Editor

9513 Posts
Kai ne mutumin da ya fi dacewa da mulkin Nijeriya – Buhari ya taya Tinubu murnar lashe zaɓe

Kai ne mutumin da ya fi dacewa da mulkin Nijeriya – Buhari ya taya Tinubu murnar lashe zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa murna a 2023, ɗan takarar Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce shi ne mutumin da ya fi dacewa da wannan shugabanci. Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, 1 ga Maris, 2023. Ya ce; “Ina taya mai girma Bola Ahmed Tinubu murnar nasarar da ya samu. Jama’a ne suka zaɓe shi, shi ne wanda ya fi dacewa da shugabancin. Yanzu zan…
Read More
Zan zama shugaban kowa – Tinubu ya gode wa ‘yan Nijeriya bayan ya doke Atiku da Peter Obi

Zan zama shugaban kowa – Tinubu ya gode wa ‘yan Nijeriya bayan ya doke Atiku da Peter Obi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gode wa ‘yan Nijeriya da suka ba shi jan ragamarsu, ya kuma ba su tabbacin cewa shi ne zai jagoranci kowa da kowa. Tsohon gwamnan na Legas ya yi wannan alƙawarin ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa na karrama shi biyo bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu. Tinubu, wanda shi ne ɗan takarar Jam’iyyar APC a zaɓen na ranar Asabar ya samu ƙuri’u 8,794,726 inda ya doke abokin hamayyarsa kuma ɗan…
Read More
‘Yan sanda sun yi ram da Alhassan Doduwa

‘Yan sanda sun yi ram da Alhassan Doduwa

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano 'Yan sanda sun kama Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, bisa zarginsa da hannu wajen kashe wasu mutane tare da ƙona sakatariyar jam’iyyar NNPP a yayin zaɓen da aka gudanar ranar Asabar. Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa aƙalla mutum uku ne suka mutu a lokacin da aka ƙona sakatariyar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar NNPP da ke Tudunwada a Kano. Mutane biyu ne suka ƙone ƙurmus a rikicin da ya ɓarke yayin tattara sakamakon zaɓen Majalisar Wakilai ta Doguwa/Tudunwada wanda a ƙarshe aka bayyana Doguwa ne ya lashe zaɓen. Wata majiya mai…
Read More
Tinubu ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa

Tinubu ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa

*Yau za a miƙa masa takardar shaida Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya zama sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya. Tinubu ya yaki wannan matsayi me biyo bayan zaɓaɓɓen da aka gudanar a ƙasar ran Asabar da ta gabata. Yau Laraba ake sa ran Hukumar INEC za ta miƙa wa Tinubu shaidar lashe zaɓaɓen da ya yi. Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, shi ne ha ba da sanarwar nasarar da Tinubu ya samu, tare da cewa za a miƙa masa shaidar ne da misalin ƙarfe 3 na ranar a Babban Zauren Taro…
Read More
Ba mu yarda a soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba – APC

Ba mu yarda a soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba – APC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamitim yaƙin neman zaɓe na ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam'iyya mai mulki APC, ya ce buƙatar da jam'iyyun hamayya suke gabatarwa ta soke zaɓen, ba za ta taɓa yiwuwa ba. Kwamitin ya bayyana haka ne a matsayin martani ga taron manema labarai da manyan jam'iyyun hamayya uku, PDP da LP da kuma APC suka yi inda suka ce sai dai a soke zaɓen na ranar Asabar. Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen na APC Festus Keyamo, ya ce shugaban hukumar zaɓen ta INEC zai saɓa doka idan har ya soke zaɓen da tuni ya riga ya…
Read More
Tinubu ya shigar da ƙara don hana LP, PDP dakatar da tattara sakamakon zaɓe

Tinubu ya shigar da ƙara don hana LP, PDP dakatar da tattara sakamakon zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ɗan takararta na Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, sun shigar da ƙara domin hana Jam’iyyar Labour Party (LP) da PDP yin wani abu na hana tattarawa da bayyana sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu. A ƙarar da aka shigar gaban Babbar Kotun Tarayya dake Kano mai lamba FHC/KN/CS/43/2023, an haxa da Action Alliance da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) a matsayin waɗanda ake ƙara, yayin da mataimakin shugaban Jam’iyyar APC, Kashim Shettima a matsayin mai gabatar da ƙara. Masu gabatar da ƙara…
Read More
Ba za a soke sakamakon zaɓe ba, inji Shugaban INEC

Ba za a soke sakamakon zaɓe ba, inji Shugaban INEC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta shawarci jam’iyyun siyasa da ke ƙorafi da su nemi haƙƙinsu a kotu idan ba su gamsu da yadda zaɓen ke gudana ba, inda ta ƙara da cewa kiraye-kirayen da wasu jam'iyyu ke yi kan shugaban INEC, Mahmood Yakubu ya yi murabus bai dace ba. Idan dai ba a manta ba a ranar Litinin ne wakilan jam’iyyar PDP, Dino Melaye da Emeka Ihedioha suka fice daga babban taron INEC na ƙasa da ke Abuja bisa zargin tafka maguɗi a zaɓe. Wakilan wasu jam'iyyu, ciki har da na SDP,…
Read More
Buhari ya gargaɗi Obasanjo kan yi wa  sha’anin zaɓe shisshigi

Buhari ya gargaɗi Obasanjo kan yi wa sha’anin zaɓe shisshigi

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da kada ya haifar wa zaɓen 2023 da tasgaro da wasiƙar da ya rubuta na tada zaune tsaye da son-kai da tada hankali kan zaɓe. A wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata, Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce abin da tsohon Shugaban ƙasar ya yi ba komai ba ne illa ƙoƙarin haifar da cikas ga tsarin zaɓe da kuma yin magudin zaɓe da tada hankali. Obasanjo ya ce babu nagarta a babban zaɓen ƙasar da aka yi ranar Asabar don haka ya ce…
Read More
INEC ta sanar da Shekarau a wanda ya lashe zaɓen sanatan Kano ta tsakiya

INEC ta sanar da Shekarau a wanda ya lashe zaɓen sanatan Kano ta tsakiya

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta sanar da sunan Malam Ibrahim Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Kano ta tsakiya a ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP. Baturen zaɓen Farfesa Tijjani Hassan Darma ne ya bayyana Sanata Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’a 456,787 akan babban abokin karawarsa na Jamiyyar APC Abdulkarim Abdussalam Zaura wanda ya sami ƙuri’a 168, 677, da Hajiya Laila Buhari ta jam'iyyar PDP da kuri'a 55,237, Jim kaɗan bayan kammala faɗin sakamakon wakilin jam'iyyar NNPP ya ƙalubalanci hukumar zaɓe akan kin canja sunan Shekarau wanda tuni ya koma jam'iyyar…
Read More