Li Keqiang ya halarci taron tattaunawa tare da shugabannin manyan hukumomin tattalin arzkin duniya

Daga CMG HAUSA

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taro na 7 na rukunin “1+6” da suka hada da shugaban bankin duniya David Malpass, da babbar daraktar kungiyar cinikayya ta duniya WTO uwargida Ngozi Okonjo-Iweala, da babbar daraktar asusun ba da lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva, da babban direktan kugiyar kwadago ta duniya Gilbert F. Houngbo, da babban sakataren kungiyar bunkasa ci gaban tattalin arziki da samar da ci gaba ko OECD Mathias Cormann, da kuma shugaban majalisar kula da hada-hadar kudi ta duniya Klaas Knot. An gudanar da taron ne a birnin Huangshan na lardin Anhui dake gabashin kasar Sin.

A yayin taron, Li Keqiang ya bayyana cewa, yanzu yanayin tattalin arzikin duniya yana fuskantar sarkakkiya, don haka ya kamata bangarorin su kara yin hadin gwiwa kan manyan manufofi, da daidaita matsalar hauhawar farashin kaya, kana su tabbatar da ra’ayin musayar bangarori daban daban, da nuna goyon baya ga yin ciniki cikin ‘yanci da adalci, da tabbatar da samar da kayayyaki yadda ya kamata a duniya.

Li Keqiang ya kara da cewa, a bana, Sin ta cimma burin tabbatar da samar da aikin yi da kiyaye farashin kaya, da bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata, wannan ba abu ne mai sauki ba a yayin da ake tinkarar cutar COVID-19.

Shugabannin manyan hukumomin tattalin arzikin duniya sun bayyana cewa, za su hada kai wajen tinkarar kalubalen duniya, sun kuma nuna yabo ga kasar Sin kan matakan da ta dauka na tabbatar da samar da aikin yi da kiyaye farashin kaya, da yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje.

Mai fassara: Zainab

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *