Editor

9513 Posts
Zaɓen 2023: An kai wa ma’aikatan EFCC hari a Abuja da Imo

Zaɓen 2023: An kai wa ma’aikatan EFCC hari a Abuja da Imo

Daga AISHA ASAS Wasu tsageru sun kai wa wasu ma'aikatan hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC, waɗanda ke aikin saka ido a zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisu, hari a kusa da fadar hakimin Bwari da ke birnin tarayya. Lamarin ya biyo bayan kame da aka yi na wanda ake zargi da ƙwarewa wurin siyen ƙuri'un zaɓe a mazaɓar da ke Science Primary School, Bwari. Ma'aikatan na EFCC sun yi nasarar damƙe wanda ake zargi, mai kimanin shekaru 30, kuma a tare da shi akwai jerin sunayen waɗanda aka riga aka…
Read More
Sakamakon Zaɓe: Kwankwaso ya lashe ƙananan hukumomi 9 a Kano

Sakamakon Zaɓe: Kwankwaso ya lashe ƙananan hukumomi 9 a Kano

Daga IBRAHIM Hamisu, a Kano Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam'iyyar NNPP, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ya lashe ƙanan hukumomi 9, da suka haɗa da Garin Malam, Kibiya, Rimin Gado, Kura, Gazawa, Minjibir, Gabasawa, Warawa. Ga sakamakon zaɓen kamar yadda INEC ta bayyana: Garun Malam Jimillar Ƙuri'u: 74,846 Waɗanda aka tantance: 26,692 APC – 8,642LP – 169NNPP – 12,249PDP – 4,409 Rimin Gado: Adadin masu zaɓen da aka yi wa rajista: 67,128 Waɗanda aka tantance: 27,476 APC – 10,861LP – 76NNPP – 14,634PDP – 907 Kibiya: Adadin masu zaɓen da aka yi wa rajista: 77,929Waɗanda aka tantance: 28,228 APC –…
Read More
Zaɓen 2023: Abinda ya sa na kaɗa wa Tinubu ƙuri’a a filin Allah – Buhari

Zaɓen 2023: Abinda ya sa na kaɗa wa Tinubu ƙuri’a a filin Allah – Buhari

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilinsa na kaɗa wa Asiwaju TInubu ɗan takarar shugaban ƙasa a jamiyyar APC ƙuri'a a bainan nasi a yayin da yake zaɓe a mahaifarsa wato Daura. Shugaban ya bayyana cewa, ba wani abu ne ya sa ya bayyana zaɓinsa ga Tinubun ba illa nuna biyayyarsa da goyon bayansa gare shi. A cewar sa, bayan ya kewaye lungu da saƙo na ƙasar nan don yin yaƙin neman zaɓe ga tsohon gwamnan na Legas, ya kamata ya cika aikinsa na jaddada goyon baya a gare shi a matsayin wanda ya fi so…
Read More
Tinubu ya lashe akwatin zaɓen el-Rufai a Kaduna

Tinubu ya lashe akwatin zaɓen el-Rufai a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi nasara a rumfar zaɓen gwamna Nasir el-Rufai na Jihar Kaduna. Tinubu ya samu ƙuri’u 173 a rumfar zaɓe mai lamba 024, Ward 07, Ungwan Sarki, Kaduna, inda ya doke ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya samu ƙuri’u 134. Peter Obi na jam'iyyar Labour Party LP ya samu ƙuri'u uku, yayin da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP ya samu ƙuri'u 20.
Read More
Gwamnan Gombe ya gaza kawo wa Tinubu akwatin zaɓensa

Gwamnan Gombe ya gaza kawo wa Tinubu akwatin zaɓensa

Daga Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya kasa kawo wa Tinubu akwatinsa zaɓensa, inda ya sha kaye a hannun jam'iyyar PDP. A sakamakon zaɓen da aka sanar da jama'a da dama, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya samu ƙuri'u 215 inda ya doke ɗan takarar jam'iyyar APC, wanda ya samu ƙuri'u 186 a jam'iyyar. Da yake bayyana sakamakon zaɓen, jami’in zaɓe (PO) na mazaɓar Yahaya Umar 010 da ke makarantar gwamnati ta Gombe, Misheal Thomas ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta samu ƙuri’u 10 ne kacal yayin da LP ta samu…
Read More
An cinna wa ofishin INEC na Takai wuta a Kano

An cinna wa ofishin INEC na Takai wuta a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar 'yan sanda a Jihar Kano ta tabbatar da cewa an cinna wa ofishin Hukumar Zaɓe na Nijeriya reshen Ƙaramar Hukumar Takai wuta. Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna kiyawa ne ya tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin. 'Yan banga ne suka cinna wa janareton da ake aiki da shi a cibiyar wuta, lokacin da suka shiga wajen ta baya, amma ba wani ci ta yi ba, kuma an kashe ta, tuni muka ƙara yawan jami'anmu a wajen,' inji Kiyawa. Manhaja ta tuntuɓi wani ganau wanda ya ce an cinna wutar kuma ta ƙona…
Read More
Wata mata ta fashe da kuka bayan dangwala wa Tinubu ƙuri’a bisa kuskure

Wata mata ta fashe da kuka bayan dangwala wa Tinubu ƙuri’a bisa kuskure

Daga AISHA ASAS An hango wata mata a mazaɓa mai lamba 047 da ke unguwar Kubwa, a rumfar makarantar firamare da ke cikin birnin tarayya Abuja, tana tana rusar kuka, sakamakon abinda ta kira da tsautsayi da ya afka mata ta hanyar jefa ƙuri'arta ba a inda ta yi niyya ba. Kamar yadda ta faɗa, ta dangwala wa Asiwaju Bola Tinubu, amma fa bisa ga kuskure, domin ba shi ne ta yi niyyar zaɓa ba. Iya ƙoƙari an yi na samun ƙarin bayani daga bakin wannan baiwar Allah kan yadda lamarin ya faru tare kuma da sanin dalilin faruwar wannan…
Read More
INEC ta ƙaddamar da zauren tattara sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa

INEC ta ƙaddamar da zauren tattara sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Hukumar Zaɓe na Ƙasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ayyana buɗe zauren karɓar sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa na 2023 a hukumance. Shugaban na INEC ya ce za a fara tattara sakamakon ne daga gundumomi zuwa ƙananan hukumomi, daga nan sai a kai matakin jiha. Ya ce bayan nan ne kuma za a kai sakamakon zuwa Abuja, babban birnin tarayya, a zauren tattara sakamakon. Yakubu ya ce baturen zaɓe idan ya zo sanar da sakamakon zaven jihar da ya zo da ita, zai faɗi ta yadda kowa zai ji, inda zai faɗi yawan mutanen…
Read More
Tinubu ya lallasa Obi a rumfar zaɓen Obasanjo

Tinubu ya lallasa Obi a rumfar zaɓen Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam'iyyar Labour, Peter Obi ya sha kaye a rumfar zaɓe ta tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisun tarayya na 2023. Ku tuna cewa tsohon shugaban ƙasar ya goyi bayan Obi ne a matsayin ɗan takarar da ya fi so gabanin zaɓen Shugaban Ƙasa. Jim kaɗan bayan ƙidaya sahihan ƙuri’u a mazaɓar Obasanjo da ke gunduma 11, Unit 22, a Ƙaramar Hukumar Abeokuta ta Arewa a Jihar Ogun, ɗan takarar Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, da ƙuri’u 56 ya kayar…
Read More