27
Feb
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta bayyana Ahmed Wadada na Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a matsayin wanda ya lashe zaven mazaɓar Nasarawa ta Yamma. Mataimakin Farfesa Nasirudeen Baba, jami’in zaɓe na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC a mazabar Nasarawa ta Yamma ne ya bayyana hakan bayan kammala tattara sakamakon zaɓen a ranar Litinin a cibiyar tattara sakamakon zaɓe na shiyya da ke ƙaramar hukumar Keffi a jihar. Ya bayyana cewa bayan zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar, Wadada ya samu ƙuri’u 96,488 yayin da ɗan takarar Jam’iyyar…
