27
Feb
Daga RABIU SANUSI Bayanai daga Jihar Zamfara na bayyana cewa ɗan tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma sanatan ɗaya daga shiyyoyin jihar, Ahmad Sani Muhammad Yariman Bakura, ya lashe zaɓen kujerar Majalisar Tarayya ƙarƙashin mazaɓun Bakura da Maradun. Hon Ahmad Sani Muhammad Bakura ya samu wannan nasarar ne da ƙuri'a 55,273 inda ya doke abokin takarar sa Muhammad Bakura Ahmed wanda ya samu kimanin ƙuri'a 17,559 Sakamakon Wanda baturen zaɓe na mazaɓar, wato Dr. Ahmad Kainuwa na Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau ya bayyana a hedikwatar tattara sakamakon zaben dake Maradun. Ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC…
