28
Feb
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-rufa'i ya rasa kujerun sanatoci na dukkan shiyyoyi uku da ke faɗin jihar. El-rufa'i wanda na gaba-gaba ne a Jam'iyyar APC kuma mai faɗa a ji a cikinta, ya rasa kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya wanda Muhammad Sani Dattijo na APC ke takara da abokin karawarsa na Jam'iyyar PDP, wato Lawal Adamu wanda aka fi sani da Mr LA. Dattijo dai ana ganin ɗan lele ne a gwamnatin Jihar Kaduna, domin ya riƙe manyan muƙamai a gwamnatin El-rufa'i, ciki har da Shugaban Ma'aikatan Gidan Gwamnatin jihar, da kuma Kwamishinan…
