26
Feb
Daga UMAR GARBA a Katsina Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya samu nasarar lashe zaɓen ƙananan hukumomi 6 daga cikin 8 da aka tattara kawo yanzu Babban jami'in tattara sakamakon zaɓe a jihar farfesa Mu'azu Abubakar Gusau ne ya sanar da hakan yau lahadi Ƙananan hukumomin da ɗan takarar jam'iyyar APC ɗin ya lashe sun haɗa da Matazu, Kaita, Musawa, Ingawa, Charachi da kuma Dutsi sai dai jam'iyyar PDP ce ta lashe zaɓen ƙaramar hukumar Batsari da kuma Kurfi A babban zaɓen da aka gudanar ranar Asabar. Tinubu ya samu ƙuri’a 82,332 a faɗin…
