Karamcin marubuta ya sa duniyar rubutu ta zama dangi gare ni – Aisha Sani Abdullahi

“Marubuta su tabbatar hijabinsu ba kawai na zahiri ba ne har zuciyarsu su rufe”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ɗayyeesherthul-Humaerath, wani suna ne mai wuyar karantawa, amma kuma da shi aka fi sanin marubuciyar wacce matashiya ce daga Jos, da ta zama fitacciya a fagen rubuce rubucen adabi na yanar gizo. Asalin sunan ta Aisha Sani Abdullahi, ta yi rubuce rubuce da dama da suka shafi soyayya, zamantakewa, rayuwar zaman gidan miji da sauran su. Littattafanta Yel, Freeya, da suka zo da wani irin suna da salon da ba a saba da shi ba a tsakanin marubutan adabi sun ja hankali sosai, babu ma kamar wani littafi da ta rubuta mai taken ‘Sai Na Auri Marubuci’ wanda ta fara rubuta shi kamar da wasa, amma daga bisani ya jawo surutai da qananan maganganu a tsakanin marubuta da masu karatu. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana yadda ta zubar da hawaye a dalilin rubutun littafi da ƙoƙarin ta na kawo sabon sauyi a rubutun adabin Hausa. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Ina son ki fara gabatar da kanki ga masu karatu?

AISHA: Sunana Aisha Sani Abdullahi wacce a duniyar rubutu aka fi sani na da Ɗayyeesherthul-Humaerath. Ni haifaffiyar garin Jos ce a Jihar Filato, kuma a nan nake rayuwa tare da iyayena, duk da yake mu asalin mu daga Jihar Kano ne a Ƙaramar Hukumar Gaya. Ni budurwa ce har yanzu, ban yi aure ba. Har wa yau kuma ni ce na kafa kuma nake jagorantar ƙungiyar marubuta ta Noble Writers Association. Ni ɗaliba ce, kuma ýar kasuwa a zaurukan sada zumunta.

Menene tarihin rayuwarki a taƙaice?

Rayuwata ta ƙunshi abubuwa na ban mamaki mai ɗauke da al’ajabi da kuma nasarori wanda bani da abin cewa illa Alhmdulillah. Ina godewa Allah kuma ina godewa iyayena da suka jajirce wajen ganin rayuwata ta inganta.

Da farko dai kamar yadda na faɗa a baya, ni haifaffiyar garin Jos ce. Na yi karatuna na firamare a Maria Memorial Private School, sannan a anan ne kuma na yi sakandire ɓangare Maria Memorial College. Daga nan kuma na fara karatu a wani sashi na makarantar da ke koyar da aikin jinya, wato School of Health Technology. A halin yanzu ina ƙoƙarin rubuta karrabawar neman shiga jami’a ta JAMB, domin samun damar shiga Jami’ar Jos, inda nake so na yi karatu a ɓangaren ba da shawara na Guidance And Counseling.

Tun yaushe ki ka fara rubutun labaran hikayoyi na adabi?

Zan iya tunawa tun a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017 lokacin ina makarantar sakandire. Tun tasowa ta na kasance ina da son rubuce rubuce, sai dai abin mamaki karatu yana ba ni wahala. Ba na mantawa lokacin ina aji ɗaya na qaramar sakandire na sha ƙin kashe kuɗin hutuna wato break don kawai in sayi littafin rubutu ni da wata ƙawata, da sunan wai zamu rubuta littafi.

Ga shi a lokacin babu isasshiyar Hausar a baki ma bare a rubuce, saboda yanayin muhallin da muka tashi. Amma a haka dai muka yi ta fama, don ganin mun zama marubuta, har dai muka haƙura. Sai muna ajin ƙarshe na sakandire ne kwatsam malamin mu mai koyar da harshen Hausa ya sa mu dole sai mun rubuta gajeren labari a matsayin wani gwaji shirin jarrabawar mu ba.

A farko mun ɗauki abin a matsayin wasa sai da muka ga babu sarki sai Allah, tilas muka dage da rubutun aikin da aka sa mu. Dukkanmu sai da muka rubuta littafi, wanda ni na sa wa nawa sunan ‘So Sarki Ne’, wanda zan iya cewa shi ne littafina na farko. Duk da cewa ina ganin ai wannan tursasani aka yi. Amma kuma shi ne ya kasance mabuɗin cigaba da harkokin rubuce rubucena.

Tun daga sannan ne kuma na mayar da himma kan rubutu amma kuma na fi sha’awar rubutun wasan kwaikwayo. A lokacin ina da wata ƙawa ita kuma ta fi ƙarfi wajen rubuta labaran hikaya. Ita ce ta nuna min cewa ai yadda ake rubuta wasan kwaikwayo haka ake tsara labari. Ina cewa ba zan iya ba tana cewa zan iya.

Daga lokacin dai na fara bin littafin da take rubutawa ina karantawa, domin ni da kawai so nake in yi rubutu kawai ba tare da na karanta na ji ya ma ake ba. Daga karanta nata sai na ɗan fara bin wasu littafan, kamar wasa kuwa na fara nima littafina mai suna ‘Babu Ruwan So’.

Wanne ƙalubale ki ka fara fuskanta a farkon lokacin da ki ka fara ƙoƙarin zama marubuciya?

Gaskiya tun da na fara rubutu ba na jin cewa akwai wata matsala da na tava fuskanta, ko da akwai ma ina ganin bai wuce wahalar rubutu ba ko typing.

Littattafai nawa ki ka rubuta kawo yanzu?

Ban da gajerun labarai na rubuta littattafai sun kai 15, sun haɗa da Babu ‘Ruwan So’, ‘Azzawajul-Muƙaddar’, ‘Wasa Da So’, ‘Jameel’, ‘Ameenatou ‘Yar Kaka’, ‘Ashe Haka So Yake? ‘Matar Police’, ‘Kuchakar Kishiya’, ‘Dr. Yusuf’, ‘Sai Na Auri Marubuci’, ‘Kalaman Soyayya 20’, ‘Hayati’, ‘Yel’, ‘Freeya’, sai kuma wanda nake kai yanzu, ‘Boɗɗiya’.

Akwai waɗanda ki ka buga a littafi ne ko dai duka a online ki ke fitar da su?

Na buga littafina ɗaya ‘Sai Na Auri Marubuci’ kuma ina da shirin buga wasu ma nan gaba kaɗan da yardar Allah.

Yaya ki ke samun hikimar yin rubutun da ki ke yi, kuma waɗanne darussa ki ka fi mayar da hankali a kai?

Na kan yi tunani kan abin da al’umma take buqata ne kawai sai in yi rubutu a kai. Darusan da nake mayar da hankali kai gaskiya suna da yawa, domin ina tava ɓangarori da dama musamman abin da ya shafi cin zarafin ɗan Adam, mace ko namiji, sannan ina yawan sako barkwanci cikin rubutuna, tare da bayyanar da cewa kowanne ɗan Adam tara yake bai cika goma ba. A bayyane yake jaruman littafina duk rintsi sai na nemo masu wani naƙasu ko rauni da suke da shi domin tabbatar da rayuwar zahiri.

Wasu littattafanki suna ɗauke da sunayen da ba kasafai ake jin su ba, irin su Freeya, Yel da sauran su, a ina ki ke samo irin waɗannan sunaye ne?

Ina so rubutuna ya bambanta da na kowa ba ma iya sunayen ba, hatta cikin labaran a kullum burina na yi abin da ba kowa yake yi ba, hakan ya sa nake rubutu da harsuna daban daban. Na kan sa Turanci, Faransanci har Larabci ma in ta kama daidai gwargwado.

Na kan fara bincike a Google sannan in zo in bi mutanen da na san sun iya harshen da nake so in tavo, don abin da za a rubuta ya zama mai inganci. Kuma a nan nake samo sunayen da nake sa wa wasu littattafai na.

Wanne littafin ne za ki ce ya fi baki wahalar sarrafa rubutun sa, kuma wanne ya fi karɓuwa a wajen jama’a?

‘Yel’, duk cikin littattafaina ya fi bani wahala sosai ba kaɗan ba, don har ciwon kai na sha yi wani lokacin na kan ji na fita a hayyacina, kasancewar sa mai dogon zango. A hakan ma tsarin rubutun daban ne ba kamar sauran littattafai na ba, don har yanzu ban kammala shi ba, saboda kashi huɗu ne kuma biyu na yi, ‘Yel’ da ‘Freeya’, cikin shekarar da ta gabata 2022. Yanzu kuma in sha Allahu sauran biyun zan ƙarasa su ne Vixen da Centure kuma ina kammala su zan buga domin kasancewar su na musamman. Na tabbata babu makarancin da zai karanta su ba tare da ya ƙaru ba komai ƙanƙantar saƙon da ke ciki.

Me ya sa ki ke su sunan littattafan cikin wani harshe da ba Hausa ba, alhalin labarin na Hausa ne?

E, to. Wannan zan iya cewa zamani ne ya zo da hakan, kuma na taɓa tambaya aka ce da ni ba laifi ba ne sanya turanci a rubutun Hausa, amman ban san matsayin amfani da wasu harsunan cikin rubutun adabi ba.

Wanne littafin ne a cikin littattafanki za ki iya cewa ya fi samun karɓuwa a wajen masu karatu, wanda ki ke ɗaukarsa Bakandamiyar ki?

Gaskiya yawanci littattafaina suna karɓuwa, ba zan iya cire ɗaya ciki ba. Sai dai zan iya fitar da littafin ‘Kucakar Kishiya’, kasancewar sa littafina na biyu a duniyar rubutu kuma wanda aka yi rububi neman sa fiye da zatona.

Ba mu labarin sabon littafin da ki ke kan rubutawa na ‘Boɗɗiya’, wanne darasi masu karatu za su amfana da shi?

Masha Allah, wato shi littafin ‘Boɗɗiya’ labari ne akan wata ƙaramar yarinya ne ‘yar shekara goma da ta ke fuskantar tsangwama a ƙasar su kasancewarta baqar fata, har ta kai ga mijin mahaifiyarta ya yi mata fyaɗe saboda son zuciya irin tasa. Ƙasar da suke ciki sam basa darajanta rayuwar ‘ya mace ballantana su mutuntata, ga jahilci da ƙarancin ilimin addini. A ƙarshe an jefar da wannan yarinyar inda wani matashin saurayi ya tsinceta duk da ba sa fahimtar harshen juna, kasancewar su ƙabilu daban daban.

Darasin dake cikin littafin na da yawa gaskiya, amma kaɗan daga ciki sun haɗa da illar cin zarafin ýaýa mata da muzgunawar da wasu baƙaƙen fata ke fuskanta, saboda wariyar launin fata. Sannan kuma da illar rashin ilimin addini wanda har yanzu ake samu a wasu sassan duniya. Na kuma yi ƙoƙari in bayyana mahimmanci taimakon raunana, da yadda raunin ‘ya mace ya kan koma ƙarfinta.

Wanne alheri ko cigaba za ki ce kin samu ta dalilin rubutun da littafi?

Alheri da cigaba ai ba a ma magana, domin na haɗu da mutane da dama sun zame min tamkar ýan’uwan jini. Na yi nasarar cin gasar marubuta ta Gajeren Labari daban daban, kuma na ƙaru da abubuwa da dama kan rubutu da ma rayuwa gabaɗaya. Na ci gasar Jarumai Writers wacce suka yi na cika shekaru biyu da kafuwar ƙungiyar, in da na zo ta biyu a shekarar 2022, sannan a gasar da Alan Waƙa ya sa na sarautar Ɗiyan Gobir ma na shiga sahun mutane goman da aka tantance na zo ta 6 shi ma a 2022.

Kina daga cikin fitattun marubuta labaran adabin Hausa a Jos, yaya za ki bayyana cigaban rubuce rubuce a tsakanin Jasawa?

Alhmdulillah, a farkon fara rubutuna na yi zaton kamar ni kaɗai ce marubuciyar Hausa a Jos, amma a hankali na riƙa fahimtar ashe akwai wasu marubutan da dama, musamman bayan kafa ƙungiyar haɗin kan marubutan Jos, ta Jos Writers Club. Na haɗu da tsofaffin marubuta da suka zama tamkar iyaye a wajena, irin su Hafsat Sodangi, Zuwaira Dauda Kolo, Zuwaira Isa, Abba Abubakar Yakubu da sauran matasan marubuta da suka haɗa da Rahama Nalele, Badawiyya Ahmad Mu’azu, Asma’u Abubakar Musa (Jasmine), Badi’at Ibrahim da wasu da dama, da suka haɗa maza da mata. Babban burina shi ne a samu haɗin kai a tsakanin marubutan adabi na Jos, kuma mu yi ayyuka tare har a san da zaman mu a Jihar Filato da ma Nijeriya bakiɗaya.

Yaya alaƙar ki da sauran marubuta na Kano da sauran jihohin Arewa?

Gaskiya ina da kyakkyawar alaƙa da marubutan Kano da ma na sauran sassan Arewa, don kuwa wasun su da yawa sun zame min tamkar ýan’uwa na jini da nake jinsu a jinin jikina. Karamcin marubuta ya sa yanzu a duniyar rubutu zan iya cewa ina da dangi guda wanda ko da ɗaga murya na yi a duniya za su yi saurin tambayata matsalata, ba tare da sun bari hawaye na ya zuba a kasa ba.

Kina da wata ƙungiya ne ta marubuta, kuma yaya ku ke gudanar da harkokin ƙungiyar?

E, ina da ƙungiya wacce ni ce na kafa ta wato Noble Writers Association, kuma muna aiwatar da harkokinmu cikin tsafta da nagarta tare da jan juna a jiki cike da girmamawa.

Wanne abu ne ya faru da ke ta dalilin rubutu da ba za ki tava mantawa ba?

E, to! Rayuwa ba a raba ta da ƙalubale ko akasin haka. Abubuwa da dama sun faru, sai dai na fi riƙe wani abu da ya faru a lokacin da na ke rubuta littafin ‘Sai na Auri Marubuci’. Abin mamaki daga marubuta har makaranta idanunsu sun rufe kawai hasashe ɗaya suke yi, inda suka riƙa ayyana cewa duk abin da na rubuta da ni ya faru a gaske. Wasu kuma suna zargin cewa da gaske ina son wanda na yi rubutun don shi ne. Haka dai aka riqa ƙananan maganganu iri iri. Har ya kasance a lokacin da nake rubuta wani ɓangare na littafin sai da na zubar da hawaye, ina kuka hawaye na zuba ina gogewa.

Ko za ki yi mana ƙarin bayani kan wannan marubuci, da ki ka rubuta littafi sukutum a kansa, da dalilin dambarwar da ta biyo baya?

Wato kamar yadda sunan littafin ya nuna, na rubuta shi ne kan wani babban marubuci wanda nake matuƙar girmamawa, kuma nake ɗaukar sa a matsayin yayana, wato Jameel Nafseen. Yadda abin ya samo asali kuwa shi ne, wata rana ana hira a cikin guruf din marubuta na manhajar WhatsApp ana raha da juna, sai a cikin wasa ya ce shi ma yana so ya zama Mijin Nobel, kasancewar a lokacin an turo wani bangon littafi da aka sa hoton wani kyakkyawan matashi ɗan Ƙasar Indiya, a lokacin sai na ce, ‘Yayana zan mayar da kai Mijin Nobel kuwa.’ Wannan shi ne dalilin rubuta littafin da na sa masa sunan ‘Sai Na Auri Marubuci,’ wanda fitar sa ta kawo shakku sosai a zukatan mutane da dama.

A matsayin ki ta matashiya ba za ki rasa masoya ba, musamman samari, kin taɓa yin soyayya da wani marubuci ko masoyin littattafanki?

Ban taɓa yi ba, kuma ba na fatan hakan ya kasance da rayuwata.

Wacce faɗakarwa ko jan hankali za ki yi ga matasan marubuta?

Su ji tsoron Allah, su tuna duk abin da za su rubuta Allah na ji kuma yana gani. Su tabbatar da cewa hijabinsu ba na zahiri ba ne hatta cikin zuciyarsu ma sun rufeta da murfi mai inganci.

Menene ra’ayinki game da yunƙurin da gungun wasu marubuta ke yi na yaƙi da marubutan batsa?

Ina bayan wannan yunƙurin ɗari bisa ɗari, da ni ma za a yi wannan tafiyar in sha Allah, domin ceto alƙalumanmu, rayuwarmu, da tarbiyyar sauran ýan’uwa musulmai musamman ƙananmu masu tasowa. Babu shakka rubutun batsa ba ƙaramin naƙasu ba ne ga rayuwar al’ummar musulmi gabaɗaya, ba ma bahaushe kaɗai ba. Zan so a ce an samu mafita sahihiya domin ganin an daƙile wannan alfashar cikin al’umma, kuma ina sa rai da ganin hakan nan ba da daɗe wa ba, In Sha Allah.

Marubuta da dama yanzu sun karkata wajen fitar da littattafan su ana karantawa a YouTube? Ko ke ma kina daga cikin su, kuma wacce riba ake samu da yin hakan?

E, to! Ni ma dai akwai masu sayen littattafaina suna ɗorawa a YouTube. Kuma a ganina hakan cigaba ne da zamani ya zo da shi, har wa yau kuma yana tallafa wa waɗanda ba sa iya karatu sai dai saurare.

Menene burinki nan gaba a harkar rubutun adabi?

Burina bai wuce in ga na zarce yadda nake a yanzu a fagen rubutu, kuma alƙalamina da muryata su zama abin sauraro a duniya gabaɗaya.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwar ki?

Alƙalami ya fi takobi!

Na gode.

Ni ce da godiya.