Editor

9513 Posts
Ɗan sanda ya bindige mutum don ya ce APC za ta lashe zaɓen gwamna a Filato

Ɗan sanda ya bindige mutum don ya ce APC za ta lashe zaɓen gwamna a Filato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani jami’in ɗan sanda ya harbe wani mutum mai suna Nyommena Salah Badapba a lokacin da suke taƙaddamar siyasa a unguwar Tudun Wada da ke garin Jos a Jihar Filato. Ɗan sandan, Solomon Damak, ya harbe Badapba ne a lokacin da suke muhawara kan wanda zai fito a matsayin wanda zai lashe zaɓen gwamna da za a yi ranar 11 ga watan Maris. An tattaro cewa, jami’in ya ce jam’iyyar APC ba za ta ci zaɓe mai zuwa ba, amma Badapba ya ƙi amincewa da shi. Ɗan sandan ya fusata da hakan, sai ya harbi Badapba…
Read More
Kotu ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin ɗan takarar gwamna na PDP a Zamfara

Kotu ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin ɗan takarar gwamna na PDP a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau. Kotun Ƙolin ta tabbatar da Dr. Dauda Lawal Dare a matsayin zaɓaɓɓen ɗan takarar Gwamna ƙarƙashin Jamiyyar PDP a zaɓen da za a gudanar ranar Asabar Mai zuwa. Wannan na zuwa ne kwanaki huɗu kafin zaɓen gwamnanoni da na 'yan majalisun jiha da za a gudanar a ranar 11 ga watan Maris da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta shirya a jihohi 36 na ƙasar nan. Kotun Ɗaukaka Ƙara reshen Sokoto ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a ranar 6 ga watan Janairun 2023 inda ta soke zaɓen fidda gwani…
Read More
INEC ta garzaya kotu kan sake fasalin na’urar BVAS

INEC ta garzaya kotu kan sake fasalin na’urar BVAS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ce za ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ba ta damar sake fasalin tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS) a gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi da za a yi ranar 11 ga Maris, 2023. Wani babban jami’in hukumar da bai so a ambaci sunansa ya shaida wa Aminiya irin ci gaban da aka samu a ƙarshen mako a Abuja. Majiyar ta yi nuni da cewa wannan umarni na da matuƙar muhimmanci biyo bayan umarnin da aka ba shi na hana…
Read More
BIDIYO: Atiku da wasu jiga-jigan PDP sun jagoranci zanga-zanga zuwa ofishin INEC

BIDIYO: Atiku da wasu jiga-jigan PDP sun jagoranci zanga-zanga zuwa ofishin INEC

Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, tare da abokin takarsa, Ifeanyi Okowa sun jagoranci zanga-zangar lumana zuwa babban ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a Abuja. Daga cikin waɗanda aka hango su a dandazon masu zanga-zangar, har da shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, Abiye Sekibo, Dino Melaye da kuma Uche Secondus. Zanga-zangar ɓangare ne na ci gaba da nuna rashin yarda da sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisun tarayya da ya guda asabar ta makon jiya, inda mambobin jam'iyyar suke zargin ba a yi adalci ba. Zanga-zangar wadda aka faro ta…
Read More
Elon Musk ya sake ƙwato kambunsa na mutumin da ya fi kowa arziki a duniya

Elon Musk ya sake ƙwato kambunsa na mutumin da ya fi kowa arziki a duniya

Daga AMINA YUSUF ALI Elon Musk ya sake dawowa matsayinsa na mutumin da ya fi kowa arziki a Duniya bayan ya tara maƙudan kuɗaɗe har Dalar Amurka biliyan $6.98 a cinikin awoyi takwas kacal. Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne dai attajiri Musk ya rasa muƙamin nasa na mai arzikin duniya bayan da wani Bafaranshen attajiri mai suna Bernard Arnault ya yi masa ƙafar baya tare da ture shi, kuma ya haye ƙaragarsa ta mutumin da ya fi kowa kuɗi a duniya, a ranar 8 ga watan Disambar, 2022. Al'amarin da ya jawo Musk ya rasa wancan…
Read More
Muhimmancin sada zumunci

Muhimmancin sada zumunci

Assalamu alaikum. Da farko dai, sada zumunci shi ne kyautatawa da jinƙai da bibiyar ’yan uwa (ma’abuta zumunci), ta hanyar sadar da dukan alheri gare su, da kawar da dukan sharri daga gare su gwargwadon iko. Ziyartarsu da amsa kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu’ar alheri, duk ɓangare ne na sada zumunci. Har ila yau, ma’anar zumunci na game yin sallama ga ɗan uwa yayin haɗuwa da gaishe shi da ce masa Yarhamukallahu idan ya yi atishawa ya ce alhamdulillahi. Sannan zuwa duba…
Read More
Dalilin bayyanar layukan abubuwan hawa a gidajen mai – NNPCL

Dalilin bayyanar layukan abubuwan hawa a gidajen mai – NNPCL

Daga BASHIR ISAH Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), ya alaƙanta layukan abubuwan hawa a gidajen mai da ake gani a Abuja da wasu sassan ƙasar da hana harkokin kasuwanci da zirga-zirga a lokacin zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisun tarayya da ya gudana ran 25 ga Fabrairu. Hukumar NNPCL ta ce, defo da manyan motocin ɗaukar mai sun ci gaba da aikin rarraba mai zuwa sassa daban-daban na ƙasar nan don daidaita lamurra. Cikin wata sanarwa da ya fitar, Kakin NNPCL, Garba Deen Muhammad, ya ce bayanan baya-baya sun nuna kamfanin na da mai a tanade da ya…
Read More
Mahaifiyar Sheikh Ahmad Gumi ta rasu

Mahaifiyar Sheikh Ahmad Gumi ta rasu

Daga BASHIR ISAH Fitaccen malamin Islaman nan da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ba da sanarwar rasuwar mahaifiyarsa da yammacin ranar Lahadi. Blueprint Manhaja ta kalato cewar marigayiyar ta rasu ne da misalin ƙarfe 5.30 na yamma inda aka yi jana'izarta a maƙabartar Unguwar Sarki da ke jihar. A saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, malamin ya ce, “Inna lillahi Wa Inna Ilaihil Raji’un. Da zuciya mai cike da alhini, a yau nake sanar da rasuwar mahaifiyata da misalin ƙarfe 5:30 na yamma. ”Ku yi mata addu'ar samun gafara da rahamar Allah. “Kalamanta na ƙarshe gare ni…
Read More
Yaya muka ga babban zaɓen 2023?

Yaya muka ga babban zaɓen 2023?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Har kullum a kan zuga tsarin dimokraɗiyya da cewa ita ce mafi ingancin hanya ta kawo cigaban ƙasa ta hanyar mutane su zavi wanda su ke so ya jagoarnce su a dukkan matakai. Ba kamar mulkin soja da wasu masu bindiga za su bi dare ko rana ma su ture gwamnati har ma wani lokacin ya kan kai ga zubar da jini ko wulakanta waɗanda su ke kan madafun iko a tsakanin fararen hula. Soja kan yi amfani da bindiga ya harba don ya tsoritar da farar hula ya kwace mulki da ƙarfin tuwo. Aa na…
Read More
Liverpool ta yi wa Manchester united wankan jego

Liverpool ta yi wa Manchester united wankan jego

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta yi wa Manchester United aiki mai sauƙi inda ta lallasa ta da ci 7 rigis a wasan Gasar Premier a yammacin Lahadi. Tauraron ɗan ƙwallon Netherlands Cody Gakpo, Mohamed Salah, da Darwin Nunez sun nuna bajinta matuƙa a filin wasa na Anfield, inda suka zura ƙwallaye biyu kowannensu a ragar abokan hamayyarsu ta Manchester. Tawagar ta Jurgen Klopp dai sun kafa sabon tarihin nasara a fafatawar da aka yi tsakanin ƙungiyoyin biyu da suka fi samun nasara a gasar Ingila. Kawo yanzu dai Mohamed Salah ya zama kan gaba…
Read More