Editor

9513 Posts
Xi ya yi kira da a inganta mu’amalar al’ummomin Sin da ƙasashen Larabawa mai makoma ta bai-ɗaya

Xi ya yi kira da a inganta mu’amalar al’ummomin Sin da ƙasashen Larabawa mai makoma ta bai-ɗaya

Daga CMG HAUSA Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga kasashen Sin da na Larabawa, da su ci gaba da raya dangantakar abokantakarsu, da inganta mu’amala tsakanin al'ummomin Sin da kasashen Larabawa mai makomar bai daya, yayin da yake jawabi jiya Jumma’a a taron shugabannin kasar Sin da kasashen Larabawa karo na farko. Shugaba Xi ya bayyana cewa, a shirye kasar Sin take ta zurfafa amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare da kasashen Larabawa, da nuna goyon baya ga juna, wajen kiyaye ikon mallaki, da cikakkun yankunan kasa, da kare martabar kasa. Yana mai cewa, ya kamata bangarorin…
Read More
Kimar Fadar White House da majalisar dokokin ƙasar na ci gaba da raguwa

Kimar Fadar White House da majalisar dokokin ƙasar na ci gaba da raguwa

Daga CMG HAUSA Farin jinin fadar White House da majalisar dokokin kasar Amurka, na ci gaba da raguwa, a cewar wani sabon bincike na Gallup. A cewar rahoton, kaso 40 cikin 100 ne mutanen da aka tambaya, sun nuna amincewa da kimar shugaban Amurka Joe Biden, inda kashi 55 cikin 100 suka nuna rashin amincewa da yadda yake tafiyar da aikinsa. Kuri’ar nuna rashin amincewa da Biden, ta ci gaba da karuwa, tun watan Satumban shekarar 2021, bayan ficewar sojojin Amurka daga kasar Afghanistan. A halin da ake ciki, yadda Amurkawa ke nuna rashin amincewa da majalisar dokokin kasar, ba…
Read More
Li Keqiang: Ƙofar Sin a buɗe take tare da maraba da baƙi daga ɓangarori daban-daban

Li Keqiang: Ƙofar Sin a buɗe take tare da maraba da baƙi daga ɓangarori daban-daban

Daga CMG HAUSA A jiya ne, Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da ‘yan jarida tare da shugabannin manyan hukumomin tattalin arzikin duniya dake halartar taro na 7 na rukunin "1+6" a birnin Huangshan na lardin Anhui dake gabashin kasar Sin. Li Keqiang ya bayyana cewa, taron ya yi imani da tabbatar da ra’ayin kasancewar bangarori daban daban, da inganta hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban, da sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Sin ta samu moriya daga manufar bude kofa ga kasashen waje, don haka ta himmatu wajen aiwatar da manufar, kana tana martaba odar…
Read More
Rashin tsoma baki ya sa ƙasar Sin ke samun ƙarin abokai

Rashin tsoma baki ya sa ƙasar Sin ke samun ƙarin abokai

Daga BELLO WANG A kwanakin nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping na ziyara a kasar Saudiyya, inda zai halarci taron koli na Sin da kasashen Larabawa, da taron kolin Sin da kwamitin kasashen dake dab da mashigin tekun Pasha ko (GCC). Yadda shugabannin kasashen Larabawa da dama suka taru a gu daya don tattauna harkokin hadin gwiwa tare da kasar Sin ya shaida matsayi mai muhimmanci na kasar Sin a idon kasashen. Wannan muhimmin matsayi, tushensa shi ne cudanya da cinikin da Sin da kasashen Larabawa suka yi cikin shekaru fiye da 2000 da suka wuce, bi ta hanyar Siliki,…
Read More
Li Keqiang ya halarci taron tattaunawa tare da shugabannin manyan hukumomin tattalin arzkin duniya

Li Keqiang ya halarci taron tattaunawa tare da shugabannin manyan hukumomin tattalin arzkin duniya

Daga CMG HAUSA Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taro na 7 na rukunin "1+6" da suka hada da shugaban bankin duniya David Malpass, da babbar daraktar kungiyar cinikayya ta duniya WTO uwargida Ngozi Okonjo-Iweala, da babbar daraktar asusun ba da lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva, da babban direktan kugiyar kwadago ta duniya Gilbert F. Houngbo, da babban sakataren kungiyar bunkasa ci gaban tattalin arziki da samar da ci gaba ko OECD Mathias Cormann, da kuma shugaban majalisar kula da hada-hadar kudi ta duniya Klaas Knot. An gudanar da taron ne a birnin Huangshan na lardin Anhui dake…
Read More
Gwamna Buni ya bayar da umurnin raba wa tsangayoyi 475 kayan abinci da tufafi a Yobe

Gwamna Buni ya bayar da umurnin raba wa tsangayoyi 475 kayan abinci da tufafi a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu A ƙoƙarin sa na inganta rayuwar al'ummar jihar, Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya bai wa hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, umurnin raba wa makarantun tsangaya 475, wanda ake sa ran alarammomi da almajiransu 8,000 za su ci gajiyar tallafin kayan abinci da na masarufi haɗi da dilolin tufafin sakawa, barguna, tabarmin leda, bokitan ruwa da sauran su a faɗin jihar Yobe. Da take ƙaddamar da rabon tallafin a Tsangayar Slaramma Goni Yahaya dake unguwar Gwange a Damaturu, Sakataren Hukumar SEMA, Dr. Muhammad Goje, wanda Daraktan hukumar, Alhaji Hassan Bomai ya…
Read More
‘Yan Nijeriya miliyan 25 za su shiga matsalar ƙarancin abinci a 2023 – FAO

‘Yan Nijeriya miliyan 25 za su shiga matsalar ƙarancin abinci a 2023 – FAO

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), ta bayyana cewa aƙalla mutum miliyan 25.3 za su fuskanci mummunan matsalar ƙarancin abinci a tsakanin watannin Yuni da Agustan 2023. A cikin sanarwar da FAO ɗin ta fitar, ta ce idan tun da wuri ba a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki ba, to mutum miliyan 4.4 a Barno, Adamawa da Yobe za su rasa cin yau da na gobe. Cikin rahoton da hukumar ta fitar na watan Oktoba 2022, FAO ta ce a yanzu haka mutum miliyan 17 na rayuwar cin abincin da kwata-kwata ba mai…
Read More
Babu laifin mu a wahalar man fetur da a ke yi a Nijeriya – IPMAN

Babu laifin mu a wahalar man fetur da a ke yi a Nijeriya – IPMAN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Dillalan Man fetur ta Ƙasa, IPMAN, ta fitar ce ba laifinta ba ne a ƙarancin man fetur da ake fama da shi a ƙasar. Ƙungiyar ta kuma ce mambobinta ba su da hannu a ƙarancin da ake fama da shi a halin yanzu. Femi Adelaja, Shugaban IPMAN ta defot ɗin Mosinmi a Jihar Ogun, a wata sanarwa da ya fitar a ƙarshen mako, ya ce babu man fetur a cikin gidajen man fetur na ƙasa (NNPC) a faɗin Nijeriya. Ya ce a yanzu haka farashin man fetur daga defot ya kai Naira 220…
Read More
Na’urorin BVAS da sauran muhimman kayan zaɓe na nan lafiya ƙalau — INEC

Na’urorin BVAS da sauran muhimman kayan zaɓe na nan lafiya ƙalau — INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa, ba a ajiye na’urorin tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS) a wuraren da 'yan bangar siyasa su ka kai hari tare da ƙona su kwanan nan ba. INEC ta kuma ce wasu muhimman kayyakin da za a yi amfani da su wajen gudanar da zaɓukan 2023 su na nan lafiya ƙalau cikin tsaro. Kwamishinan INEC na Ƙasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, Mista Festus Okoye ne ya sanar da hakan a wani…
Read More
Al-Mustapha ya zargi ƙasashen Yamma da tsawaita ta’addancin Boko Haram

Al-Mustapha ya zargi ƙasashen Yamma da tsawaita ta’addancin Boko Haram

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Ɗan takarar Shugaban Nijeriya a Jam'iyyar ‘Action Alliance’ kuma tsohon jami’in tsaron tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji Marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi zargin cewar, akwai wata maƙarƙashiya da ƙasashen Yamma suke yi na tsawaita ta’addancin Boko Haram a ƙasar nan. Al-Mustapha ya yi wannan tsokaci ne a wata tattaunawa kan zaɓen shekara ta 2023 da aka gudanar a makon da ya gabata a birnin Abuja. Ya ce duk da cewar, an ƙyanƙyashe ta’addancin Boko Haram ne a ranar 1 ga watan Nuwamba na shekarar 1999, amma an ƙudura aniyyar sa…
Read More