Assalamu alaikum. Da farko dai, sada zumunci shi ne kyautatawa da jinƙai da bibiyar ’yan uwa (ma’abuta zumunci), ta hanyar sadar da dukan alheri gare su, da kawar da dukan sharri daga gare su gwargwadon iko. Ziyartarsu da amsa kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu’ar alheri, duk ɓangare ne na sada zumunci.
Har ila yau, ma’anar zumunci na game yin sallama ga ɗan uwa yayin haɗuwa da gaishe shi da ce masa Yarhamukallahu idan ya yi atishawa ya ce alhamdulillahi.
Sannan zuwa duba dan uwa yayin da yake rashin lafiya da jajanta masa kan wata asara da ya yi da taya shi farin cikin samun wani alheri da rufa masa asiri da riqe amanarsa da kare mutunci da martabarsa a kan idonsa ko a bayansa a ɓoye ko a bayyane da yi masa nasiha da shawara ta alheri duk sada zumunci ne.
Hukuncin sada zumunci:
Wajibi ne Musulmi su sada zumuncin da ke tsakaninsu, kamar yadda shiryarwar Musuluci ta ginu kan haka, Allah Ta’ala Yana cewa, “ka tuna lokacin da muka riki alkawari daga Banu Isra’ila cewa kada su bauta wa kowa sai Allah, kuma su kyautata ga iyaye da ma’abucin zumunci (’yan uwa) da marayu da miskinai, kuma ku gaya wa mutane kyakkyawan zance, kuma ku tsai da Sallah ku bada Zakka, sai kuka juya baya (ga barin wannan umarni), sai ’yan kaɗan ne daga cikinku, kuna masu bijirewa.”
Kuma a suratul Bakara, aya ta 27 Allah Ya fassara fasiƙai a cikin faɗinsa, “su ne masu warware alƙawarin Ubangiji (kan aiko Annabi SAW), bayan ƙarfafa alqawarin gare su, kuma suke yanke abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi (zumunci), kuma suke ɓarna a bayan ƙasa, waɗannan su ne taɓaɓɓu.”
Ma’abuta zumuci:
Su ne duk makusantan mutum (na jini) na kusa ko na nesa, magadansa ne ko ba magada ba, muharramai ne ko ba muharramai ba, masu dangantaka da shi da suka haɗa da kakanni da iyaye da ’ya’ya da jikoki, ’yan uwa maza ko mata kanne da yayye da ’ya’yansu da ’yan uwan uba da na uwa.
Idan muka faɗaɗa ma’anar zumunci zuwa ga ’yan uwantakar Musulunci da bada haƙƙi ga ma’abutansa, to kai-tsaye, aya ta 36 a Suratun-Nisa’i, za ta yi mana jagoranci ga raba ma’abuta haƙƙin kyautatawa zuwa gida uku, inda Allah Maɗaukaki Yake cewa, “kuma ku bauta wa Allah, kada ku haɗa wani da shi a cikin bauta (shirka), kuma ku kyautata ga iyaye da ma’abucin zumunci da marayu da miskinai da maƙwabci ma’abucin zumunci da makwabci manisanci da aboki a gefe da ɗan tafarki da bayinku. Haƙiƙa Ubangiji ba Ya son wanda ya kasance mai taƙama, mai yawan alfahari.”
Bisa koyarwar wannan aya, za mu iya raba ma’abuta haqqin a kyautata musu zuwa gida uku:
a) Mutum mai haqqi uku: ɗan uwa na jini Musulmi kuma makwabci.
b) Mautum mai haƙƙi biyu: Musulmi kuma makwabci.
c) Mutum mai haƙƙi zaya: makwabci a gida ko a kasuwa ko abokin tafiya da ba Musulmi ba.
Falalar sada zumunci:
Falalar sada zumunci ba za ta kayyaɗu ba, sai dai kawai a faɗi kaɗan daga ciki:
- Tsawaitar rayuwa.
- Wadatar zuciya.
- Bunƙasar dangi.
- Tsallake Siraɗi cikin sauƙi.
- Samun yardar Allah.
- Samun haɗin kai.
- Samun shiga Aljanna da sauransu.
Uƙubar yanke zumunta:
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, shi ne abin da za mu iya cewa, saboda abin da ya samu zumunci na ɓalɓalcewa, babu zumunci, ɗan uwa ya ga ɗan uwansa, kowa ya shige, saboda rashin sani, ko a kan sani. Ba a zumunci, mai kuɗi don girman kai da ganin sai dai shi a zo masa, talaka kuma don tsoron wulaƙanci, talaka da talaka kuma don tsoron kada ya ɗora wa ɗan uwansa nauyi.
Ayoyi da Hadisai da dama, sun ja kunne kan yanke zumunci. Ma’aiki (SAWW) ya ce, “mai yanke zumunci ba zai shiga Aljanna ba.”
Hanyoyin sada zumunci:
Ana sada zumunci ne ta hanyoyi da dama, kamar tattaki zuwa wurin ’yan uwa ko wasiqa ko wayar sadarwa ko saƙon baka (a aika gare) ko shirya tarurrukan taya farin ciki ko jajanta wa wani.
Allah Ya inganta zumuncin da ke tsakanin Musulmi, ya kuma ba mu damar cigaba da sada zumunci da ’yan uwanmu, Ilahee Ameen.
Wassalam, Daga Mustapha Musa Muhammad, Ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.