da wasu kura-kurai a zaɓukan. Akwai kujerun Sanata guda uku da na majalisar wakilai 11 a jihar. An tattaro cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ke jagorantar Sanata Ibrahim Danbaba Dambuwa na jam’iyyar APC a Sanatan Sakkwato ta Kudu kafin a bayyana ta da rashin kammaluwa. A sakamakon zaɓen, Tambuwal ya samu ƙuri'u 87,850 yayin da Dambuwa ya…
Read More
Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta gayyaci zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Wakilai

Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta gayyaci zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Wakilai

Daga RABIU SANUSI a Kano Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ƙarƙashin Kwamishinan 'Yan Sanda, CP Muhammad Yakubu, ta gayyaci zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Tarayya Mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Dala, Hon Aliyu Sani Madakin Gini. Wannan bayanin na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar tare kuma da raba wa manema labarai a ranar Laraba. A cikin sanarwar kakakin rundunar 'yan sandan ya ce hukumar ta gayyaci Madakin Ginin ne bisa zargin sa da yin amfanin da bindiga yayin yaƙin neman zaɓensa da ya gudana kwanan baya. Sanarwar ta kara da cewa,…
Read More
NPC ta cafke mai yi mata sojan gona a Kano

NPC ta cafke mai yi mata sojan gona a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) reshen Jihar Kano ta nesanta kanta da bayanan dake yawo na karɓar 5000 don tabbatar da sunan wanda suka cike aikin ƙidaya na wucin-gadi a jihar. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar a jihar Kano, Hajiya Jamila Abdulkadir, wadda aka raba wa manema labarai. Sanarwar ta ce, bisa bayanan da ta samu ta sa jami'an tsaro bincikar lamarin. Kalika, sanarwa ta ce waɗannan masu karɓar kuɗin da sunan za su tabbatar ma wanda ya cike gurbin aikin wucin-gadi na ƙidaya ba su da alaƙa da su,…
Read More
Kotu ta tsare Alhassan Doguwa a kurkuku

Kotu ta tsare Alhassan Doguwa a kurkuku

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kotun Majastare a Kano ta tisa ƙeyar Shugaban Masu Rinjaya a Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, zuwa gidan yari kafin lokacin da za a ba da belinsa. Jaridar Solacebase ta rawaito cewa mai kare kansa, Alhassan Doguwa, na fuskantar tuhuma ne kan laifuka da dama da suka haɗa da kisan kai, haɗin baki, mallakar bindiga ba bisa ƙa'ida ba da tada fitina a tsakanin al'umma. Alƙalin kotun, Ibrahim Mansur Yola, shi ne ya ba da umarnin tsare Doguwa a kurkuku zuwa 7 ga Maris inda za a saurari neman belinsa.
Read More