27
Feb
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashe dukkan ƙananan hukumomi 11 na jihar Gombe. A sakamakon zaɓen da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana a safiyar ranar Litinin, jami’ar da ke kula da zaɓen, Farfesa Maimuna Waziri, mataimakiyar shugabar jami’ar tarayya ta Gashua, ta ce Atiku ya samu ƙuri’u 319,123 kan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya samu ƙuri’u 146,977. A sakamakon da aka bayyana daga ƙaramar hukumar Shongom, Atiku Abubakar ya samu ƙuri'u 13,520 yayin da APC ta samu 7,525; Peter…
