Mahaifiyar Sheikh Ahmad Gumi ta rasu

Daga BASHIR ISAH

Fitaccen malamin Islaman nan da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ba da sanarwar rasuwar mahaifiyarsa da yammacin ranar Lahadi.

Blueprint Manhaja ta kalato cewar marigayiyar ta rasu ne da misalin ƙarfe 5.30 na yamma inda aka yi jana’izarta a maƙabartar Unguwar Sarki da ke jihar.

A saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, malamin ya ce, “Inna lillahi Wa Inna Ilaihil Raji’un. Da zuciya mai cike da alhini, a yau nake sanar da rasuwar mahaifiyata da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.

”Ku yi mata addu’ar samun gafara da rahamar Allah.

“Kalamanta na ƙarshe gare ni makonni biyu da suka shuɗe: “lnsha Allah, Allah zai sanya ni tare da ‘ya’yana da jikokina a Aljannah”.

”Waɗannan kalmomi sun shige ni sosai. Allah Ya yi mata rahama. Amin.”